A+ R A-
13 July 2020

Sakon Jagora Imam Khamenei Na Sabuwar Shekarar 1393 Hijira Shamsiyya

Shimfida: A cikin sakonsa na sabuwar shekara ta 1393 hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana wannan sabuwar shekarar da sunan shekarar "Tattalin Arziki Da Al'adu Tare Da Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa".

Abin da ke biye fassarar wannan sakon na sabuwar shekarar ce da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar a yau 20 ga watan Maris, 2014:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 

Ya Mai sassauya zukata da idanuwa, Ya Mai jujjuya dare da rana, Ya Mai sauya karfi da yanayi, Ka sauya yanayinmu zuwa ga mafi kyawun yanayi.

Ya Ubangiji Allah, ka yi salati ga Fatima da mahaifinta da mijinta da 'ya'yanta.

Ya Ubangiji Allah, Ka zamanto majibinci, garkuwa, shugaba, mataimaki, mai shiryarwa da kuma nuna hanya ga Waliyinka, Al-Hujjat dan Al-Hasan, tsira da amincinka su tabbata a gare shi da kuma iyayensa, a wannan lokacin da kuma dukkanin lokuta har ka tabbatar da shi doron kasarka yana mai maka biyayya da kuma tabbatar da shi na tsawon lokaci.

Ya Ubangiji ka gaggauta bayyanarsa sannan ka sanya mu daga cikin masu goyon baya da taimaka masa da kuma ‘yan Shi'ansa.

Ina taya dukkanin ‘yan'uwana ‘yan kasar nan masu girma da kuma daidaikun Iraniyawa da suke a duk fadin kasar nan da kuma wadanda suke zaune a bangarori daban-daban na duniya, murnar shigowar sabuwar shekara. Haka nan kuma ina sake taya murna ta musamman ga iyalan shahidai masu girma, hakan nan ga sojojin da suka sami raunuka a fagen daga, haka nan ga matayensu da kuma dukkanin wadanda suka yi kokari kuma suke ci gaba da yi a tafarkin Musulunci da kuma ciyar da kasar Iran gaba. Haka nan ina taya dukkanin al'ummomin da suke gudanar da bukukuwan Norouz (sabuwar shekara) da kuma girmama wannan bikin (a duk fadin duniya).

Shigowar sabuwar shekarar bana ta yi daidai da lokacin juyayin shahadar shugabar matan duniyar musulmi, Siddiqatul Kubra (Fatima al-Zahra - tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta). Muna fatan insha Allahu, al'ummarmu za su amfana da albarkokin da ke tattare da hasken Fatima da kuma koyi da koyarwarta da sanya su cikin rayuwarsu don su haskaka kansu da hasken shiryarwa ta Ubangiji da aka ba wa dukkanin bil'adama kyautarsu ta hannun Nana Fatima al-Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) da Zuriyar Ma'aikin Allah (s.a.w.a).

Ya kamata gushewar shekaru daya bayan daya su zamanto mana wata kwarewa sannan kuma wata hanya ta samun basira. Mu dau darussa daga shekarun baya, sannan kuma mu kalli gobe da kuma makomarmu da idon basira da kuma zuciyar da take a farke don daukar matakan da suka dace da makomarmu. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa dukkanin al'ummar Iran masu girma lafiya ta jiki, ruhi da ke cike da farin ciki, kwanciyar hankali, ci gaba, daukaka, sa'ada da kuma rahamarsa cikin wannan sabuwar shekarar. Haka nan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa matasanmu karfin gwiwa da aiki tukuru, sannan mazaje da matayenmu kuma ya ba su himma da irada da karfafaffiyar azama wacce ta dace don shiga cikin fagage da hanyoyin da suke cike da nasarori da ababen alfahari; ya ba wa yaranmu farin ciki da lafiya; sannan ya ba wa iyalanmu tsaro da soyayya da tausayawa. Aikin da ke wuyanmu shi ne dubi da kuma waiwaye zuwa ga shekarun da suka gabata don daukar darasi da daukar matakan da suka dace saboda makomarmu.

An ba wa shekarar da ta gabata sunan "Shekarar Yunkuri Na Siyasa Da Karfafa Tattalin Arziki". Alhamdu lillahi a bangarori daban-daban na siyasa an gudanar da yunkuri na siyasa cikin mafi kyawun yanayi, shin a fagen zabubbuka ne ko kuma a lokutan gangami da jerin gwano daban-daban da aka gudanar; haka nan kuma a fagen shigowar mutane cikin fagage daban-daban da kuma irin kokarin da jami'an gwamnati da kuma mutane suka yi tsawon shekarar. Shekara ce da aka yi musayen gwamnatoci da ikon gudanarwa; wanda aka gudanar cikin dukkanin kwanciyar hankali da tsaro a kasar nan. Alhamdu lillahi an sake samar da wani sabon hadi da ya hada dogon tafarkin iko da gudanar da kasar nan.

A bangaren yunkuri na tattalin arziki kan aikin da ya wajaba a aikata da kuma irin fatan da ake da shi, lalle ba a samu hakan ba. An gudanar da ayyuka daban-daban, wanda abin godiya ne, amma babban aikin da ya kamata a aikata a fagen tattalin arziki har yanzu yana nan a kasa. Wajibi ne mu aikata hakan. Batun tattalin arziki wani batu ne mai muhimmanci ga kasarmu da kuma al'ummarmu; alhamdu lillahi a karshe-karshen shekara ta 1392, an gabatar da wani tushe na tunani don samar da wannan yunkuri na tattalin arziki; wato an sanar da siyasar ‘Tattalin arziki na gwagwarmaya" sannan kuma fagen cimma hakan, insha Allahu, a share yake.

Dangane da sabuwar shekara ta 1393, a tunanina abin da ke da muhimmanci sama da komai, abubuwa ne guda biyu: na farko shi ne dai wannan batu na tattalin arziki, na biyu kuma shi ne batun al'adu. A dukkanin wadannan fagage biyu, fatan da ake da shi, shi ne kokari da aiki tare tsakanin jami'an gwamnati da sauran al'umma. Ba za a iya cimma wannan fatan da ake da shi dangane da gina rayuwa da kuma ciyar da makoma gaba ba, in ba tare da shigowar mutane fage ba. A saboda haka baya ga ayyukan gudanarwa wanda wajibi ne jami'ai su gudanar, kasantuwar mutane a dukkanin wadannan fagage guda biyu wajibi ne; wato fagen tattalin arziki da kuma fagen al'adu. Ba za a sami ci gaba da kuma kai ga gacin da ake so in ba tare da kasantuwar mutane a fage ba. Mutane ta hanyar kungiyoyi daban-daban na mutane sannan da kuma tsayayyiyar irada da azama ta kasa za su iya taka gagarumar rawa. Su ma jami'ai don ciyar da ayyukansu gaba, suna bukatar goyon bayan mutane. Don haka wajibi ne su ma su shigo cikin fagen aiki suna masu dogaro da Allah Madaukakin Sarki da neman taimakonsa da kuma taimakon mutane; shin a fagen tattalin arziki ne haka nan kuma a fagen al'adun. Da yardar Allah a jawabin da zan gabatar gobe Juma'a zan yi karin bayani cikin dukkanin wadannan abubuwan. A saboda haka a tunani na babban abin da ke gabanmu a wannan sabuwar shekarar, shi ne ciyar da tattalin arziki gaba ta hanyar taimakon jami'an gwamnati da kuma mutane, haka nan kuma bangaren al'adu wanda shi ma da himmar jami'an gwamnati da sauran al'umma za a iya ciyar da shi gaba da kuma ayyana makomar kasarmu da kuma al'ummarmu. A saboda haka taken wannan shekarar da kuma sunan wannan shekarar shi ne "Shekarar Tattalin Arziki Da Al'adu Tare Da Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa".

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimaki al'umma da jami'an (kasar nan) masu girma don su sami damar aiwatar da aikin da ke wuyansu a wannan fagen; haka nan kuma ya sanya zuciya mai tsarki ta Waliyul Asr (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) ta yi farin ciki da mu; sannan kuma ya sanya ruhin Imaminmu mai girma (Imam Khumaini) da shahidanmu masu girma su yarda da kuma yin farin ciki da mu.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagoran

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook