A+ R A-
26 May 2020

Jagora Imam Khamenei: Amurka Ce Babbar Alamar Girman Kan Duniya

A safiyar yau Lahadi (3-11-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban daliban makarantu da jami’oin Jamhuriyar Musulunci ta Iran don tunawa da ranar kasa ta fada da girman kan duniya.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi karin bayani dangane da dalilan da ya sanya ma’abota girman kan duniya suke adawa da al’ummar Iran, kamar yadda kuma ya yi karin haske kan batun shirin tattaunawa da Amurka da gwamnatin Iran take yi kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar inda ya ce: tarihin Amurka da kuma halayenta sun tabbatar da cewa batun nukiliya wani lamari ne kawai da take fakewa da shi wajen ci gaba da adawar da take yi da Iran. A saboda haka bai kamata wani ya yaudaru da sakin fuska ta yaudara da makiya suke yi ba. Idan har (tattaunawar da ake yi din) ta haifar da da mai ido, to me ya fi hakan, idan kuwa ba haka ba, to hakan yana tabbatar da maganganun da muka sha yi ne na cewa za a iya magance matsalolin da ake da su ne kawai ta hanyar dogaro da kai.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da abubuwa guda uku da suka faru a wannan rana ta 13 ga watan Aban (ranar fada da girman kan duniyan), Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: tura Imam zuwa gudun a shekarar 1343 saboda jawabin da ya yi na adawa da dokar kariya da gwamnatin Shah (ta wancan lokacin) ta ba wa sojoji da ma’aikata Amurkawa da suke Iran, kisan gillan rashin imani da jami’an tsaron gwamnatin kama karya ta (Shah) da take samun goyon bayan Amurka suka yi wa daliban makarantu a Tehran a shekara ta 1357 da kuma yunkuri na jaruntaka da daliban jami’a suka yi na kame ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1358, kowane guda daga cikin wadannan abubuwa ukun, ta wani bangaren suna da alaka da Amurka. A saboda haka ne ake kiran ranar 13 ga watan Aban a matsayin rana ta kasa ta fada da girman kai.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske dangane da wannan kalma ta (ma’abota) girman kai da ta zo cikin Alkur’ani inda ya kara tunatar da al’umma da cewa: Matasa muminai daliban jami’a wadanda a shekarar 1358 suka kame ofishin jakadancin Amurkan, sun gano hakikanin wannan ofishin jakadancin ne wanda a hakikanin gaskiya wata sheka ce ta leken asiri, sannan kuma suka nuna wa duniya hakan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: a wancan ranar, matasanmu sun sanya wa ofishin jakadancin Amurkan sunan shekar leken asiri. A yau bayan gushewar sama da shekaru talatin, sai ga shi ana kiran ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Turai, wadanda abokan Amurkan ne ma, da sunan shekar leken asiri. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa matasanmu suna gaba da duniya da shekaru talatin da wani abu wajen fahimtar wannan lamarin.

Bayan wannan bayanin ne sai Jagoran ya koma ga batun ma’anar girman kan inda ya ce: Ana amfani da wannan kalma ta girman kai ne ga mutane da kuma gwamnatocin da suke ganin tsoma baki cikin lamurran al’ummomin duniya da tilasta musu abin da suke so a matsayin wani hakki da suke da shi, sannan kuma babu wani da ya isa ya ce musu uffan.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kishiyar girman kan kuwa ita ce a samu al’ummomi da mutanen da ba su yarda su mika wuya ga wannan tsoma baki na ma’abota girman kai din sannan kuma suna fada da haka, wanda al’ummar Iran tana daga cikin irin wadannan al’ummomi.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa gwamnatin Amurka gwamnatin girman kai ce wacce take ganin kanta a matsayin wacce take da hakkin tsoma baki cikin lamurran cikin gidan wasu kasashe, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A hakikanin gaskiya al’ummar Iran sakamakon wannan juyin juya hali na su sun tabbatar da tsayin dakan su wajen rashin yarda da wannan girman kai na Amurka, sannan kuma bayan nasarar juyin juya halin Musuluncin sun gutsure tushen wannan girman kan a cikin gidansu, sannan kuma sabanin wasu kasashen, ba su bar gyauron wannan tushen ba, ballantana daga baya ya cutar da su ba.

Har ila yau kuma yayin da ishara da cewa babu wani amfani da kasashe da al’ummomin duniya za su samu sakamakon mika kansu ga ma’abota girman kan, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Irin mu’amala da girman kan Amurka ne ya sanya al’ummomin duiya kyama da kuma rashin yarda da ita, baya ga cewa tarihi ya tabbatar da cewa duk wata al’umma ko wata gwamnatin data dogara da Amurka, to kuwa ta sha kashi koda kuwa tana daga cikin kawayen Amurkan ne.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kawo wasu misalai don tabbatar da wannan magana da ya fadi ciki kuwa har da yarda da Amurkan da Dakta Mosaddiq (tsohon firayi ministan Iran) ya yi da Amurka inda daga baya suka yi masa juyin mulki a ranar 28 ga watan Mordad da kuma rashin cika alkawarin da Amurkawan suka yi wa Muhammad Ridha Pahlawi (Sarki Shah) bayan ya gudu daga Iran inda ya ce: A halin yanzu a tsakanin al’ummomi, gwamnatin da al’umma suka fi kyama a duniya, ita ce gwamnatin Amurka.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yau idan har da za a gudanar da ingantacciyar kuri’ar jin ra’ayin al’umma ingantacciya sannan kuma cikin adalci, to kuwa da an ga cewa babu wata gwamnatin da al’ummomin duniya suka fi kyama kamar gwamnatin Amurka.

A karshen wannan bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: A saboda haka batun nuna kiyayya ga girman kai da kuma ranar kasa ta fada da girman kan duniya, wani lamari ne mai muhimmancin gaske wanda kuma ya samo asali daga ingantacciyar fahimta.

Daga nan Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kirayi dukkanin matasa zuwa ga sanya ido da kuma kyakkyawar fahimta ga lamarin fada da girman kan duniya inda ya ce: Matasan farko na juyin juya halin Musulunci ba sa bukatar wani sharhi dangane da fada da Amurka, don kuwa da idanuwansu sun ga iriin zaluncin da Amurka take yi da kuma irin goyon bayan da take ba wa gwamnatin dagutu ta wancan lokaci. Amma matasanmu na yau wajibi ne su gudanar da bincike da kuma yin kyakkyawar fahimtar dalilan da suka sanya al’ummar Iran adawa da girman kai da halayen Amurka. Wato mene ne dalilin da ya sanya al’ummar Iran kyamar Amurka?

Daga nan kuma sai Jagoran ya koma ga batun tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da ake shirin yi inda ya yi karin haske kan wasu lamurra masu muhimmanci.

Yayin da yake bayyanar da goyon bayansa ga tawagar jami’an Iran da suke tattaunawa da manyan kasashen duniya ciki kuwa har da Amurka kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran, Jagoran cewa ya yi: Wadannan mutane dai ‘ya’yan wannan juyin ne sannan kuma wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne wadanda suke gudanar da wannan aiki mai wahalar gaske,  don haka bai kamata wani ya raunana su ba ko cin mutumcinsu ko kuma daukansu a matsayin masu sassauci da mika kai ba.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa tattaunawar da Iran take yi da wadannan kasashe shida ciki kuwa har da Amurkan, tattaunawa ce kawai kan batun nukiliya ban da wani abu na daban, don haka sai ya ce: Cikin yardar Allah ba za mu cutu cikin wannan tattaunawar ba, don kuwa hakan zai zamanto tamkar wata kwarewa ce ga al’ummar Iran, tamkar kwarewar da aka samu yayin dakatar da tace sinadarin uranium a shekarun 1382-83, wanda hakan ya kara irin yadda al’ummarmu suke tunani da kuma sharhi kan lamurra.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Shekaru goma da suka gabata, a lokacin da muke tattaunawa da Turawa, mun amince da abin da suka dora masa da kuma ja da baya, to amma bayan shekaru biyu na dakatar da tace sinadarin uranium din da kuma dakatar da abubuwa da yawa, daga nan kowa ya fahimci cewa babu wani abin da za a iya samu daga wajen kasashen yammaci ko da kuwa an mika musu kai din ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan da a ce ba mu hakan ba, da mai yiyuwa ne wasu su yi ikirarin cewa idan da a ce kun dan ja da baya da mika kai, to da kuwa an magance matsalolin da kuma kawo karshen wannan matsala ta nukiliya. Amma sakamakon wannan dakatarwar ta dan lokaci da aka yi, kowa ya fahimci cewa masu adawa da mu din wani abu na daban suke son cimmawa. A saboda haka ne aka sake komawa bakin aiki sannan kuma aka sami ci gaba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana bambancin da ke cikin shirin nukiliyan Iran a yau da kuma shekaru goman da suka gabata da cewa wani bambanci ne tamkar sama da kasa, daga nan sai ya sanar da goyon bayansa ga jami’an kasar Iran da suke tattaunawa da Amurka inda ya ce: Ni dai ba ni da wani kyakkyawan fata ga tattaunawar da ake yi da Amurka, don kuwa babu wani tabbas na cewa za a kai ga sakamakon da al’ummar Iran suke fatan gani. To amma duk da haka na yi amanna da cewa babu laifi a samu irin wannan kwarewar, amma da sharadin cewa al’ummarmu za su kasance a farke sannan kuma su san me ke gudana.

Haka nan kuma yayin da yake kakkausar suka ga wasu mutane da suke ta maganganu ko dai da wata manufa ko kuma saboda karamar kwakwalwa da suke da ita, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Akwai wasu mutane wadanda ta hanyar dogaro da kafafen watsa labaran ‘yan kasashen waje suke ta kokar wajen batar da mutane suna masu cewa idan da a ce mun sassauto da mika kai cikin wannan batu na nukiliya, to kuwa da an magance dukkanin matsaloli na tattalin arziki da sauransu da ake fuskanta.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai ya kawo wasu misalai da suke tabbatar da rashin ingancin maganganun wadannan mutanen da suka hada da makirce-makircen Amurka da kiyayyar da take nuna wa al’ummar Iran tun ma kafin a fara maganar nukiliya a Iran, don haka sai ya kirayi dukkanin matasan Iran da su yi taka tsantsan kan irin wadannan farfagandar.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Shin a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci lokacin da Amurka ta kakabawa Iran takunkumi sannan kuma ta ci gaba da hakan, shin akwai wani batun nukiliya ne a lokacin? Shin a lokacin da suka kai hari kan jirgin fasinjan Iran da kashe mutane 290 a cikin jirgin, shin akwai wata magana ta nukiliya ne? Shin a farko-farkon juyin juya halin Musulunci a lokacin da Amurka ta tsara juyin mulkin barikin soji na Shahid Nuje, shin a lokacin akwai maganar nukiliya ne? Shin irin goyon baya na siyasa da makamai da Amurka take ba wa kungiyoyi masu adawa da juyin juya halin Musulunci na Iran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, shin suna yin hakan ne saboda batun nukiliya?

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A saboda haka, batun nukiliya wani lamari ne kawai da suke fakewa da shi. Idan ma har abin a wani lokaci a ja da baya ne, to kuwa za su sake kawo wasu abubuwan don ci gaba da wannan kiyayyar da suke yi da Iran, ciki kuwa har da irin ci gaban da Iran ta samu a fagen makamai masu linzami, adawar da al’ummar Iran suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take ba wa kungiyoyin gwagwarmaya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Adawar da Amurka take yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya samo asali ne sakamakon kin amincewa da manufofinsu, sannan kuma sun yi amanna da cewa babu wani abin da Amurka za ta iya yi wa al’ummar Iran.

Jagoran ya ce: Amurka tana adawa da kasantuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma irin tasiri da karfin da wannan tsari da al’umma suka zaba yake da shi ne. kamar yadda cikin ‘yan kwanakin nan daya daga cikin ‘yan siyasan Amurka a fili ya fadi cewa Iran dai ko tana da makaman nukiliya ko ba ta da su, hatsari ce. Don kuwa tana da karfi da kuma tasiri a wannan yanki.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A saboda haka batun nukiliya wani abin da suke fakewa da shi ne kawai, sannan kuma Amurka za ta bar wannan adawar da take yi da al’ummar Iran ne kawai a lokacin da ta ga cewa al’ummar Iran sun zamanto saniyar ware marasa wani tsiri da kuma mutumci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Matukar dai wata al’umma ta dogara da irin karfin da take da shi, to kuwa ba za ta cutu daga fushi ko kuma takunkumin makiya ba. Wajibi ne mu yi dukkanin abin da za mu iya wajen tabbatar da wannan manufar.

Jagoran ya kara da cewa tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yanzu babu wani lokaci da al’umma da kuma jami’an kasar Iran suka yi sassauci ko gajiya da fada da makiya, kuma a nan gaba ma ba za su yi hakan ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, al’ummar Iran ba ta da wani abin azo a gani na abin duniya da suka hada da kudi, makamai, kwarewa ta soji da sauransu, alhali kuwa makiyan al’ummar Iran na lokacin wato gwamnatin Saddam tana samun dukkanin goyon baya daga wajen ma’abota girman kan duniya, to amma duk da hakan al’ummar Iran ta sami nasarar dunkufar da shi a kan gwiwansa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A halin yanzu yanayin Iran ya sauya da yanayin wancan lokaci, don kuwa a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci tana da kwarewa ta ilimi da fasaha, ga makamai na zamani ga kuma kwarewa, alhali su kuwa masu adawa da Iran wato Amurkawa da kawayensu suna fuskantar matsaloli daban-daban na siyasa da tattalin arziki da kyawawan halaye.

Daga karshe dai ya kirayi jami’an diplomasiyya na kasar da su yi taka tsantsan wajen tattaunawa da Amurka inda ya ce: Kiran da nake yi wa jami’an diplomasiyya da kuma tattaunawa da Amurka shi ne su yi taka tsantsan, kada sakin fuska na yaudara na Amurka ya yaudare ku.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami’ai su sanya ido sosai dangane da dabi’un wadanda suke tattaunawa da su din. Don kuwa suna iya sake fuska da kuma nuna cewa suna son a tattaunawa, to amma a bangare guda kuma suna fadin cewa dukkanin matakan da za su iya dauka suna nan daram. Ko mai suke son yi oho.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da maganar daya daga cikin ‘yan siyasan Amurka wanda ya bukaci a kawo wa Iran hari da makaman nukiliya inda ya ce: Idan har Amurkawa da gaske suke yi na cewa lalle suna son tattaunawar, wajibi ne su bugi bakin mutumin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mu dai tun a ranar farko mun fadi, sannan kuma a halin yanzu ma muna sake fadi a nan gaba ma za mu fadi cewa mu dai muna ganin haramtacciyar kasar Isra’ila ne a matsayin wata haramtacciyar kasa maras halalci.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook