A+ R A-
28 February 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Halarci Bikin Yaye Daliban Jami'ar Soji Ta Imam Husain (a.s)

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da bikin ranar 3 ga watan Khordar don tunawa da zagayowar ranar da sojojin Iran suka kaddamar da hare-haren Baitul Mukaddis da kwato garin Khoramshahr daga sojojin Iraki a lokacin kallafaffen yaki, a safiyar yau Laraba (21-05-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarcin bikin yaye daliban jami'ar Imam Husain (a.s) ta jami'an dakarun kare juyin juya halin Musulunci.

Jagoran dai ya fara ziyarar tasa ce da ziyartar makabartar shahidan da ke jami'an inda ya karanta musu Fatiha da kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kara musu girman matsayi. Daga nan kuma sai ya wuce ta gaban dakarun sojin da suka fagen har zuwa inda aka tsara masa zai gabatar da jawabinsa.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin, Ayatullah Khamenei ya bayyana tarbiyyartar da matasa muminai masu riko da koyarwar juyin juya hali sannan kuma masana a wannan jami'a ta Imam Husain (a.s) a matsayin wani misali na tafarkin da juyin juya halin Musulunci ya rika. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin tsayin dakan da al'ummar Iran suka yi wajen tinkarar ma'abota girman kai da rashin amincewa da raba al'ummomin duniya zuwa ga ‘yan mulkin mallaka da wadanda suka amince a mulke su Jagoran cewa ya yi: A yau ma'abota girman kan duniya suna cikin matukar bakin ciki da fushi sakamakon irin ci gaban da al'ummar Iran da tsarin Musulunci na kasar suka samu ba tare da dogaro da Amurka da sauran masu tinkaho da karfi na kasashen yammaci ba, suna masu dogaro da irin karfi da kwarewar da suke da ita na cikin gida. Don haka ne muke sake jaddada musu wannan jumla ta Shahid Beheshti cewa: ku mutu da wannan fushi na ku.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan tafarkin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta rika a matsayin daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci da aka rika. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin damuwar da wasu suke yi a baya na yiyuwar fuskantar matsala koma baya, Jagoran cewa ya yi: Kamar yadda na fadi a wancan lokacin, a halin yanzu dai tafarkin juyin juya halin Musulunci ya tsallake matakin rugujewa. Matasa masu riko da juyin juya halin Musulunci a duk fadin kasar nan, su ne masu sanya fata mai kyau ga makomar kasar nan da kuma ci gabanta.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar Musulunci shi ne kawai hanyar tseratar da bil'adaman da aka zalunta da kuma cutarwa daga bala'oi daban-daban na zamani da kuma tabbatar masa da karama da mutumci na hakika, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Matasa ma'abota riko da juyin juya halin Musulunci su ne masu samar wa kasar nan da makoma mai kyau sannan kuma tushe na asali na samar da sabon ci gaba na Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan matsaloli da kalubalen da tsarin Musulunci na Iran yake fuskanta, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Samuwar kalubale ba ya sanya mutum ma'abocin basira da kuma jaruntaka da sanin inda aka dosa cikin damuwa, face dai hakan ya kan sanya shi komawa ga irin karfi da kwarewar da ake da su a cikin gida wadanda har ma da wadanda aka dakatar da su daga bakin aiki.

Jagoran ya ce babban dalilin irin wadannan kalubale shi ne irin ci gaba da kuma karfin da a kullum jamhuriyar Musulunci take samu ne, daga nan sai ya ce: Shekaru 35 kenan bayan nasarar juyin juya halin Musulunci al'ummar Iran suka tsaya kyam da kuma yin watsi da wannan bakar al'ada ta ‘yan mulkin mallaka ta raba duniya zuwa ga ‘yan mulkin mallaka da wadanda ake mulka, hakan ne kuwa ya sanya masu tinkaho da karfi na kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka suke tsananin fushi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Koda yake tabbas irin wannan tsayin dakan shi ne ya janyo zukatan al'ummomin duniya zuwa ga al'ummar Iran. Hatta ma da dama daga cikin gwamnatocin da ba su da jaruntakar tsayin daka a gaban wadannan masu tinkaho da karfi, suna farin ciki da irin wannan tsayin daka na Jamhuriyar Musulunci da kuma jinjinawa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce gabatar da batutuwa irin su batun nukiliya da take hakkokin bil'adama da sauran batutuwa na daban da masu tinkaho da karfi na duniya suke gabatarwa a kan al'ummar Iran wani abu ne kawai da suke son fakewa da shi don cimma manufofinsu a kan al'ummar Iran, inda ya ce: Kokarinsu shi ne ta hanyar wadannan abubuwa da matsin lambar, za su sanya al'ummar Iran janyewa daga wannan tsayin daka da suka yi. To amma hakan ba za ta taba faruwa ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Al'ummar Iran sun tabbatar da irin karfi da kwarewar da suke da ita a fagage daban-daban, sannan kuma sun tabbatar da cewa al'ummomi suna iya samun ci gaba a fagagen ilimi da zamantakewa da daukaka ta kasa da kasa da kuma ta siyasa ba tare da dogaro da Amurka ba.

Jagoran ya ce: Al'ummar Iran sun zabi hanyar da ta dace, sannan kuma za ta ci gaba da bin wannan tafarkin. Mafi yawan al'ummomin duniya suna tare da ita.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin da ma'abota girman kai suke yi wajen hana isar irin ci gaban da al'ummar Iran suke samu zuwa ga kunnuwar duniya, Jagoran ya ce: Duk da irin wadannan kokari, a halin yanzu wani adadi mai yawa na al'ummomin duniya suna dogaro da al'ummar Iran, sannan kuma suna jinjina musu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi watsi da batun da ake yi cewa kasashen duniya suna tinkarar kasar Iran, inda ya ce wannan lamari dai karya ce inda ya ce wasu ‘yan kasashe ne ma'abota girman kai da suke karkashin matsin lambar wasu kamfanoni da kungiyoyin sahyoniyawa suke fada da Iran din.

Shi ma a nasa bangaren babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran din Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari, a jawabin da ya gabatar ya yi karin haske kan irin karfi da ci gaban da dakarun kare juyin suke da shi inda ya ce samun ci gaba da kuka karfafa irin karfin mayar da martani a koda yaushe yana daga cikin ayyukan da dakarun kare juyin suka sa a gaba.

Haka nan shi ma shugaban jami'ar ta Imam Husain (a.s) ta jami'ar dakarun kare juyin juya halin Musuluncin Admiral Murtadha Safari ya gabatar da rahoto kan ayyukan da ake gudanarwa a jami'ar.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora

 

 

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook