A+ R A-
29 February 2020

Jagora Imam Khamenei Yayin Ganawa Da Jami’an Aikin Hajji: Wajibi Ne Musulmi Su Yi Amfani Da Aikin Hajji Wajen Karfafa Hadin Kansu

A safiyar yau Litinin (11-11-2013) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami’an aikin hajjin bana na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya bayyana aikin hajji a matsayin wata kyauta ta Ubangiji sannan kuma wata dama wacce ba ta karewa wajen samar da fahimtar juna da kuma gano abubuwan da al’ummar musulmi na duniya suke bukatarsu, daga nan kuma sai ya ce: Daya daga cikin manyan matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a wannan lokacin, ita ce matsalar kokarin ruruta wutar fitina da sabani na mazhaba da bangaranci da ake yi a tsakanin al’ummar musulmi.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada wajibcin lura da kuma fahimtar irin yanayin da duniya take ciki da kuma abubuwan da ake bukata don samun damar amfanuwa da gagarumar damar da take cikin aikin hajji, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: ma’abota girman kan duniya da ‘yan mulkin mallaka suna da gagarumar kwarewa wajen kunna wutar sabani na mazhaba (tsakanin musulmi). A saboda haka a irin wannan yanayin ya zama wajibi a yi amfani da damar aikin hajji wajen fada da wannan makircin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Rikicin bangaranci da mazhaba ba zai takaita kawai ga Sunna da Shi’a ba. Matukar makiya Musulunci suka sami damar haifar da wannan rikicin, to kuwa babban abin da za su sa a gaba shi ne haifar da fitina na kabilanci cikin ‘yan Sunna da kuma cikin ‘yan Shi’a.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samar da yanayi na fahimta juna da kuma irin abubuwan da aka yi tarayya kansu a duniyar musulmi a matsayin daya daga cikin dama maras tamka da ake samu a lokacin aikin hajji daga nan sai ya ce: har ya zuwa yanzu ba a gano da dama daga cikin damar da ake da su a cikin aikin hajji ba. A saboda haka wajibi ne a yi amfani da kwararru wajen gano irin wadannan damar da ake da su don amfanuwa da su.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gode wa jami’an aikin hajjin na bana na Iran saboda irin namijin kokarin da suka yi wajen yin hidima ga maniyyatan na bana kamar yadda kuma yayi fatan al’ummar musulmi za su amfana da irin wannan gagarumar ni’ima ta aikin hajji da suka samu.

Tun da fari dai, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Qadhi Askari, wakilin Jagoran sannan amirul hajji na Iran, ya gabatar da rahoto kan irin ayyukan da suka gudanar a yayin aikin hajjin na bana.

Shi ma a nasa bangaren, Malam Awhadi, shugaban hukumar alhazai ta Iran ya gabatar da rahoto kan irin tsare-tsare da kuma hidimomin da hukumar tasa ta gudanar don jin dadin alhazan.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook