A+ R A-
25 May 2020

Jagora Imam Khamenei: Amurka Ba Ta Da Karfin Kifar Da Gwamnatin Musulunci Ta Iran

A safiyar yau Asabar (08-02-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan kwamandoji da jami'an sojin sama na Jamhuriyar Musulunci ta Iran don tunawa da ranar da kwamandoji da jami'an sojin Iran suka yi mubaya'a ga marigayi Imam Khumaini (r.a) a ranar 8 ga watan Fabrairun 1979, kwanaki uku kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979.

A lokacin da yake gabatar da jwabinsa a wajen wannan taron, Ayatullah Khamenei ya bayyana batun ‘yancin kai da fada da ma'abota girman kai da ‘yan mulkin mallaka a matsayin daya daga cikin tushe na asali na juyin juya halin Musulunci na Iran yana mai cewa: Irin maganganun rashin mafadi da jami'an Amurka suke yi sun zamanto darasi ga kowa. Wajibi ne al'ummar Iran su sanya idanuwansu sosai kan tattaunawar da ake yi da kuma irin maganganun da Amurkawa suke yi. Haka nan kuma yayin da yake ishara da riko da asalin koyarwar juyin juya halin Musulunci da mahangar marigayi Imam Khumaini (r.a) cikin kuwa hard a mahangarsa kan Amurka da kuma bayyanar da hakan a fili ba tare da wani noke-noke ba a matsayin abubuwan da za su lamunce da kuma kiyaye wannan ‘yancin kan da aka samu, Jagoran cewa ya yi: Sirrin tabbatuwa da kuma karfin tsarin Musulunci na Iran shi ne dogaro da imani, so da kauna da kuma iradar mutane. A wannan shekarar ma a yayin gangamin ranar 22 ga watan Bahman (ranar nasarar juyin juya halin Musulunci) al'ummar Iran da dukkan karfinsu za su rera taken juyin juya halin Musulunci sannan a wannan karon ma za su sake nuna wa duniya irin karfi da tsayin dakan da suke da shi.

Yayin da yake magana kan wannan mubaya'ar da sojojin saman suka yi wa marigayi Imam Khumaini a ranar 8 ga watan Fabrairun 1979, Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun sojin kasar Iran ya bayyana cewa wannan lamarin dai yana da bangarori daban masu cike da albarkoki. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wani bangare mai muhimmanci na wannan lamari na 8 ga watan Fabrairu, shi ne sake rayar shu'urin ‘yancin kai tsakanin dakarun sama kana daga baya kuma a tsakanin dukkanin sojojin. Don kuwa hakan ya zamanto abin da ya share fagen samar da ruhin yarda da kai da kuma dogaro da karfi na cikin gida da ake da shi.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin ma'anar ‘yanci, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da sabon salon mulkin mallaka da ‘yan mulkin mallakan suke amfani da shi ta hanyar amfani da ‘yan amshin shatansu maimaikon shigowa kai tsaye inda ya ce: Yayin da ake fada da wannan sabon mulkin mallakan, wajibi ne har ila yau kuma a yi fada da mulkin kama-karya da ke mulki da kuma masu daure musu gindi daga waje. Don kuwa fada da dan mulkin kama-karya sannan da kuma yin sulhu da ma'abocin girman kai, ba zai haifar da da mai ido ba.

Don haka ne ma Ayatullah Khamenei ya yi ishara da makomar wasu juyin juya halin da suka faru a wannan yanki na Gabas ta tsakiya yana mai cewa: Juyin juya halin da zai yi nasara shi ne juyin da ya fahimci masu karfi na bayan fagen da suke daure wa ‘yan mulkin kama-karyan gindi, sannan kuma yayi fada da ‘yan mulkin mallakan maimakon yin sulhu da su.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A saboda haka ne bayan kame tsohon ofishin jakadancin Amurka a Tehran da matasa mabiya tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a), Imam (r.a) ya bayyana hakan a matsayin juyin juya halin da ya fi na farko girma. Don kuwa wannan yunkurin yana nuni da cewa al'ummar Iran bayan sun kawar da gwamnatin dagutu, lalle sun fahimci matsala ta gaba da za su fuskanta don haka suka yi fada da ita.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wannan fahimtar da kuma fada da masu tsoma baki cikin lamurran cikin gida, ita ce hakikanin ma'anar ‘yanci.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Masu tinkaho da karfi da tsoma baki cikin lamurran cikin gidan kasashen duniya suna tsananin adawa da ‘yancin kan kowace kasa. A saboda haka ne a koda yaushe suke kokari ta hanyoyi daban-daban wajen raunana ruhin neman ‘yanci tsakanin al'ummomi da jami'ansu.

Jagoran ya ce daya daga cikin irin wadannan hanyoyi da suke bi ita ce sanya wa al'ummomin jin cewa ba za su iya samun ci gaba ba karkashin ‘yancin kansu yana mai cewa: kafafen farfagandar ‘yan mulkin mallaka da ‘yan amshin shatansu na cikin gida suna kokarin nuna wa mutane cewa dogaro da karfi na cikin gida koda wasa ba zai tafi tare da ci gaba ba. Don haka duk wata kasar da take son ci gaba, to wajibi ne ta yi watsi da ruhinta na neman ‘yancin kai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Lalle wannan kuskure ne, magana ce ta mutanen da suke adawa da ‘yancin kan kasashe.

Yayin da yake jaddada cewar ‘yancin kai ba yana nufin fada da duniya ba ne, Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: ‘yancin kai yana nufin tsayawa kyam ne a gaban tsoma bakin kasashen da suke son take manufofin al'ummomi don cimma manufofinsu.

Jagoran ya bayyana riko da tushe da koyarwar juyin juya halin Musulunci a matsayin abin da zai kiyaye irin ‘yancin kan da al'ummar Iran suke da shi, sannan kuma yayin da yake ishara da tarihin marigayi Imam Khumaini (r.a) ya bayyana cewar: Imam Khumaini (r.a) ba tare da wani noke-noke ba yake bayanin mahangarsa dangane da gwamnatin dagutu da irin mulkin kama-karyan da take yi da kuma bayyanar da wajibcin tabbatar da tsarin da ya ginu bisa koyarwar Musulunci. Haka nan kuma yake bayyanar da mahangarsa dangane da cibiyoyin sahyoniyawa masu mulkin duniya da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila ba tare da la'akari da wani abu ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A fili marigayi Imam Khumaini (r.a) ya nuna rashin amincewarsa da wannan tsari na kasa da kasa da ya yi amanna da raba duniya gida biyu wato ‘yan mulkin mallaka da wadanda ake mallakan, sannan kuma a fili yake bayyanar da mahangarsa ta fada da tushen wannan tsarin wanda ita ce gwamnatin Amurka.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: wannan shi ne tushen juyin juya halin Musulunci, kuma har ya zuwa yanzu bayan shekaru 35 ba a sauya wannan tushen da kuma manufar ba. Karkashin riko da wannan koyarwar ce tsarin Musulunci na Iran ya sami irin wannan ci gaba mai ban mamaki da ya samu sannan kuma ya zamanto mai fadi a ji a wannan yankin sannan kuma wani karfi mai tasiri a fagen kasa da kasa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsayin daka da kuma riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da al'ummar Iran suka yi ne ya sanya al'ummomin duniya ciki kuwa har da masanansu suke ganin su a matsayin jaruman al'umma masu gaskiya, fahimta, gwagwarmaya da kuma hakuri duk kuwa da siyasar kyamar Iran da cibiyoyin farfagandar kasashen ‘yan mulkin mallaka suke yadawa shekara da shekaru.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A halin yanzu ba wai ma kawai kauna da mutumcin al'ummar Iran bai ragu ba ne, face ma dai sun karu ne, a bangare guda kuma irin kyama da kiyayyar da al'ummomi suke yi wa Amurka sai karuwa suke yi.

Yayin da yake bayyana cewar sirrin ci gaba da riko da tafarkin juyin juya halin Musulunci da kuma tafarkin Imam Khumaini (r.a) da al'ummar Iran suka yi shi ne fitowa fili da bayyanar da matsayarsu da suke yi ba tare da tsoron wani ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Koda wasa bai kamata a yi watsi da irin wannan fitowa fili da bayyana matsaya ba shin a gaban masoya ne ko kuma a gaban makiya. Wajibi ne a yi bayanin matsaya da mahangar Jamhuriyar Musulunci a fili ba tare da shakka ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar akwai yiyuwar a sauya salon aiki, to amma tushe da koyarwar juyin kan ba abu ne da za a iya sauya shi, wanda wajibi ne a ci gaba da riko da su da dukkan karfin.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana fahimtar masoya da makiyan wannan juyi na Musulunci a matsayin wani lamari mai matukar muhimmancin gaske yana mai cewa: Wasu ‘yan tsirarru lalatattun masu tinkaho da karfi marasa mutumcin ne suke adawa da wannan juyin Musulunci na Iran, amma masoya wannan juyin kuwa su ne dukkanin al'ummomin da suka fahimci irin take da sakon da ke cikin juyin da kuma zaluncin da aka yi wa al'ummar Iran.

Yayin da yake ishara da irin goyon bayan da al'ummar Iran suke ba wa tsarin Musulunci na kasar da kuma rungumarsa da dukkan karfinsu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Jami'an Amurka a lokacin da suke tattaunawa da jami'an kasar Iran suna fadin cewa mu dai ba muna son kifar da gwamnatin Iran ba ne, alhali kuwa karya suke yi. Don kuwa idan da suna da karfin hakan, to ko shakka babu ba za su yi kasa a gwiwa wajen aikata hakan ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: wani dalilin gazawar Amurka wajen kifar da gwamnatin Musulunci ta Iran, shi ne imanin mutane da kuma irin kaunar da suke yi wa wannan tsarin da kuma iradarsu ta kare shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kasantuwa a fage da kuma irin goyon bayan da al'ummar Iran suke ba wa juyin juya halin Musulunci duk kuwa da gushewar shekaru 35 da nasarar juyin a matsayin wani lamari maras tamka cikin tarihin duniya inda ya ce: A ranar 22 ga watan Bahman kowa zai ga yadda al'ummar Iran za su fito fage a dukkanin garuruwa da kuma nuna wa duniya irin karfi da tsayin dakan da suke da shi.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana tsayin daka a matsayin sirrin irin ci gaban da al'ummar Iran suke samu, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Daya daga cikin alamun tsayin daka na kasa shi ne irin gagarumin taro da jerin gwanon al'umma irin su jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman da kuma zabubbukan da ake gudanarwa. A duk lokacin da al'umma suka bayyanar da irin tsayin dakansu na kasa a gaban makiya, to kuwa babu wani abin da makiyan za su iya.

Yayin da yake magana kan maganganun baya-bayan nan na jami'an Amurka dangane da kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Lalle wadannan maganganu (na jami'an Amurkan) wani darasi ne ga al'ummarmu. Ya kamata al'ummar Iran su dinga sanya ido kan wadannan maganganu na maras mafadi da jami'an Amurkan suke yi, don kowa ya fahimci makiyan da kyau.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin da wasu suke yi wajen sauya tunanin al'ummar Iran dangane da irin kiyayyar da Amurka take nuna wa Iran, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A cikin wadannan maganganun ma ana iya ganin irin kiyayyar da suke da ita. A tattaunawa ta bayan fage da suke yi da jami'an kasarmu, Amurkawa suna fadin wani abu, idan suka fito waje kuma wani abin na daban suke fadi. Hakan kuwa shi ne irin wannan harshen damon da bakar aniyar da suke da ita. Wajibi ne al'ummar Iran su sanya ido da kyau sosai.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wadannan maganganu a fili suna nuni da irin abubuwan da na sha jan hankulan jami'an gwamnati kansu, wato wajibcin kiyaye karfi na cikin gida. Abin farin cikin shi ne jami'an bangaren tattalin arziki na kasa sun fahimci cewa hanyar magance matsalolin da ake fuskanta ita ce karfafa irin kwarewar da ake da ita a cikin gida, sannan kuma sun fara share fagen wannan aikin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jaddada cewar: Hanya guda kawai ta magance matsalolin tattalin da ake fuskanta ita ce ba wa irin karfi na cikin gida da ake da shi muhimmanci, ba wai dogaro da kasashen waje da damfara fata kan dage takunkumi ba. Don kuwa babu yadda za a damfara fata kan makiya.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan maganganun da jami'an Amurka suke yi na nuna kauna ga al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A wannan bangaren ma karya suke yi. A bangare guda suna cewa muna kaunar al'ummar Iran, a bangare guda kuma suna yi musu barazana da kuma fatan ganin sun rage irin karfin kariyar da suke da shi. Lalle hakan wani wasa da hankali ne kawai.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Da yardar Allah al'ummar Iran da jami'an bangarori daban-daban na gwamnati musamman dakarun soji, za su ci gaba da kara irin karfin da suke da shi.

Ayatullah Khamenei ya bayyana dogaro da karfi na cikin gida a matsayin hanyar magance matsaloli na cikin gida daban-daban da ake da su a fagagen tattalin arziki, siyasa, zamantakewa da al'adu.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya gabatar da wasu nasihohi ga al'umma da kuma jami'an Iran.

Nasiha ta farko ita ce wajibcin kiyaye hadin kai tsakanin mutane da jami'an gwamnati da kuma nesantar ba wa kananan abubuwa na bayan fage muhimmanci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A yau babban abin da ke da muhimmanci a wajen al'ummar Iran shi ne samar da tsayin daka da karfi na cikin gida da kuma tsayin daka a gaban irin kiyayyar da ake nuna musu. Da yardar Allah al'ummar Iran za su yi nasarar magance wannan kiyayyar kamar yadda suka yi tsawon shekaru 35 din da suka gabata.

Nasiha ta gaba da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ta shafi masu sukan gwamnati ne da kuma su kansu jami'an gwamnatin inda ya kirayi masu sukar gwamnatin da su yi mata adalci da kuma kara hakuri don kuwa gwamnatin ta Iran ba ta jima da hawa karagar mulki ba, kamar yadda kuma ya kirayi jami'an gwamnatin da su yi hakuri da kuma bude zukatansu dangane da irin sukan da ake musu don magance matsalolin da ake da su.

Jagoran ya kirayi dukkanin al'ummar Iran da su yi riko da tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma toshe duk wata kafa da makiya za su so amfani da ita wajen cutar da kasar.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da babban hafsan hafsoshin sojin saman na Iran Admiral Hasan Shah Safi ya gabatar da jawabinsa inda ya gabatar da rahoto kan irin nasarori da ci gaban da dakarun saman suka samu. Babban hafsan hafsoshin sojin saman na Iran ya kara da cewa dakarun kasar Iran suna da karfin lalata makirce-makircen makiyan al'ummar Iran, kamar yadda kuma ya ja kunnen makiyan al'ummar Iran din da cewa za su fuskanci gagarumin mayar da martani daga wajen dakarun Iran a duk lokacin da suka yi kokarin kawo wa Iran hari.

 

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook