A+ R A-
28 February 2020

Imam Khamenei: Kokarin Haifar Da Sabani Na Mazhaba Kaifafa Takobin Makiya Ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wani adadi na mawaka da masu yabon Ahlulbaiti (a.s) a Husainiyar Imam Khumani (r.a) da ke gidan Jagoran don tunawa da ranar haihuwar shugabar matar duniyar da lahira, ‘yar Manzon Allah, Sayyida Fatima al-Zahra (a.s) da jikanta marigayi Imam Khumaini (r.a).

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan taron, Jagoran ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Sayyida Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta, da jikanta marigayi Imam Khumaini (r.a) (wanda shi ma aka haifa a irin wannan ranar) inda ya bayyana ‘kokari’, ‘himma’ da kuma ‘tsarkakakkiyar rayuwa’ a matsayin manyan darussan da za a iya dauka daga rayuwar Fatima al-Zahra (a.s) ga bil’adama. Daga nan kuma sai ya ce: Majalisi na addini wata gagarumar dama ce maras tamka ta bayanin darussa masu muhimmanci na rayuwar gwaraza na addini. A saboda haka wajibi ne a yi amfani da wannan dama wajen isar da wadannan darussa masu wayar da kai, farkar da al’umma, sanya fata cikin zukatata da tabbatar da hadin kai (tsakanin musulmi) ta hanyar da dace da kuma kiyaye iyakoki na shari’a a irin wadannan tarurruka na addini wajen fada da makircin makiyan Musulunci da kuma ciyar da manufofin tsarin Musulunci gaba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gudanar da tarurrukan tunawa da Imamai a tsarin Musulunci a matsayin wata dama abar amfanuwa sannan kuma wata babbar ni’ima ta Ubangiji inda ya ce: Duk da cewa kwakwalwar bil’adama ba za ta iya fahimtar bangaori na kusaci da Allah na manyan bayin Allah irin su Fatima al-Zahra (a.s) da kyau ba, to amma wajibi ne a sanya halaye da dabi’unsu su zamanto abin koyi wajen isa ga manyan manufofi na zamantakewa da ke gabansu.

Jagoran ya bayyana samar da kyakkyawar rayuwa ta Musulunci da al’umma ma’abociyar ci gaba, ‘yanci, ‘yancin kai da kyawawan halaye da hadin kan al’umma da kuma tsoron Allah da nesantar abubuwan da ya haramta a matsayin wasu daga cikin manufofin tsarin Musulunci, daga nan kuma sai ya ce: Za a iya tabbatar da irin wannan al’umma ce kawai ta hanyar kaskantar da kai a gaban Allah da kokari da nesantar ragwantaka da kuma rashin yanke kauna.

Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da kokari ba kama hannun yaro da makiyan juyin juya halin Musulunci na Iran suke yi wajen lalata akidu da abubuwan da mutane suka yi imani da su da kuma kawar da su daga tafarkin tsarin musu ta hanyoyi daban daban na zamani da sadarwa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Manufar makiyar ita ce dunkufar da Musulunci da kuma hana koyarwar Shi’anci da ‘yan Shi’a zama abin koyi ga sauran al’ummomin duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tsarin Musulunci yana da kayan aikin fada da wannan makirci mai rikitarwa na makiya, wanda irin wadannan tarurruka na addini da jawaban da malamai da mawaka suke yi a kan mimbarori, daya ne daga cikin irin wadannan kayan aikin marasa tamka.

Jagoran ya bayyana rashin amfanu yadda ta dace da wadannan kayan aiki da kuma damar da aka samu butulci ne ga wannan ni’ima ta Ubangiji, daga nan kuma sai ya ce: Matukar dai sakamakon wake da wa’azuzzukan masu wa’azi suka zamanto masu kashe gwiwan al’umma, ba su zamanto masu wayar da kan al’umma ba, to kuwa an lalata wannan dama da aka samu kenan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cutar da hadin kai da kuma kokarin haifar da fitina da rarrabuwan kai tsakanin Shi’a da Sunna a matsayin daya daga cikin alamun butulci da kafircewa wa ni’imar Ubangiji daga nan sai ya ce: A lokuta da dama na sha fadin cewa a tarurruka na addini bai kamata a dinga fadin abubuwan da za su tunzura mutane a bangaren mazhaba ba. Don kuwa a fili yake cewa haifar da sabani da rarrabuwa kai tsakanin musulmi, tamkar wani takobi ne a hannun makiyan Musulunci, za su amfani da hakan wajen cimma manufofinsu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kiraye-kirayen da manyan malamai da masana na duniyar musulmi suke yi dangane da wajibcin hadin kai tsakanin musulmi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Mu muna alfahari da cewa mu din nan ‘yan Shi’an Ali ne, haka nan kuma muna alfahari da cewa Imaminmu mai girma (Imam Khumaini) shi ne ya daga tutar riko da wilaya wanda hakan ne ya sanya musulmin duniya, ‘yan Shi’a da wadanda ba Shi’a ba, suke alfahari da addininsu na Musulunci. To amma bai kamata mu kaifafa takobin makiyan Musulunci ta hanyar aikata wani abin da zai haifar da rarrabuwan kai tsakanin Musulunci ba.

Kira na gaba da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi wa mawaka da masu yabon Ahlulbaitin shi ne wajibcin kiyaye kan iyakoki na shari’a a wajajen da ake gudanar da tarurruka na addini.

Daga karshe dai Ayatullah Khamenei ya bayyana zaban maudhu’ai da suke cike da koyarwa da kuma wayar da kan al’umma a matsayin wani lamari da ya zama wajibi mawaka da masu yabon Ahlulbaitin su kula da shi yayin da suke tsara wakokin na su.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin sai da wasu mawaka da masu yabon Ahlulbaiti su 8 suka gabatar da wakensu kan matsayi da falolin ‘yar Manzon Allah, Sayyida Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook