A+ R A-
26 May 2020

Jagora Ya Aike Da Sako Ga Taron Hadin Gwuiwan Kungiyoyin Daliban Iran A Turai Karo Na 48

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, cikin wani sako da ya aike wa mahalarta taron shekara shekara na hadin gwiwan kungiyoyin Musulunci na daliban Iran a jami’oin kasashen Turai karo na 48, ya bayyana cewar: ‘Ya’yan al’ummar Iran da a halin yanzu suke karatu a jami’oi daban-daban na duniya, tamkar wata bishiya ce da ta kama kasa wacce kuma da yardar Allah za ta ba da ‘ya’yanta masu amfani da kima ga al’ummar wannan kasar.

Abin da ke biye fassarar sakon Jagoran ne wanda wakilin Jagoran juyin juya halin Musuluncin kan harkokin daliban Iran da suke karatu a jami’oin kasashen Turai Hujjatul Islam wal muslimin Jawad Ejai ya karanta a wajen wannan taro da aka gudanar a Cibiyar Musulunci ta  Imam Ali (a.s) da ke birnin Vienna, babban birnin Austria:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 

Matasa da ‘ya’yan al’ummar Iran da a halin yanzu suke karatu a jami’oi daban-daban na duniya, haka nan sauran ‘yan’uwansu maza da mata da suke karatu a rayayyun jami’oin cikin gida, tamkar wata bishiya ce da ta kama kasa wacce kuma da yardar Allah za ta ba da ‘ya’yanta masu amfani da kima ga al’ummar wannan kasar.

Wannan shi ne abin da ya kamata ya zamanto abin tunani da kuma ba da himmar daliban Iran da suke karatu a bangarori daban-daban na duniya. Yadda kuke karatu da kuma bangaren ilimin da kuka zaba da kuma irin halayenku yayin karatun su ne za su bayyanar da yanayinku. A saboda haka wajibi ne ku yi riko da wannan tunani da tafarki mai haske da kuma tsara hanyar daga shi.

Wajibi ne, sama da komai, ku dogara da Allah da neman taimako da rahamarSa tsawon wannan lokaci mai cike da kumaji na sauyi daga dalibta a yau, zuwa ga jami’ai da fitattun mutane a gobe. Hakan shi ne abin da zai fadada kwarewarku da karfafa kokarinku sannan da kuma kwantar muku da zukatanku.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya tabbatar da makoma mai kyau a gare ku da kuma wannan kasa (ta mu).

 

Sayyid Ali Khamenei

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook