A+ R A-
29 February 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Yi Allah Wadai Da Sace 'Yan Matan Chibok Da Boko Haram Suka Yi

A safiyar yau Talata (27-5-2014) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami'an gwamnatin Iran, al'ummomi daban-daban na Iran, baki mahalarta taron gasar karatun Alkur'ani mai girma na kasa da kasa da jakadun kasashen musulmi a Iran don tunawa da zagayowar ranar da aka aiko Ma'aikin Allah Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kyautata tunani, amfani da basira, fahimtar makiyan al'ummar musulmi na hakika da kuma hadin kai da nesantar rarrabuwan kai na akida da mazhaba a matsayin muhimman bukatun duniyar musulmi a wannan lokaci da muke ciki inda ya ce: A yau an daga tutar alfahari da Musulunci sama sannan kuma alfahari da riko da Musulunci a yau a tsakanin musulmi ya dara na shekarun da suka gabata. Haka nan kuma al'ummar Iran sakamakon imani da kuma dogaro da alkawarin da kuma taimako na Ubangiji sun kama hanyar ci gaba da kuma magance matsalolin da aka kirkiro musu daya bayan daya a tafarkin da suka rika na fada da zalunci, jahilci da rashin adalci.

Haka nan kuma yayin da yake isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar musulmi saboda zagayowar ranar da aka aiko Ma'aikin Allah (s.a.w.a), Jagoran ya ce mafi muhimmancin dalilin aiko Manzannin Allah musamman Manzon Musulunci (s.a.w.a) shi ne shiryar da mutane zuwa ga amfani da hankali da hikima. Daga nan sai ya ce: Matukar dai al'ummar musulmi suka yi amfani da karfi na tunani da hankalin da suke da shi, to kuwa za a magance da dama daga cikin matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan gurguwar fahimtar da wasu suka yi wa Musulunci da kuma Alkur'ani mai girma, Jagoran cewa ya yi: Rashin kyakkyawar fahimta ga koyarwar Musulunci da ma'anoni na Alkur'ani ne ya sanya a yau wasu da sunan Musulunci, suke zaluntar musulmi da yi musu kisan kiyashi ta yadda hatta a wata kasa ta Afirka aka samu wasu da sunan Musulunci suke satar ‘yan matan da ba su ci ba su sha ba.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wani misali na rashin amfani da hankali da tunani a irin wannan yanayi da duniyar musulmi ta ke ciki inda ya ce: A yau a fili makiya suke bayyanar da kiyayyarsu ga Musulunci, babbar hanyar da suke amfani da ita kuwa ita ce haifar da sabani na akida da kokarin haifar da yakin Shi'a da Sunna, wanda matukar aka yi amfani da hankali da hikima za a iya fahimtar wannan makirci da kiyayya ta makiya da kuma nesantar fadawa tarkon masu bakar aniya ga Musulunci.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hadin kai da kafa al'umma guda a matsayin wata bukata ta wajibi ta duniyar musulmi. Sannan kuma yayin da yake jaddada cewa daya daga cikin babbar manufar haifar da sabani tsakanin musulmi da yada akidar kiyayya da Shi'anci da kuma Iran ita ce rufe irin matsalolin da ma'abota girman kai suke fuskanta da kuma kiyaye haramtacciyar kasar Isra'ila inda daga nan sai ya ce: Fatan da ake da shi daga wajen al'ummar musulmi musamman masana da zababbun cikinsu shi ne amfani da tunani da basira wajen fahimtar makiyan al'ummar musulmi, sannan kuma a fahimci wannan lamari da kyaun gaske.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa cibiyoyin siyasa na kasashen yammaci su ne masu yada irin wannan yanayi na jahiliyya wanda manufar aiko Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ita ce kawar da su, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Rashin adalci, nuna wariya, yin karen tsaye ga karamar dan'adam, yada fasadi da tsiraicin mata, dukkanin wadannan wasu alamu ne na irin lalacewar kasashen yammaci, wanda a hakikanin gaskiya komawa ce ga zamanin jahiliyya sai dai kawai ta wani sabon salo.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da kokarin da ake yi wajen raunana irin farkawa ta Musulunci da aka samu a duniyar musulmi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Duk da cewa a zahiri sun yi nasara a wasu yankuna na duniyar musulmin, to amma hakikanin lamarin shi ne cewa farkawa ta Musulunci ba wani abu ne da za a iya kawo karshensa ba.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin ci gaban da al'ummar Iran suke ci gaba da samu karkashin riko da sakon Aiko Ma'aiki (s.a.w.a) da hadin kai na cikin gida da suke da shi bugu da karin kan jaruntakar tinkarar makiya da riko da alkawarin Ubangiji na taimako inda ya ce: A yau cikin rahamar Ubangiji an kafa sabuwar gwamnati a Iran da sabbin jami'ai, sannan ta hanyar alfahari da Musulunci suna ci gaba da ayyukansu a fagage daban-daban

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar fuskantar matsaloli da kalubale wani abu ne da dan'adam ya saba da shi a kan tafarkin da yake tafiya, don haka sai ya ce: Mutane masu hikima da tunani su kan yi hakuri da matsalolin da suka bijiro musu don isa ga daukaka da kuma samun kusaci da Ubangiji. To amma mutane marasa tunani da hikima maimaikon mika kai ga Ubangiji, sai suka riki tafarkin Shaidanu da kuma kankantar da kansu a gabansu.

A kan hakan Ayatullah Khamenei ya yi ishara da koyarwar Alkur'ani mai girma kan hakan inda ya ce: kamar yadda ayoyin Alkur'ani suka nuna, mutanen da maimakon su yi riko da tafarkin Ubangiji wajen isa ga daukakar da suke bukata, amma suka koma ga kaskantar da kansu a gaban makiyan Musulunci da kuma bil'adama da kuma riko da iko na Shaidanu, lalle daga karshe dai ba za su sami wannan daukakar ba sannan kuma su kansu wadannan Shaidanun ba za su gode musu ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a dau darasi daga wannan koyarwa da misali na Alkur'ani sannan kuma a yi riko da ingantacciyar hanya ta samar da sa'ada ta hakika cikin wannan koyarwa ta Alkur'ani.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce sirrin nasarorin da tsarin Musulunci na Iran ya samu a fagage daban-daban na gwagwarmaya ta tattalin arziki, siyasa, zamantakewa da kasa da kasa shi ne yarda da kuma imani da gaskiyar alkawarin Allah yana mai cewa: Wannan dai shi ne tafarkin da al'ummar Iran ta rika, sannan a nan gaba ma haka lamarin zai kasance.

Daga karshe Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Rahamar Allah ta tabbata ga Imaminmu mai girma (Imam Khumaini) wanda shi ne ya nuna mana wannan hanyar. Rahamar Allah ta tabbata ga shahidan da suka sadaukar da rayukansu a bisa wannan tafarkin. Rahamar Allah ta tabbata ga al'ummar Iran wadanda suka tabbatar wa da duniya irin shirin da suke da shi na riko da wannan tafarkin. Haka nan kuma rahamar Allah ta tabbata ga jami'anmu wadanda suka bayyanar da shirin da suke da shi na riko da wannan tafarki da kuma kokari wajen ciyar da shi gaba.

Kafin jawabin Jagoran sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal musulmin Sheikh Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake taya al'ummar musulmi murnar wannan rana ta aiko Ma'aiki (s.a.w.a) inda ya ce: Annabi (s.a.w.a) ya samu nasarar janyo hankulan mutane zuwa gare shi ne ta hanyar nuna tausayawa da kyawawan halaye.

Sheikh Hasan Ruhani ya bayyana rarrabuwan kai, rashin adalci, amfani da karfi da tsaurin ra'ayi a matsayin wasu munanan halayen da ma'abota kafircin duniya suka cusa wa duniyar musulmi inda ya ce: A halin yanzu juyin juya halin Musulunci ya kasance mai kira zuwa ga hadin kai da yin watsi da sabanin da ke tsakanin al'ummar musulmi wajen tinkarar sansanin kafircin duniya.

 

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook