A+ R A-
29 February 2020

Jagora: Babbar Manufar Masu Adawa Da Iran Ita Ce Hana Ta Samun Karfi Na Ilimi Da Fasaha

A safiyar yau Laraba (09-10-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullahi Sayyid Ali Khamenei ya gana na sa’oi biyu da wasu matasa daliban jami’oi sama da dubu da suna nuna bajinta a bangarori daban inda suka gabatar da mahangarsu kan batutuwa daban-daban da kuma matsalolin da suke fuskanta kana daga baya kuma Jagoran ya gabatar da nasa jawabin.

A jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: kwararrun matasan Iran, su ne masu tsara ci gaban makomar kasar nan.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar siyasar ci gaban ilimi da Iran ta dauka, wata siyasa ce da ta samo asali daga koyarwar Musulunci, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: masana da kwararrun kasar Iran dai sun cimma matsayar cewar daya daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen tsallake matsaloli da barazanar da ake fuskanta, ko shakka babu samun ci gaban ilimi yana daga cikin wadannan abubuwan.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara kan irin kwarewa da kuma karfin da Iran take da shi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: ko shakka babu kwararru da masana matasa na Iran suna da karfin ciyar da Iran da al’ummar kasar gaba a dukkanin bangarori.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: irin shiri da kuma kwarewar da masanan Iran suke da ita ta kai wani matsayin da za a iya cimma duk wata manufa ta ilimi da fasaha da kasar nan take bukata.

Jagoran ya ce: Babban dalilin da ya sanya aka mayar da batun ci gaban ilimi ya zamanto wata manufa da aka sa gaba a Iran, shi ne cewa babu yadda za a iya samun ci gaba na hakika ba tare da ci gaba na ilimi da fasaha ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: wajibi ne wannan ci gaban na ilimi ya zamanto ya dogara ne da irin kwarewar da ake da ita a cikin gida, don kuwa ci gaba na ilimi da ya samo asali daga cikin gida ya kan share fagen tabbatar da daukaka da kuma mutumcin kasa da kuma al’ummarta.

Har ila yau kuma yayin da yake karin haske dangane da irin muhimmancin da ilimi yake da shi wajen tabbatar da tsaro da mutumcin kasar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Kwararrun matasa, dukkanin jami’ai da kuma al’ummar Iran su san cewa babbar manufar masu adawa da tsarin Musulunci na Iran, ita ce hana Iran samun karfi na ilimi da fasaha.

Jagoran ya ci gaba da cewa: wajibi ne a dukkanin sharhi da dubin da za a yi wa lamurran da suka shafi siyasa, tattalin arziki da sauran lamurra na yankin nan da kuma na kasa da kasa, su zamanto ta yadda za a san cewa akwai wasu masu takama da karfi a duniyar nan da ba sa fatan ganin kasar Musulunci ta Iran da al’ummarta sun zamanto masu karfi da ci gaba a fagage daban-daban musamman a fagen ilimi da fasaha.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da maganganun da wasu masana da kwararrun Amurka da kasashen yammaci suke yi kan Iran a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: A cikin wadannan maganganu da kasidu, sun ja kunnen ‘yan siyasar kasashen yammacin da cewa nasarar juyin juya halin Musulunci ba  wai kawai sauya wani tsari ko  gwamnati ba ce, face nasarar juyin juya halin Musuluncin yana nufin bayyanar wani sabon karfi ne a yankin yammacin Asiya wanda mai yiyuwa ne kasashen yammaci su rasa irin ikon da suke da shi a wannan yankin mai tsananin muhimmanci wanda hakan zai zamanto babban kalubale ga kasashen yammacin.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Bayan gushewar sama da shekaru talatin, a halin yanzu wannan damuwa da kasashen yammaci da Amurkawan suke da ita, ta tabbata, sannan kuma an tabbatar da wata kasa mai karfi a yankin nan wacce dukkanin matsin lamba na siyasa, tattalin arziki, tsaro da farfaganda sun gagara dunkufar da ita. Kai wannan kasar ma ta zamanto mai tasiri cikin al’ummomin yankin nan da kuma karfafawa al’ummar musulmi gwiwa.

Yayin da ya ke magana kan lamurran da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya da kuma arewacin nahiyar Afirka cikin shekaru biyun da suka gabata kuwa da kuma matakan da Amurka da kasashen yammaci suka dauka kan hakan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Farkawar da al’ummomi suka yi da kuma tsayin dakan da suka yi hannu rabbana wajen tinkarar wulakancin da kasashen yammaci da Amurka suke yi musu, lalle hakan wani lamari ne mai girma, wanda kuma sabanin fatan da kasashen yammacin suke da shi, har ya zuwa yanzu bai kawo karshe ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wannan lamari wani juyi ne na tarihi wanda har ya zuwa yanzu yankin nan yana cikinsa, wanda hakan ne ya ke ci gaba da damun kasashen yammacin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: wannan gagarumin lamari kuwa ya samo asali ne albarkacin juyin juya halin Musulunci wanda tun farko-farkonsa ya yi bisharar bayyanar wani karfi na al’umma da kuma muminai.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami’an gwamnati da kuma sauran jami’an da lamari ya shafa da su ba da himma wajen karfafa duk wata hanyar da za ta samar da ci gaban ilimi da fasaha a kasar Iran wanda hakan zai share fagen tabbatar da kasar Iran ma’abociyar ci gaba da kuma daukaka.

Tun da fari dai sai da wasu daga cikin mahalarta taron suka gabatar da jawabansu da kuma mahangarsu kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar Iran da kuma duniya musamman a fagen ilimi da kuma abubuwan da ke gudana, bugu da kari kan matsalolin da ake fuskanta da kuma hanyoyin da suke ganin za a iya magance su.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook