A+ R A-
26 May 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Halarci Taron Juyayin Daren Tasu’a A Husainiyar Imam Khumaini (r.a)

A daren yau Talata (12-11-2013) wanda ya yi daidai da daren ranar Tasu’a (tara ga watan Muharram) ne aka gudanar da taron zaman makokin shahadar Imam Husaini (a.s) tare da mabiyansa su 72 a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A yayin wannan taron dai, wanda ya sami halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci da manyan jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran bugu da kari kan dubun dubatan al’ummar kasar, Hujjatul Islam Sayyid Ahmad Khatami ne ya gabatar da jawabi inda ya tabo bangarori daban-daban na abin da ya faru a Karbala da kuma wannan yunkuri na Imam Husain (a.s).

Har ila yau a wajen taron, mawakan Ahlulbaiti (a.s) Hajj Nura’iy da Hajj Mahmud Karimi sun gabatar da wakokin juyayi da bayanin abubuwan da ya sami Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Karbala.

Za’a ci gaba da gudanar da wadannan tarurruka na juyayin Ashura a Husainiyar ta Imam Khumaini (r.a) har zuwa ranar Juma’a mai zuwa, wacce ta yi daidai ga 11 ga watan Muharram.

Ana Iya Ganin Hotunan Taron Ta Nan

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook