A+ R A-
13 July 2020

Jagora Imam Khamenei A Jawabin Sabuwar Shekara: Duniya Ba Ta Tafiya Yadda Amurka Take So

A safiyar yau Juma'a (21-3-2004) ce, wadda ta yi daidai da ranar farko ta sabuwar shekarar 1393 hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan al'ummar Iran da suka taru a hubbaren Imam Ridha, amincin Allah ya tabbata a gare shi, da ke birnin Mashhad don taya su murnar shigowar sabuwar shekarar inda kuma yayi bayanin bangarori daban-daban na siyasar Iran a sabuwar shekarar da aka ba ta sunan "Shekarar Tattalin Arziki Da Al'adu Tare Da Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa" inda ya bayyana cewar: wajibi ne al'ummar Iran su yi karfin da masu takama da karfi na duniya ba za su iya take musu hakkokinsu ba.

Yayin da yake karin bayani dangane da asalin kiran da ya yi a wannan sabuwar shekarar, wato wajibcin samun karfin al'ummar Iran da tsayin dakansu don maganin bakar aniyar masu tinkaho da karfi na duniya inda ya ce: Amfani da karfi da tursasawa a kan raunanan al'umma, ita ce dabi'ar duniyar da ta ginu bisa koyarwa da tunani na abin duniya. Don haka wajibi ne mu yi karfi, don mu sami ci gaba.

Yayin da yake bayanin dalilin da ya sa shi sanya wa wannan shekarar ta 1393 sunan "Shekarar Tattalin Arziki Da Al'adu Tare Da Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa" a matsayin wata taswirar hanya ta gaba ta sabuwar shekarar ta 1393, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin kwarewa da kuma albarkatun kasa da Iran take da su inda ya ce: Aiwatar da wannan take daga bangaren jami'an gwamnati da kuma al'ummar kasa za ta haifar da gagarumar ci gaba bisa wannan tafarkin ci gaban kasa da aka rika.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin tushen karfin kowace al'umma, Jagoran ya bayyana wajibcin samun ci gaba a fagage daban-daban sai dai kuma ya ce: Tattalin arziki, al'adu da ilimi su ne tushe guda uku na karfin kowace al'umma wanda bisa taimakon Allah cikin shekaru sha biyun da suka gabata mun sami gagarumin ci gaba a fagen ilimi da fasaha.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ba da muhimmanci na musamman ga lamurran da suka shafi tattalin arziki da al'adu a matsayin lamarin da ya zama wajibi, don haka ne ma ya ba ware wani bangare mai yawa na jawabin nasa wajen karin haske kan wannan wadannan batutuwan.

Yayin da yake magana kan batun tattalin arzikin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: wajibi ne mu karfafa tattalin arzikin Iran ta yadda babu wani lokaci a duniya kuma babu wani mutum a ko ina yake a duniyar nan, shin Amurka ne ko kuma wanin Amurka, da zai iya cutar da tattalin arzikin Iran da rayuwar mutane sakamakon wata matsaya da zai dauka. Hakan kuwa shi ne wannan tattalin arziki na gwagwarmaya da muke magana kai.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da sanar da siyasar tattalin arzikin gwagwarmaya da aka yi da kuma maraba da hakan da shugabannin bangarori uku na gwamnatin Iran da sauran cibiyoyi suka yi, Jagoran ya yi karin haske kan wasu tambayoyi da wasu suke gabatarwa kan wannan lamari da kuma ba su amsoshinsu.

Tambayoyin dai su ne:

1- Mece ce siffofin wannan tattalin arziki na gwagwarmaya

2- Shin manufar da aka shata din mai yiyuwa ne ko kuma dai wani fata ne kawai da ake da shi?

3- Idan har mai yiyuwa ne, to wasu abubuwa ne ya wajaba a kula da su?

Yayin da yake amsa tambayar farko dangane da siffofin wannan tattalin arziki na gwagwarmaya, Jagoran cewa ya yi: tattalin arziki na gwagwarmaya wani abin koyi a ilmance da ya dace da bukatun kasashe. Tabbas da dama daga cikin kasashen duniya su ma sun dogara da wannan tsarin wajen rage irin tasirantuwa da tattalin arzikinsu ya ke yi da lamurra na zamantakewa da tattalin arziki da suke faruwa a duniya, daidai da irin yanayin da suke ciki.

Dogaro da karfi da albarkatu na cikin gida tare da kyautata alaka ta tattalin arziki da sauran kasashen duniya, ita ce siffa ta biyu da ta kebanci wannan siyasa ta tattalin arziki na gwagwarmaya da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da shi.

Jagoran ya kara da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu marubuta da masu bakin magana suna ta kokari wajen gabatar da wasu tambayoyi irin su takaita tattalin arzikin Iran da nufin toshe wannan hanya ta karfafa tattalin arzikin Iran da jin dadin al'umma, alhali kuwa tsarin tattalin arziki na gwagwarmaya zai yi mu'amala mai kyau da kasashen duniya.

Yayin da yake bayani siffa ta uku ta tsarin tattalin arziki na gwagwarmayar, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar wannan tsarin tattalin arzikin dai ba na gwamnati ba ne, tsari ne na al'umma, koda yake nauyin jami'an gwamnati ne su share fagen hakan da kuma sanya ido kan bugu da kari kan bude fagen da mutane za su shigo da zuba jarinsu.

Tattalin arzikin da ya ginu bisa ilimi da kuma amfanuwa da irin kwarewa da fasahar masana a fagen masana'antu da ayyukan gona suke da ita wani bangare ne na Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi bayaninsa don kara bayanin irin siffofin da wannan tsari ya kumsa.

Ba da muhimmanci ga adalci na tattalin arziki da zamantakewa tare kuma da kula da manyan siffofin da tattalin arzikin duniya suke kebanta da su irin su ci gaban kasa da abubuwan da ake samarwa a cikin gida bugu da kari kan tasirin tattalin arzikin gwagwarmayar cikin dukkanin yanayi, shin lokacin da ake cikin takunkumi ne ko kuma a'a, ita ce siffa ta karshe ta tattalin arzikin gwagwarmayar da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ita yayin amsa tambaya ta farko da ake gabatarwa.

Yayin da yake amsa tambaya ta biyu da ake gabatarwa ta cewa shin tattalin arzikin gwagwarmayar ba kawai wani fata da mafarki ba ne?, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya amsa wannan tambayar inda ya bayyana cewa lalle lamarin ba haka ba ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin gagarumin karfi na al'umma da ake da shi a Iran ciki kuwa har da irin matasan da ake da su, daliban da suka gama karatun jami'arsu da adadinsu ya kai miliyan goma, sama da wasu miliyan hudu da suke karatu a halin yanzu, ga kuma miliyoyin mutane da sauran kwararrun da suke da kwarewa a fagen masana'antu da sauransu, bugu da kari kan irin albarkatun kasa masu yawan gaske da kuma kima da ake da su, ga kuma waje maras tamka da ake, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke tabbatar da cewa ko shakka babu za a iya cimma manufar da ake da ita a wannan siyasa ta tattalin arziki na gwagwamaya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne wani ya ce to ai takunkumin da ake ciki ya hana amfanuwa da wadannan albarkatun da ake da su, to amma shin ba a cikin takunkumin ne muka sami ci gaba kala-kala a fagen ilimi da kariya ba da suka hada da fasahar nan ta Nano, fasahar makamashin nukiliya, ‘ya'yan halitta da makamai masu linzami na zamani da sauran ci gaba masu ban mamaki da muka samu ba?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Bisa wadannan hakikar, idan har muka karfafa azamarmu da kara damara, muka hada hannayenmu waje guda, muka rufe idanuwanmu daga dogaro da makiya da jin cewa yaushe ne za su dage mana takunkumi ko kuma ma ba za su dage ba, to ko shakka babu za mu cimma nasarori a fagage da dama ciki kuwa har da fagen tattalin arzikin.

Wajiban cimma wannan tsari na tattalin arzikin gwagwarmaya ita ce tambaya ta uku da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ware wani lokaci cikin jawabin nasa na sabuwar shekarar don amsa ta.

Amsar da Jagoran ya bayar a wannan fagen ta ba da muhimmanci ga wasu batutuwa guda hudu: 1- Goyon bayan samar da kayayyakin cikin daga wajen jami'an gwamnati a matsayin tushen ci gaban kasa. 2- Ba da muhimmanci ga kayayyakin da ake samarwa a cikin gida daga bangaren masu zuba jari. 3- Fifita bangaren samar da kayayyakin da ake bukata maimakon fifita sauran bangarori daga bangaren masu zuba jarin. 4- Ba da muhimmanci ga batun amfani da kayayyakin da aka samar a cikin gida.

Yayin da yake karin bayani kan wadannan abubuwa guda hudu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Mu ba muna cewa sayen kayayyakin waje haramun ne ba, to amma muna fadin cewa amfani da kayayyakin da ake samar da su a cikin gida wani wajibi ne kuma lamari ne mai muhimmanci wajen karfafa tattalin arziki da kuma ci gaban kasa. Hakan yana yin tasiri cikin dukkanin lamurra da suka hada da samar da aikin yi da kara kyautata kayayyakin da ake samarwa a cikin gidan. Tabbas nauyin da ke wuyan jami'an gwamnati ya dara na sauran mutane.

Bayan dukkanin wadannan bayanan da kuma muhimmancin da ke cikin aiki tare tsakanin gwamnati da sauran al'umma wajen karfafa tattalin arzikin na Iran, daga nan kuma sai Jagoran ya koma ga bangaren al'adu wanda ya ce: Hakan ma ya fi batun tattalin arziki muhimmanci.

Yayin da yake karin haske kan dalilan muhimmancin al'adun, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Al'adu tamkar iskar da muke shaka ne wanda ko muna so ko ba ma so dole ne mu shaka. A saboda haka idan har tana da kyau ko kuma ta gurbata, to kuwa za ta yi tasiri mabambanta cikin al'umma da kuma kasar nan.

Haka nan kuma yayin da yake kafa hujja dangane da tasiri maras tamka na al'adu a mahangar mutane, Jagoran ya yi ishara da batutuwa irin su samar da kayayyakin bukata na cikin gida, girmama dokoki da kuma iyali, inda ya ce: Dukkanin halaye na yau da kullum, dabi'u, mahangar tattalin arziki, zamantakewa da siyasa na mutane dukkaninsu sun samo asali ne daga al'adu. A saboda haka al'adu suna da alaka da dukkanin batutuwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar irin muhimmancin da makiya suke ba wa lamarin al'adu da kokarin cutar da wannan bangare da suke yi ya samo asali ne daga irin gagarumin muhimmancin da hakan yake da shi, daga nan sai ya ce: Wajibi ne jami'an bangaren al'adu su sanya ido sosai ga wannan bangare mai matukar muhimmanci na ala'du, sannan kuma yi aiki da nauyin da ke wuyansu.

Yayin da yake ishara da gazawar da ake nunawa a bangaren al'adun, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya bayyana cewar: Ba wai dukkanin matsaloli na al'adu da muke da su ne suka samo asali daga ayyukan makiya ba, to amma bai kamata a yi inkarin irin makirce-makircen da makiyan suka kulla mana tsawon shekaru talatin da ukun da suka gabata ba ko kuma a rufe ido kansu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ‘yanci a matsayin daya daga cikin take na asali na juyin juya halin Musulunci kuma tushen Jamhuriyar Musulunci inda ya ce: Irin muhimmancin da jami'ai suke bayarwa ga batutuwan da suke lalata al'adun mutane, koda wasa bai yi hannun riga da batun ‘yanci ba. Don kuwa akwai bambanci tsakanin ‘yanci wannan wata babbar ni'ima ce ta Ubangiji da kuma rufe iko da nuna halin ko in kula ga lamurra masu lalata al'umma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce ‘yanci ba tare da wasu kan iyakoki da dokoki ba, ba shi da wata ma'ana, yana mai ishara da wasu kan iyakoki da ba a tsallake su da kasashen yammaci masu ikirarin kare ‘yancin fadin albarkacin baki suka shata inda ya ce: A kasashen Turai mutum bai isa ya sanya alamun tambaya kan batun holocaust (kisan kiyashin da aka ce wai an yi wa yahudawa a Turai) wanda babu wani tabbas dangane da faruwarsa, to amma kuma suna fatan za mu rufe idanuwanmu dangane da iyakokin Musulunci da juyin juya halin Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da karin bayani kan wasu lamurra da cewa: Idan wani yayi isgili da ruhin ‘yancinmu na kasa, ya kwadaitar da dogaro da wasu, ya ci mutumcin tushen kyawawan halaye da addini na al'ummarmu, ya ci mutumcin take na asali na wannan juyin, ya kaskantar da harshen farisanci da ababen girmamawa na kasa, ya yi kokarin yada lalata a tsakanin al'umma da kuma raunana ruhin daukaka ta kasa ta matasan Iran, to shin sai mu rufe ido kan wadannan ayyuka nasa na rusa al'umma?

Haka nan kuma yayin da yake ishara da rashin juriyar da kasashen yammaci suke nunawa ga batutuwa irin su hijabi da kuma kabilanci da wariya da kasahen yammaci suke nuna wa wasu al'ummomin, Jagoran cewa yayi: dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da irin jurewar da kasashen yammaci suke da ita, wanda wasu suke kokarin kwadaitar da al'ummar Iran su yi koyi da su.

Bayan karin bayani kan nauyi mai girman gaske da ke wuyan jami'an bangarori daban-daban na al'adu, Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bangare mafi muhimmanci na magana a bangaren al'adu ta shafi matasanmu muminai da riko da koyarwar juyi wadanda suke gudanar da ayyukansua fagen al'adu wadanda kuma sun aikata ayyuka masu kyaun gaske. Jagoran ya kiraye su da su ci gaba a wannan aiki da suke yi da dukkan karfinsu. kamar yadda kuma ya yi kira ga wadanda suke gudanar da ayyukansu a bangaren al'adun da suka hada da malaman addini, malaman jami'a, ‘yan boko masu riko da koyarwar juyi da su ba da himma ga bangaren al'adu da kuma yin karin bayani wa al'umma kan batutuwan da suka shafi al'adunsu.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da sanya wa shekarar bara ta 1392 sunan "Shekarar Yunkuri Siyasa Da Karfafa Tattalin Arziki" da aka yi yana mai cewa: a bangaren yunkuri na siyasa lalle mutane sun yi abin da ke fatan gani daga wajensu ta hanyar wasu abubuwa guda biyu da suka yi. Na farko shi ne a lokacin zaben shugaban kasa karo na sha daya, na biyun kuma shi ne gagarumin jerin gwano da gangamin da suka yi a duk fadin kasar Iran a ranar 22 ga watan Bahman.

Jagoran ya ce: Batu mai muhimmanci cikin zaben a gwamnatin Musulunci ta Iran shi ne cewa tun daga nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yau, yanayin fitowar mutane a wajen zaben bai taba yin kasa ba. A wannan zabe na shugaban kasa karo na 11 kashi 72 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'ar ne suka fito, wanda hakan wani lamari ne mai girman gaske.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Ma'anar fitowar mutane a yayin zaben wani lamari ne da ke tabbatar da tsarin demokradiyya na addini a Iran, wanda wajibi ne a girmama wannan ni'ima mai girma ta Ubangiji. To sai dai abin bakin cikin shi ne cewa wasu a shekara ta 2009 sun yi butulci ga wannan babbar ni'ima ta Ubangiji.

Daga nan kuma sai Jagoran ya yi karin haske dangane da gagarumar fitowar da al'ummar Iran suka yi a lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman ta shekarar 1392 don tunawa da shekaru 35 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce wannan fitowa da al'umma suka yi ta samo asali ne saboda siyasar ma'abota girman kai da kuma cin mutumcin al'ummar Iran da jami'an Amurka suke yi.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar nukiliya, ‘yan siyasar Amurka cikin rashin ladabi suna kokarin nuna cewa al'ummar Iran sun dawo daga rakiyar koyarwar da suka rika. To hakan sai ya kara wa al'ummar Iran karfin gwiwan ci gaba da fitowa da shigowa fage don su nuna wa duniya cewa suna nan daram kan koyarwar Jamhuriyar Musulunci da kuma tsarin Musulunci.

A karshen jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da rashin nasara da shan kashin da Amurka take fuskanta a bangarori daban-daban na duniya ciki kuwa har da kasar Palastinu, Siriya, Iraki, Afghanistan da Pakistan inda ya ce: Hakikanin abin dake gudana a duniya ba yadda Amurka take so ba ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: A kasar Iran ma, shekaru talatin da biyar kenan suke nuna kiyayya ga al'ummar Iran, to amma albarkacin kasantuwar al'umma a fagen sun gagara cimma abin da suke so.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Manyan masu fadi a ji a gwamnatin Amurka a fili suke fadin cewa mun kara tsananta takunkumi ne don mutane su fito kan tituna wajen tinkarar tsarin Musulunci da kuma kawo karshen juyin juya halin Musulunci, to amma irin fitowa da kuma basirar al'umma ta sake sanya sun sha kasha.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi fatan alheri da makomai mai kyau ga al'ummar Iran musamman matasan kasar.

Kafin jawabin Jagoran dai, sai da Ayatullah Wa'iz Tabasi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musuluncin kuma mai kula da haramin Imam Ridha (a.s) ya gabatar da jawabin maraba da jagoran.

Mun Dauko Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagoran

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook