A+ R A-
26 May 2020

Jagora Ga Mahalarta Taron Hadin Kai: Rarrraba Kan Musulmi Shi Ne Abin Da Makiya Suka Sa A Gaba

A safiyar yau Lahadi (19-01-2014), wadda ta yi daidai da zagayowar ranar da aka haifi Manzon Musulunci Muhammad (s.a.w.a) da kuma Imam Ja’afar al-Sadiq (a.s), ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu manyan jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran, baki mahalarta taron hadin kan musulmi da kuma wasu gungun al’ummar Iran.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi kasashen musulmi zuwa ga aiwatar da abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke fatan gani daga wajen al’ummarsa yana mai cewa: A halin yanzu mafi muhimmancin lamarin da ya shafi duniyar musulmi, shi ne hadin kai a tsakaninsu. Duk kuwa da irin makirce-makircen da ake kulla musu, to amma hadin kai da farkawa ta muslunci za su iya samar da makoma mai kyau ga al’ummar musulmi.

Har ila yau kuma yayin da yake taya al’ummar musulmi murnar haihuwar Manzon Allah Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) da kuma Imam Ja’afar Sadiq (a.s), Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘yantar da kai daga wahami da munanan zato sannan da kuma kokari wajen ‘yantuwa daga zalunci da babakeren gwamnatoci ‘yan kama karya da samar da adilar hukuma a matsayin wasu koyarwar addinin Musulunci wajen ‘yantar da bil’adama yana mai cewa: Wajibi ne al’ummar musulmi su yi kokari wajen samar da ‘yanci na tunani sannan da kuma ‘yanci na siyasa, tabbatar da hukumomi na al’umma da tsarin demokradiyya na addini da ya ginu bisa koyarwa ta addinin Musulunci, wanda ta hakan ne za sa sama wa kansu irin ‘yancin da Musulunci yake so.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana makirce-makirce da yunkurin makiyan Musulunci wajen kawar a ‘yanci na hakika da kuma sa’ada ga al’ummar musulmi a matsayin wani lamari mai rudarwa wanda kuma yake da bangarori daban-daban, don haka sai ya ce: Haifar da rarrabuwan kai tsakanin musulmi shi ne babban aikin da ma’abota girman kan duniya suka sa a gaba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kokari na shekaru 65 da makiya suka yi wajen kawar da tunanin matsalar Palastinu da kuma tilasta wa al’ummar musulmi haramtacciyar kasar sahyoniyawa a matsayin daya daga cikin misalan irin kokari ba dare ba rana na Amurka da sauran ma’abota girman kan duniya inda ya ce: Yakukuwan kwanaki 33 a kasar Labanon da kuma na kwanaki 22 da kwanaki 8 a Gaza sun tabbatar da cewa in ban da wasu gwamnatoci wadanda a halin yanzu suka zamanto masu kare manufofi makiya, amma sauran al’ummar musulmi sun kiyaye matsayin Palastinu sannan sun nuna kiyayyarsu ga haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa da masu daure mata gindi.

A ci gaba da magana kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi duniyar musulmi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar gafalar da al’ummar musulmi daga batun Palastinu a matsayin daya daga cikin manufofin da ya sanya makiya haifar da yakin basasa da yada sabani da akidar kafirta juna da tsaurin ra’ayi na wuce gona da iri a tsakanin musulmi.

Har ila yau kuma yayin da yake nuna damuwarsa dangane da halin da musulmin suke ciki, Jagoran ya bayyana cewar: Wasu mutane masu akidar kafirta mutane, maimako su ba da himmarsu wajen fada da lalatacciyar gwamnatin sahyoniyawa, suna amfani da sunan Musulunci da shari’a suna kafirta mafi yawa daga cikin al’ummar musulmi da kuma share fagen yaki da rikici da sabani tsakanin musulmi. A saboda haka ne samuwar irin wannan kungiya, ta zamanto wani tukwuici ne ga makiya Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ayar nan ta Alkur’ani mai girma da take siffanta musulmi da cewa: “Su din nan masu tsanani ne ga kafirai, sannan kuma masu rahama a tsakaninsu” Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Wadannan mutane masu kafirta musulmi sun yi karen tsaye ga wannan aya ta Allah Madaukakin Sarki, sannan kuma ta hanyar rarraba musulmi zuwa gida biyu “musulmi da kafirai” sun hada su fada da yaki a tsakaninsu.

Jagoran ya yi tambayar cewa: A irin wannan yanayi da ake ciki, shin akwai wanda zai iya inkarin cewa kungiyoyin leken asirin gwamnatocin girman kan duniya da ‘yan amshin shatansu ne suka samar da wannan kungiya da kuma irin goyon baya na kudi da makami da suke samu?

A bisa haka ne Ayatullah Khamenei ya bayyana wannan yunkuri na kafirta musulmi a matsayin babban hatsari ga duniyar musulmi, sannan kuma yayin da yake jan hankulan kasashen musulmi da su yi  taka tsantsan da abin da ke faruwan ya ce: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu gwamnatocin musulmi sun rufe ido kan sakamakon wannan lamari wanda wutarsa ba za ta bar kowa ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar yaduwar sabani tsakanin Shi’a da Sunna da kuma karuwar rikici na cikin gida tsakanin musulmi cikin shekaru uku zuwa hudu na baya-bayan nan mayar da martanin azzaluman duniya ne ga irin karuwar farkawa ta Musulunci da ake samu a kasashen musulmi ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A kokarin da suke yi na dushe hasken irin wannan farkawa ta Musulunci da ake samu, ma’abota girman kai suna ta kokari wajen haifar da rikici tsakanin mabiya mazhabobi daban-daban na Musulunci da kuma karfafa ayyukan rashin imani irin su ‘cin hantar mutanen da aka kashe’ don bakanta hakikanin Musulunci a gaban idanuwan duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Ko shakka babu ba haka kawai kuma ba a lokaci guda kawai wadannan abubuwa suka faru ba, masu tinkaho da karfi na duniya tsawon lokaci suka yi suna shiri wajen samar da hakan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana fada da duk wani abin da ke haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi a matsayin wani babban nauyi da ke wuyan Shi’a da Sunna da sauran mazhabobi na Musulunci inda ya ce: ‘Yan siyasa, ‘yan boko da malaman addini suna da gagarumin nauyi a wuyansu wajen tabbatar da hadin kai a tsakanin musulmi.

Don haka ne Ayatulllah Khamenei ya kirayi malaman addini na kasashen musulmi da su ja kunnen al’umma dangane da mummunan sakamakon sabani na mazhaba sannan su kuma ‘yan boko su dau nauyin yin bayani wa daliban jami’oi muhimman manufofin Musulunci su kuma ‘yan siyasar kasashen musulmi zuwa ga dogaro da al’ummominsu da kuma nesantar makiyan Musulunci yana mai cewa: A yau hadin kai shi ne lamari mafi muhimmanci a duniyar musulmi.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin irin yadda al’ummar musulmi suka fara ficewa daga iko da mulkin ‘yan mulkin mallaka na kasashen yammaci, Jagoran ya bayyana cewar: Ma’abota girman kai suna kokari wajen tabbatar da abubuwan da suke samu a baya a lokacin mulkin mallaka na kai tsaye ta hanyar mulkin mallaka na siyasa da al’adu da tattalin arziki a halin yanzu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘farkawa da kuma fahimtar inda aka sa gaba’ a matsayin hanya guda kawai ta samun daukaka da sa’adar al’ummar musulmin duniya yana mai cewa: Albarkatun kasa daban-daban, kasantuwa a yanki mai muhimmanci, tarihi da ke cike da abubuwa masu muhimmanci da kuma tushen tattalin arziki maras tamka da kasashen musulmi suke da su, suna iya zama abubuwan da za su samar wa al’umma din daukaka da karama idan har musulmin suka hada kansu waje guda.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana nasarar da juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya samu da kuma tabbatar da abin koyi na Jamhuriyar Musulunci tsawon shekaru 35 din da suka gabata duk kuwa da makirce-makircen ma’abota girman kai a matsayin abubuwan da ke tabbatar da irin kyakkyawan makomar da al’ummar musulmi suke da ita, daga nan sai ya ce: Da yardar Allah al’ummar Iran da tsarin musulmi za su ci gaba da samun karfi da karfafa a kowace rana.

A karshen taron dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya shigo cikin baki mahalarta taron don gaisawa da su kai tsaye.

Tun da farko dai sai da shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake isar da sakon tayar murnarsa ga al’ummar musulmi dangane da zagayowar ranar haihuwar Cikamakin Annabawa (s.a.w.a) da Imam Ja’afar Sadiq (a.s), ya yi ishara da irin yanayin da duniya take ciki a lokacin jahiliyya yana mai cewa: A irin wancan lokaci, haihuwar Manzon Rahama (s.a.w.a) ta zamanto wani haske na shiriya ga al’umma.

Dakta Ruhani ya bayyana riko da kira zuwa ga hadin kai tsakanin musulmi da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi a matsayin hanya guda kawai ta samun tsirar al’ummar musulmi inda ya ce: Addini guda, Manzo guda, manufofi guda, makiya guda sannan da kuma batutuwa irin su Palastinu da aka mamaye da kuma masallacin Qudus mai alfarma suna iya zama abubuwan da za su iya hada musulmi waje guda.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa: Al’ummar musulmi, ta hanyar komawa ga Alkur’ani mai girma da kuma amfani da hankali, sanya fata cikin zuciya da kuma kokari ba kama hannun yaro, za su iya sake rayar da koyarwa da kuma wayewar Musulunci.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook