A+ R A-
25 May 2020

Jagora Ya Gana Da Gungun Mata Masana Don Tunawa Da Ranar Haihuwar Fatima al-Zahra (a.s)

A safiyar yau Asabar (19-04-2014) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan mata masana na Iran don tunawa da zagayowar ranar haihuwar ‘yar Manzon Allah, Sayyida Fatima al-Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta).

Yayin da yake taya mahalarta taron murnar zagayowar ranar haihuwar Sayyida Fatima al-Zahra (a.s), Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana haduwar ranar haihuwar Fatima al-Zahra (a.s) da makon mat da ranar girmama uwa a matsayin wata dama ta daukar darasi daga rayuwar shugabar matar duniya da lahira Sayyida Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da “isma” (tsarkaka daga aikata zunubi da sabo) da matsayi na kusaci da Ubangiji da Sayyida Fatima al-Zahra (a.s) take da shi, shi din ma a irin wadannan ‘yan shekaru da take da su, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Wajibi ne a kutsa cikin rayuwar Shugabar matar duniya don daukar darasi da abubuwan koyi irin su tsoron Allah, tsarki, kokari da jihadi, iya zama da miji, tarbiyyar yara, siyasa da kuma kasantuwa cikin fagage masu muhimmanci na rayuwa, daga rayuwar na ta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kasantuwar dubun dubatan mata masana a Iran a matsayin wata ni’ima ta Ubangiji sannan kuma daya daga cikin abubuwan alfahari na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce: Wannan hakika ce maras tamka a tarihin kasar Iran wacce kuma ta samo asali albarkacin riko da koyarwar Musulunci da kuma hangen nesar marigayi Imam Khumaini (r.a).

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin rawa da gudummawar da matan Iran suka bayar a lokacin kallafaffen yaki a matsayin wani lamari mai muhimmanci da kuma haskaka tarihin Iran, don haka sai ya jinjina wa irin hakuri da tsayin dakan da iyaye da matayen shahidai da sojojin da suka sami raunuka a wajen yakin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu mahanga da lamurra guda uku masu muhimmanci da suka shafi lamarin mace a cikin al’umma da kuma yin karin haske kansu:

Na farko: Ta ya ya za a iya amfanuwa da gagarumar rawar da mace take takawa ta ingantacciyar hanya sannan kuma wacce ta dace?

Na biyu: Ta ya ya za a iya amfanuwa da batun jinsi da irin damar da ake da ita a wannan fagen wajen samun daukaka ba wai lalata bil’adama ba.

Na uku: Bisa la’akari da bambancin da ake da shi tsakanin jinsin mace da namiji, wasu abubuwa ne za a karfafa su a cikin al’umma da za su kawo karshen zaluncin da ake yi wa mace a cikin iyali da kuma al’umma?

A saboda haka ne Jagoran ya bayyana mace da iyali a matsayin wasu batutuwa guda biyu da ba za a iya taba raba tsakaninsu ba inda ya ce: Duk wanda ya raba lamarin mace da lamarin iyali, to kuwa zai fuskanci matsalar gano hakikanin matsalar mace da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa daga cikin lamurran da suka zama wajibi a ba su muhimmanci yayin da ake dubi cikin lamurran da suka shafi mace da kuma hanyoyin da za a bi wajen karfafa iyali har da batun nesantar irin tunani da mahangar kasashen yammaci dangane da mace. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Saboda wasu dalilai mabambanta, kasashen yammaci sun yi mummunar fahimtar lamarin da ya shafi mace, to amma duk da haka sun ci gaba da yada wannan mummunar fahimta ta su a duniya da kuma toshe kafar da wasu za su fadi mahangarsu kan mace.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk da cewa wajibi ne a yi nazari da fahimtar bangarori daban-daban na mahangar kasashen yammaci dangane da mace, to amma wajibi ne a yi tsayin daka wajen kawar da tushen wannan tsohon tunani da ake kokarin nuna shi a matsayin sabon abu sannan kuma wanda ke cike da ha’inci amma a rigar nuna so da kauna da tausayawa. Don kuwa ko shakka babu, babu yadda za a yi wannan tunanin ya shiryar da al’umma da kuma samar wa bil’adama da sa’ada.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin mahanga ta abin duniya da nesantar koyarwa ta Ubangiji a matsayin ummul aba’isin din wannan kauce wa hanya na wannan tunani na kasashen yammaci kan mace, yana mai cewa: Irin kallo na kayan kasuwanci da karfafa tattalin arziki da ake yi wa mace da kuma mayar da ita wata hanya ta biyan sha’awar namiji, wani tushe ne na daban da ya gina tunanin kasashen yammaci dangane da mace da ke cike da zalunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kafa hujja da wasu makaloli da littafa da aka buga a kasashen yammaci da suke magana dangane da yanayin mace don karfafa wadannan maganganu da yayi yana mai cewa: Matukar muna son mahangarmu dangane da mace ta zamanto wata mahanga lafiyayyiya, wacce ta yi daidai da hankali da kuma share fagen magance matsalolin da ake fuskanta, to wajibi ne mu nesanci tunanin kasashen yammaci dangane da mace irin su (amfani da mace don) don kasuwanci da samar da aikin yi da kokarin nuna daidaito da cewa babu wani bambanci tsakanin mace da namiji.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce da wani dalili da kuma hankalin ne za a tilasta wa mata shiga cikin wasu fagage da ba abin da za su haifar musu in ban da wahala alhali kuwa Allah Madaukakin Sarki, sakamakon irin jiki da yanayinsu, ya halicce su saboda wani bangare na rayuwa?

Don haka sai Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin mahangar Musulunci dangane da mace yana mai cewa: A cikin batutuwa masu dama ciki kuwa har da batun kyautata ruhi da neman kusaci da Ubangiji babu wani bambanci tsakanin mace da namiji. To amma akwai bambancin gini da kuma jiki tsakanin mace da namiji, don haka a hankalce za a iya samun bambanci a wasu bangarori na rayuwar.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi kakkausar suka ga tushen tunanin mafi yawa daga cikin cibiyoyi na kasa da kasa dangane da lamarin da ya shafi mace inda ya ce: Tsayin dakan da kasashen yammaci suka yi wajen riko da wannan tushe da ke cike da kuskure shi ne ki gaba da haifar wa bil’adama da matsaloli. A saboda haka wajibi ne a kaurace wa irin wannan tunanin don a sami isa ga ingantaccen tushe da kuma mahangar da ta dace.

Har ila yau kuma yayin da yake karin haske kan batu na biyu da ya zama wajibi a yi riko da shi wajen samar da ingantaccen tunani da ya shafi mace, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wajibcin riko da koyarwar Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Dangane da batun mace, bai kamata a yi riko da duk wani abin da aka bayyanar da shi da sunan addini, wajibi ne a yi riko da koyarwar da suka yi daidai da Alkur’ani da Sunnar Ma’aiki da kuma sanya su a matsayin tushe.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana nesantar kananan abubuwa da kuma batutuwa da ake ganinsu a matsayin rassa da kuma riko da batutuwa da su ne na asali a matsayin batu na uku da wajibi ne a yi riko da shi wajen samar da ingantacciyar mahanga da hanyar da za a bi wajen magance matsalar mace. Jagoran ya ce: Batun iyali musamman ‘zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankalin mace a cikin iyali’ wani lamari ne na asali da wajibi ne a yi riko da shi da kuma ba shi muhimmanci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a gano abubuwan da suke hana kwanciyar hankali a cikin iyali da kuma kawar da su ta hanyoyin da suka dace ciki kuwa har da kafa dokoki da kuma wayar da kan mutane ta hanyar da ta dace.

Har ila yau kuma Ayatullah Khamenei ya bayyana rashin jin dadinsa da irin mahangar da ake da ita a da da yanzu da ke nuna mace a matsayin wata halitta mai daraja ta biyu kana kuma mai hidima ga namiji inda ya ce: wannan mahangar ta yi hannun riga da mahangar Musulunci dangane da mace.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu mutane, wai don kada su bata ‘yan kasashen yammaci rai, sai su dauko wasu abubuwan daga Musulunci su cakuda su da wasu tunanin kasashen yammacin, lalle wannan ba abin amincewa ba ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana neman ilimi da kuma daukaka a matsayin wasu lamurra da suka zama wajibi ga mace yana mai cewa: Sabanin wasu mahangar, yin aikin (gwamnati ko a wani kamfani) ba shi daga cikin asalin aikin mace, to amma matukar yin aiki da jagorantar wasu ma’aikatu, ba zai cutar da asalin aikin mace wanda shi ne kula da gina iyali ba, to babu matsala cikin hakan.

Jagoran ya kara da cewa: Hana mata yin wasu ayyuka ba kaskanci ko nakasa ce a gare su ba, face kuskuren shi ne a ba su aikin da bai dace da irin halittar da Ubangiji ya yi musu ba.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar mata masu fahimta wadanda kuma suka yi karatu su ne suka fi dacewa da bin diddigi da gudanar da ayyukan da suka shafi mace, don haka ya kiraye su zuwa ga kokari a wannan fagen.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai sai da Malama Maulawardi, mataimakiyar shugaban kasar Iran kan lamurran da suka shafi mace da iyali ta gabatar da jawabinta da kuma gabatar da rahoto kan irin ayyukan da suka gudanar inda ta ce matan Iran suna cikin mafi kyawun yanayi na lafiya da kwanciyar hankali wajen gudanar da ayyukan da suka shafi mace, kamar yadda kuma suna cikin shirin da ya dace wajen taka gagarumar rawa don cimma taken da aka ba wa wannan shekarar ta bana wato "Shekarar Bunkasa Tattalin Arziki Da Al'adu Tare Da Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa".

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook