A+ R A-
25 May 2020

Jagora Imam Khamenei: Masu Kafirta Musulmi Hatsari Ne Ga Musulmi, Sunna Da Shi'a

A safiyar yau Litinin (12-5-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da firayi ministan kasar Pakistan Nawaz Sharif da ‘yan tawagarsa da suka kawo masa gaisuwar ban girma a gidansa da ke birnin Tehran.

A lokacin da yake jawabi a yayin ganawar, Jagoran ya bayyana tarayyar da al’ummomin kasashen Pakistan da Iran suka yi a bangaren al’adu da addini a matsayin babban dalilin kyautatuwar alaka tsakaninsu, sannan kuma yayin da yake bayyana rashin jin dadinsa dangane da raguwar alaka ta kasuwanci tsakanin kasashen biyu, Jagoran ya ce: Akwai wasu da suke aiki ba dare ba rana ta hanyoyi daban-daban da suka hada haifar da yanayin rashin tsaro a kan iyakokin kasashen biyu don haifar da sabani da sanya tazara tsakanin al’ummomin kasashen Iran da Pakistan. To amma bai kamata a ba su damar lalata alakar da ke tsakanin wadannan kasashe biyun ba.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin kara fadada alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Pakistan cikin kuwa har da ayyuka na tattalin arziki da suka hada shirin shimfida bututuwa iskar gas da ake yi, Jagoran ya gaya wa firayi ministan na Pakistan cewa: Muna fata a lokacin mulkinka, za a sami kyautatuwar alaka tsakanin wadannan kasashe biyu a bangarori daban-daban.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan cewa bai kamata a jira izinin wani mutum na daban ba a fagen kyautata alaka, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Amurka dai wacce lalatarta ta bayyana ga kowa, tana daga cikin kasashen da suke kokari wajen haifar da sabani da tazara tsakanin Iran da Pakistan. Koda yake baya ga Amurkan, akwai wasu gwamnatocin ma na daban da suke gudanar da ayyukansu a wannan fagen.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu yanayi na rashin tsaro da ke faruwa cikin ‘yan watannin baya-bayan a kan iyakokin kasashen biyu inda ya ce: Wasu mutane da gangan suke kokari wajen haifar da rashin tsaro a kan iyakokin wadannan kasashe biyu mai tsawon gaske. Lalle ba za mu taba yarda da cewa abin da ke faruwar ba wani abu ne da aka shirya shi da gangan ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tabbas muna da wasu bayanai dangane da wasu tsare-tsare da ake gudanarwa a yankin Baluchestan na Pakistan da nufin haifar yanayin rashin tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kungiyoyi masu kafirta musulmi a matsayin babban hatsari ga dukkanin al’ummar musulmi Shi’ansu da Shi’ansu yana mai cewa: Matukar ba a yi fada da kungiyoyi masu kafirta musulmi ba, to kuwa za su haifar da gagarumar cutarwa ga duniyar musulmi.

Daga karshe dai Jagoran ya sake jaddada fatansa na ganin alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kara fadaduwa.

Shi ma a nasa bangaren, firayi ministan kasar ta Pakistan Nawaz Sharif wanda mataimakin shugaban kasar Iran na farko Malam Jihangiri yake wa jagoranci, ya bayyana tsananin farin cikinsa da wannan ganawa da ya yi da Jagoran juyin juya halin Musuluncin, inda yayin da yake ishara da ziyarar da Ayatullah Khamenein ya taba kai wa Pakistan da kuma garin Lahore ya bayyana cewar: A yayin wannan ziyarar na kasance ministan jihar Punjab da ke da helkwata a birnin Lahore, wanda irin gagarumar tarbar da jama’a suka yi alama ce da ke nuni da gagarumar alaka ta al’adu, addini da tarihi da ke tsakanin kasashen biyu.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan tattaunawar da yayi da jami’an Iran, firayi ministan Pakistan din ya ce: Lalle zan yi dukkanin abin da zan iya wajen karfafa alaka ta tattalin arziki da ke tsakanin kasashen biyu.

Firayi ministan na Pakistan ya bayyana irin yanayin rashin tsaron da ke faruwa a kan iyakokin kasashen biyu a matsayin wani lamari abin bakin ciki a kokarin da ake yi na raba kan al’ummomin kasashen biyu, don haka ya bayyana wa Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa: Ina sanar da kai cewa gwamnatin Pakistan ba za ta taba yin kasa a gwiwa wajen fada da masu haifar da wannan yanayin rashin tsaro ba, sannan kuma za ta goyi bayan matakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook