A+ R A-
13 July 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 1241 Saboda Zagayowar Babbar Salla Da Idin Ghadir

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi afuwa fursunoni dubu daya da dari biyu da arba’in da daya (1,241) da kotuna daban-daban na Iran suka yanke musu hukumci don tunawa da zagayowar idin babbar salla da kuma Idin Ghadir, ranar da Manzon Allah (s) ya nada Imam Ali (a.s) a matsayin halifa a bayansa.

Shafin watsa labarai da ayyukan Jagoran ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya watsa inda ya bayyana cewar Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi wannan afuwar ce bisa bukatar hakan da alkalin alkalai kuma shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Ayatullah Sadiq Amoli Larijani ya gabatar masa don tunawa da wadannan ranaku masu girma da muhimmanci a tsakanin al’ummar musulmi.

Fursunonin da aka yi musu afuwa ko kuma rage musu wa’adin zaman gidan yarin na su don tunawa da ranakun idin babbar salla da kuma idin Ghadir din sun hada ne da fursunonin da kotunan fararen hula, na juyin juya hali da kuma na dakarun soji suka yanke musu hukumci saboda laifuffukan da suka aikata.

A kowace shekara dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kan yi irin wannan afuwar ga fursunonin da suka nuna da’a da sauran halaye na kwarai da kuma wadanda suke da matsaloli na musamman da dai sauransu don girmama wadannan ranaku na idi na al’ummar musulmi.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook