A+ R A-
07 August 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Halarci Taron Juyayin Daren Ashura A Husainiyar Imam Khumaini (r.a)

A daren yau Laraba (13-11-2013) wanda ya yi daidai da daren ranar Ashura (goma ga watan Muharram) ne aka gudanar da taron zaman makokin shahadar Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A yayin wannan taron, wanda ya sami halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da wasu manyan jami’an gwamnati da na soji bugu da kari kan dubban al’ummomi daban-daban na kasar Iran, Hujjatul Islam wal muslimin Sheik Ali Ridha Panahiyan ne ya gabatar da jawabi inda ya tabo bangarori daban-daban na wannan yunkuri na Aba Abdillah al-Husain (a.s).

Har ila yau a wajen taron, mawakan Ahlulbaiti (a.s), Malam Behtash da Sa’id Haddadiyan ne suka gabatar da wakokin juyayi da bayanin abubuwan da ya sami Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Karbala.

Za'a ci gaba da gudanar da wadannan tarurruka na juyayin Ashura a Husainiyar ta Imam Khumaini (r.a) har zuwa ranar Juma'a mai zuwa, wacce ta yi daidai ga 11 ga watan Muharram.

Ana Iya Ganin Hotunan Taron Ta Nan

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook