A+ R A-
26 May 2020

Imam Khamenei Wajen Taron Basij: Amurka Ita Ce Jagorar Ma'abota Girman Kai

A safiyar yau Laraba (20-11-2013) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandoji dubu hamsin na dakarun sa kai na Iran (Basij) don tunawa da makon dakarun sa kan inda yayi karin haske kan matsayin dakarun na Basij da kuma siffofi da hanyoyin da ma’abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suke bi wajen yaudarar mutane.

A jawabin da ya gabatar a wajen wannan gagarumin taron, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana dakarun Basij a matsayin wata alama ta girma da daukakar al’ummar Iran sannan kuma wani karfi na cikin gida na kasar Iran inda ya ce: Dakarun Basij masu faranta rai da sanya fata cikin zukata masoya wannan tsari (na Musulunci), juyin juya hali da kuma kasar Iran, sannan kuma masu sanya yanke kauna da tsoro cikin zukatan makiya da masu fatan sharri ga wannan tsari na Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da yadda makon Basij din ya yi daidai da lokacin gagarumin yunkuri Sayyida Zainab (amincin Allah ya tabbata a gare ta), Jagoran cewa ya yi: Yunkurin Zainab cikamaki ne na yunkurin Ashura, wato a wata ma’anar yunkurin Sayyida Zainab yunkuri ne na raya yunkurin Ashura da kuma kiyaye shi.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wannan madaukakiyar mace ta kasance koli na daukaka da tsayin daka wajen tinkarar dukkanin musiba da abubuwa masu sosa rai da suka faru sannan kuma ta zamanto abin koyi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin da Sayyida Zainab (a.s) ta yi a gaban mutanen garin Kufa da kuma wanda ta yi a fadar Ibn Ziyad da kuma na Yazid, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Ko shakka babu wannan madaukakiyar mace ta kasance babbar alama ta daukaka, kamar yadda Imam Husaini (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya kasance a ranar Ashura.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce sakamakon wannan yunkuri da tsayin daka na Sayyida Zainab shi ne samar da tafarki da kuma dawwamammen yunkuri na tsayin daka a bisa tafarkin gaskiya ba tare da tsoro ba. Don haka sai ya ce: wajibi ne tafarkin Zainab ya zamanto abin koyinmu, sannan kuma manufarmu ta zamanto Musulunci da kuma daukaka irin ta dan’adam.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa babban dalilin bayyanar irin wannan karfin hali da Sayyida Zainab (a.s) da sauran Annabawa da Waliyai da muminai suka nuna shi ne riko da gaskiya da kuma alkawarin da suka yi wa Ubangiji, daga nan sai ya ce: Alkur’ani mai girma ya bayyana wannan gaskiyar a matsayin abin da manyan Annabawa da Waliyai da muminai da sauran mutane suke bukatuwa da ita. A saboda haka wajibi ne dukkaninmu mu yi kokarin cika wannan alkawari da muka yi wa Ubangiji.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A bisa nassi na Alkur’ani, wannan alkawarin shi ne tsayin daka wajen tinkarar makiya a fagen daga ne ko kuma a fagen siyasa da tattalin arziki da kuma rashin juya baya ga makiya.

Jagoran ya ce: A bisa wannan alkawarin, wajibi ne a tsaya kyam a gaban makiya a duk wani fage na fito na fito, sannan kuma wajibi ne azama da iradar muminai ta yi galaba a kan iradar makiya.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya yi karin haske dangane da batun sauyi cikin diplomasiyya da yayi magana kansa a kwanakin baya inda ya ce: wasu sun bayyana wannan magana da cewa ja da baya ne daga koyarwar tsarin Musulunci, sannan wasu makiya ma sun yi da’awar cewa an yi watsi da koyarwa da manufofin wannan tsarin, alhali kuwa babu gaskiya cikin hakan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: sauyi cikin diplomasiyya yana nufin yunkuri cikin kwarewa da amfani da hanyoyi daban-daban wajen cimma manufofi daban-daban na wannan tsari na Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya ce: wadannan manufofi, dai wasu manufofi ne masu mataki-mataki wadanda jami’an gwamnati suke bin wadannan matakai wajen isa gare su.

Daga nan kuma sai Jagoran ya gabatar da wasu tambayoyi da cewa: Shin dagewar da tsarin Musulunci na Iran ya yi wajen samun ci gaba, shin hakan yana nufin neman tsoka da yaki ne? Shin gwamnatin Musulunci ta Iran tana son fada da dukkanin al’ummomi da gwamnatocin duniya ne? kamar yadda a wasu lokuta wasu makiyan al’ummar Iran, ciki kuwa har da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa, suke fadi.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: wannan da’awar ta makiya, ta yi hannun riga da mahanga da kuma tafarkin Musulunci. Don kuwa manufar tsarin Musulunci na Iran wadda aka samo ta daga koyarwar Musulunci da Alkur’ani da Manzon Allah da tsarkakan Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su), ita ce tabbatar da adalci da kyautatawa da taimako ga dukkanin al’ummomi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Babbar barazanar ga duniya, su ne wadannan masu fatan sharri ga duniya da suka hada da wannan haramtacciyar gwamnatin ta Isra’ila da kuma masu dauke mata gindi.

Ayatullah Khamenei ya ce: Tsarin Musulunci ba ya kiyayya hatta da al’ummar Amurka, duk kuwa da cewa gwamnatin Amurka tana nuna kiyayya, girman kai da kulla makirci ga al’ummar Iran da kuma tsarin Musulunci na Iran.

Jagoran ya ce: Abin da gwamnatin Musulunci ta Iran take kyama da kuma fada da shi, shi ne girman kai.

Daga nan kuma sai Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske dangane da wasu alamu da halaye na ma’abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka a da da kuma a wannan lokacin.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar girman kai dai, wata kalma ce ta Alkur’ani inda ya ce: Tsawon tarihi tushen girman kai guda daya ne, sai dai kawai hanyoyinsa ne kawai ya bambanta. Don haka wajibi ne a yi tsare-tsare da nuna hikima a dukkanin fagage ciki kuwa har da fagen fada da girman kai.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana akidar jin cewa mutum yana sama da sauran mutane a matsayin daya daga cikin siffofin ma’abota girman kai inda ya ce: A lokacin da wata kasa ko wata gwamnati ta dauki kanta a sama da sauran, to kuwa za a samar da wani yanayi mai hatsarin gaske ga yanayi na duniya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana jin cewa mutum yana da hakkin tsoma baki cikin lamurran cikin gidan sauran kasashen duniya, tilasta wa sauran al’ummomi mahangarsa da kuma da’awar jagorantar duniya, a matsayin wasu siffofi na ‘yan mulkin mallaka inda ya ce: Jami’an gwamnatin Amurka suna magana kai kace su din nan suna da iko kan al’ummomi da kuma duniya da wannan yankin baki daya.

Wata siffar ma’abota girman kan da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi bayaninta ita ce kin yarda da gaskiya.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin yadda ma’abota girman kai da kuma Amurka suke take hakkokin al’ummomin duniya, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: batun nukiliyan kasar Iran, daya ne daga cikin alamun irin take hakkokin al’ummomi da ‘yan mulkin mallakan suke yi.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Duk wani mutum ko kasa ma’abociyar hankali da girmama dalilai, suna yarda da gaskiya, amma ma’abota girman kai kan ba sa amincewa da gaskiya da kuma hakkokin sauran mutane, sannan kuma suna yin dukkanin abin da za su iya wajen take wadannan hakkokin.

Siffa ta gaba ta ma’abota girman kan da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da ita a jawabin nasa ita ce rufe ido wajen aikata duk wani nau’i na ta’addanci da zubar da jinin sauran al’ummomi ba tare da nuna wata damuwa ba, inda ya ce: ‘Yan mulkin mallaka ba sa girmama duk wasu al’ummomi da mutanen da suka ki mika musu kai. Don haka suke halalta aikata duk wani nau’i na danyen aiki a kansu.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da wasu misalai na irin danyen aikin da Amurka da Ingila suka aikata kan al’ummomin da suka mamaye su da mai she su bayinsu.

Ayatullah Khamenei yayi ishara da amfani da makaman kare dangi da Amurka ta yi a kan al’ummar Japan a matsayin wani misali na irin ayyukan ashsha na ma’abota girman kan duniya inda ya ce: A tarihin duniyar nan sau biyu kawai aka taba amfani da makaman kare dangi, wanda dukkaninsu Amurka ce ta yi amfani da su a kan al’ummar Japan. Amma duk da irin wannan danyen aikin da ta aikata, har ya zuwa yanzu Amurka tana ganin kanta a matsayin mai kula da batun da nukiliya a duniya.

Har ila yau Jagoran ya yi ishara da irin azabtar da al’ummomin kasashen Vietnam, Iraki, Pakistan da Afghanistan da Amurkan take yi yana mai cewa: Ko shakka babu al’ummomin duniya ba za su taba mantawa da irin azabar da mutane da Amurka ta yi a gidajen yarin Guantanamo da Abu Ghraib ba.

A ci gaba da bayanin hanyoyi da siffofin da ma’abota girman kai suka kebanta da su don gani hanyar da za a yi fada da su cikin hikima da sanin ya kamata, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da wata siffa ta ma’abota girman kan wadda ita ce yaudara da munafunci.

Jagoran ya ce: Fakewa da batun yin hidima wajen aikata danyen aiki, daya ne daga cikin hanyoyi da halayen ma’abota girman kai.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Amurkawa suna cewa idan da a ce ba a kashe mutane dubu 200 a hari (da makaman kare dangi) da suka kai wa garuruwan Hiroshima da Nagasaki (na kasar Japan) ba, to da kuwa ba a kawo karshen yakin duniya na biyu ba da kuma an kasha sama da mutane miliyan biyu a duniya. A saboda haka wannan hari da suka kai wa Japan, wata hidima ce ga bil’adama.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa suna fadin wannan karya mai ban mamaki ne a daidai lokacin da dukkanin bayanai suke nuni da cewa Hitler, wanda shi ne tushen wannan yaki na duniya ya kashe kansa ‘yan watanni kafin wannan harin da Amurka ta kai wa Japan. Sannan kuma kafin harin ne aka kama Mussolini, wanda daya ne daga cikin rukunan wannan yakin, sannan kuma watanni biyu ma kafin hakan, kasar Japan ta sanar da aniyarta na mika wuya.

Ayatullah Khamenei ya ce hakikanin lamarin shi ne cewa Amurka tana son ta gwada sabon makamin da ta yi ne a fagen daga na hakika, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba a Hiroshima da Nagasaki. Amma har ya zuwa yanzu a kafafen farfagandarsu suna bayyana wannan danyen aikin a matsayin wata hidima da suka yi ga mutanen duniya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin munafuncin da (Amurka da kawayenta) suka nuna dangane da batun amfani da makamai masu guba a kasar Siriya a matsayin daya daga cikin misalan irin yaudara da munafuncin ma’abota girman kan inda ya ce: A lokuta da dama shugaban kasar Amurka da sauran jami’an Amurkan sun sha bayyana amfani da makamai masu guba a matsayin jan layin da ba za su taba amincewa a tsallake shi ba. Amma sai ga shi ita kanta wannan gwamnatin ta Amurkan ba wai kawai ba ta nuna rashin amincewarta da hari da makamai masu guba da Saddam ya kawo wa al’ummar Iran ba, face ma dai sun ba wa Saddam alal akalla ton dari biyar na sinadarori masu guba masu hatsarin gaske, wadanda ya yi amfani da su a kan jaruman dakarun Iran.

Jagoran ya bayyana kashe kusan fasinjoji 300 a harin da jirgin ruwan yakin Amurka ya kai wa jirgin fasinjar Iran da kuma irin goyon bayan da Amurkan take ba wa Saddam a matsayin wani bangare na danyen aikin gwamnatin Amurkan, daga nan sai ya ce: Neman yaki da kokarin haifar da rikici da sabani tsakanin al’ummomi a matsayin wata siffar ta daban ta ma’abota girman kan.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya yi ishara da irin fada da ke gudana tsakanin sansanin gaskiya da sansanin ma’abota girman kai tsawon tarihi, sannan kuma ya yi karin bayani dangane da dalilan irin makirci da kuma adawar da ma’abota girman kai suke yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Dangane da hakan, Jagoran ya yi ishara da dalilan kafa jamhuriyar musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce: An kafa wannan juyin juya hali na al’ummar Iran da kuma tsarin da suka zaba ne bisa tushen nuna rashin amincewa da girman kai da kuma ‘yan amshin shatansa. A saboda haka, ko shakka babu ma’abota girman kan duniya ba za su taba hakura suna ganin wannan tsarin ba saboda irin wannan siffa da suke da ita da aka ambata a baya, sai dai idan har sun yanke kaunar ba za su iya samun nasara a kansa ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wajibcin sanya makiya su yanke kauna a matsayin tushen abin da zai kawo karshen makircin da makiya suke yi wa al’ummar Iran, don haka sai ya kirayi al’ummar Iran da cewa: Wajibi ne dukkanin al’ummar Iran, matasansu da dukkanin wadanda suke kaunar kasarsu, su yi dukkanin abin da za su iya wajen sanya yanke kauna cikin zukatan makiya da hana su ci gaba da wannan makirci na su.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: kokarin haifar da rikici na kabilanci, kokarin shirya juyin mulki, kwadaitar da Saddam da ya kawo wa Iran hari da kuma ba shi dukkanin taimakon da yake so, sanya takunkumi da sauran nau’oi na matsin lamba, dukkanin wadannan alamu ne na kiyayyar da Amurka take yi da al’ummar Iran wacce shekaru talatin da biyar din da suka gabata ta fara wani yunkuri na neman ‘yanci a wannan yanki mai muhimmanci na nahiyar Asiya, sannan kuma duk da irin kiyayyar da ake nuna mata, amma ta ci gaba da samun ci gaba da kuma zama abin koyi ga al’ummomi.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da rawar da shugaban kasar Amurka na yanzu ya taka wajen fitinar da ta kunno kai a kasar Iran bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2009, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske kan irin rawar da gwamnatin Amurkan ta taka wajen karfafa shafuffukan internet da hanyoyin sada zumunta irin su facebook da twitter da sauransu saboda tunanin da suke da shi na cewa za su taimaka wajen kifar da gwamnatin Musulunci ta Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana sanya takunkumi a matsayin wata hanya ta daban da makiya suke amfani da ita wajen dunkufar da al’ummar Iran inda ya ce: Matsalar wadancan mutanen ita ce cewa ba su fahimci wannan al’umma ma’abociyar imani da hadin kai ba, sannan kuma ba sa daukan darasi daga irin kashin da suka sha a baya.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Dukkanin irin nasarorin da muka samu da kuma irin kashin da ma’abota girman kai suka sha, suna nuni da cewa tsayin daka shi ne kawai hanya guda daya tilo ta magance irin matsalolin da makiya suke haifarwa. Wannan kuwa wani lamari ne da al’ummarmu suka fahimce shi da kyau.

Wani lamarin kuma da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya tabo cikin jawabin nasa, shi ne batun tattaunawar da Iran take yi da kasashen yammaci kan shirin nukiliyanta inda ya ce: Ni dai ina kara jaddada wajibcin goyon bayan gwamnati da jami’an gwamnati da wadanda suke gudanar da wannan tattaunawar, don kuwa ina daukar goyon bayan dukkanin gwamnatocin a matsayin wani nauyi da ke wuya na.

Jagoran ya ci gaba cewa: A baya na taba rike matsayin shugaban kasa, lalle na fahimci irin nauyi da wahalar da ke cikin shugabancin kasa, kuma na san cewa nauyin shugabancin kasa yana bukatar taimako da goyon baya. A saboda haka ko shakka babu zan ci gaba da goyon bayan gwamnati.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Koda yake a bangare guda kuma ina jaddada wajibcin kiyaye hakkokin al’ummar Iran ciki kuwa har da hakkin mallakar fasahar nukiliya. Lalle bai kamata a ja da baya kan hakkokin al’ummar Iran ba.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Ni dai ba na tsoma baki cikin tattaunawar da ake yi, to amma akwai wani jan layi da wajibi ne a kiyaye shi kuma bai kamata a tsalle shi ba. Wajibi ne a kan jami’an gwamnatin su kiyaye wannan jan layin. Bai kamata su tasirantu da farfaganda da kuma barazanar makiya ba.

Jagoran ya bayyana kiyayya da girman kan Amurka a matsayin babban dalilin irin takunkumin da ta sanya wa Iran inda ya ce: Wannan kiyayyar da Amurka take nuna wa al’ummar Iran wata kiyayya ce da take a fili, sannan kuma manufar matsin lambar da suke yi wa Iran ita ce ko za su sanya al’ummar su mika kai. To amma kuskure suke yi, don kuwa matsin lamba ba zai sa al’ummar Iran su mika kai ga wani ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Cikin yardar Allah, al’ummar Iran za su jure wa wanann matsin lambar sannan kuma za su mayar da hakan zuwa ga wata dama.

Jagoran ya ce: Takunkumi ba zai yi tasiri ba, su kansu Amurkawan sun san hakan, shi ya sa ma suke barazanar kawo hari na soji. Hakan kuwa abu ne da ke nuni da cewa takunkumi ba zai samar musu da abin da suke so ba.

Jagoran ya ce: Koda yake irin barazanar kawo harin soji da shugaban Amurka da sauran jami’an Amurka suke yi, abin kyama ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kamata yayi shugaban Amurka da sauran jami’an kasar su damu da matsalar tattalin arziki da bashin da ya yi musu kanta maimakon barazanar kawo wa al’ummar Iran hari. Su tafi su ci gaba da tunanin yadda za su magance matsalolinsu don kada a sake dakatar da ayyukan gwamnatin Amurkan.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Al’ummar Iran suna girmama dukkanin al’ummomi, to amma martanin al’ummar Iran ga makiya zai kasance martani ne mai sa su jin kunya, sannan kuma za su yi musu bugun mummuken da ba za su taba mantawa da shi ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana irin maganganun da jami’an Amurka suke yi da nufin faranta ran yahudawan sahyoniya a matsayin wani abin kunya a gare su inda ya ce: Ko shakka babu haramtacciyar kasar Isra’ila za ta kawu, don kuwa wata gwamnati ce da aka samar da ita sakamakon tilasci da amfani da karfi. Duk wani abin da aka kafa shi bisa tushe na tilasci da amfani da karfi kuwa ba zai dawwama ba.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi magana kan maganganun da wasu gwamnatocin kasashen Turai suka yi da nufin janyo hankali yahudawan sahyoniya da faranta musu rai inda ya ce: A wani lokaci a baya, al’ummar Faransa sakamakon tsayin dakan shugaban kasar na lokaci a gaban Ingila da Amurka, suna da wani matsayi na siyasa. Amma a halin yanzu jami’an gwamnatin Faransa ba wai kawai a gaban Amurka ba hatta a gaban azzalumar gwamnatin sahyoniyawa ma suna kaskantar da kansu wanda hakan abin kunya da kuma wulakantar da al’ummar Faransan ne. wajibi ne su sama wa kansu maganin hakan.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske kan ma’anar Basij da kuma irin nauyi da aikin da ke wuyan dakarun na Basij.

An fara wannan taron  ne dai da umurnin da Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musuluncin wanda kuma shi ne babban kwamandan sojin Iran, bayar na fara gudanar da atisayen da dakarun sa kai na Basij din suke gudanarwa da sunan ‘Kama Hanya Zuwa Baitul Mukaddas” a larduna guda 9 na Iran.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook