A+ R A-
29 February 2020

Jagora Yayin Ganawa Da Sarkin Kuwait: Kungiyoyi Masu Kafirta Musulmi, Hatsari Ne Ga Kasashen Musulmi

A safiyar yau Litinin (02-06-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da sarkin kasar Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jabir al-Sabah da ‘yan tawagarsa da suka kawo masa ziyarar ban girma. A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yankin Tekun Fasha da kuma tsaron yankin a matsayin lamari mai matukar muhimmanci inda ya ce: Tabbatar da tsaron wannan yankin, wani lamari ne da zai amfani dukkanin kasashen yankin.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A saboda haka ne a koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran take kokarin ganin an sami ingantacciyar alaka tsakaninta da makwabtanta na kasashen Tekun Fasha, a halin yanzu ma wannan siyasar ce take gudanarwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Kusatar kasashen wannan yankin da junansu da kuma kyautatuwar alaka a tsakaninsu lamari ne da zai amfani kowa. Amma idan har ba a kiyaye hakan ba, to kuwa sabani da nesantar juna a tsakanin kasashen yankin, lamari da zai faranta ran makiyan dukkanin kasashen.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar rashin kyakkyawar alaka tsakanin kasashen yankin nan shi ne dalilin da ya sanya haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da aiwatar da siyasarsa ta mamaya a yankin yana mai cewa: A koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai maraba da kasashen wannan yankin.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kyautatuwar alaka tsakanin kasashen Kuwait da kasar Iraki a matsayin lamarin da zai amfani kasashen yankin gaba daya inda ya ce: Dangane da kasar Siriya kuwa, Jamhuriyar Musulunci za ta yi maraba da duk wata matsaya da al'ummar Siriya suka dauka dangane da makomar kasarsu.

Yayin da kuma yake ishara da hatsarin kungiyoyi tafkiriya masu kafirta Musulunci ga dukkanin kasashen gabas ta tsakiya kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu daga cikin kasashen yankin nan ba su fahimci irin hatsarin da kungiyoyi masu kafirta musulmi suke da shi ga makomarsu ba, don haka har ya zuwa yanzu suke ci gaba da goya musu baya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Har ya zuwa yanzu wasu kasashen yankin nan suna ci gaba da ba wa wadannan kungiyoyi masu kafirta musulmi taimako, suna ci gaba da goya musu baya wajen kashe mutanen Siriya da sauran kasashe. To amma nan ba da jimawa ba, ‘yan wadannan kungiyoyi za su koma kan al'ummomin wadannan kasashen da suke goya musu bayan.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa kasar Kuwait din dangane da matakan da take dauka cikin lamurran da suka shafi yankin Gabas ta tsakiya wanda sun yi kama da irin matsayar da Iran take dauka.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da alaka ta kasuwanci da tattalin arziki da ke tsakanin Iran da Kuwait, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi akwai fagage da dama da kasashen biyu za su iya kyautatta alaka ta kasuwanci da ke tsakanisu.

Shi ma a nasa bangaren, sarkin na Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Jabir al-Sabah, wanda shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ke wa jagoranci, yayin da yake taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Husain (a.s), ya bayyana Jagoran juyin juya halin Musuluncin a matsayin jagora kuma mai shiryarwa ga dukkanin kasashen yankin daga nan sai ya ce: Kasar Kuwaiti a shirye take ta bude wani sabon shafi na kyautata alaka tsakaninta da Iran. A tattaunawar da muka yi an cimma yarjejeniyoyi masu kyau da nufin kyautata alaka ta kasuwanci da tattalin arziki.

Haka nan kuma yayin da ya ke jaddada maganar da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi na wajibcin hadin kai da aiki tare tsakanin kasashen musulmin yankin, fada da tsaurin ra'ayi, rikicin Siriya da kuma alaka tsakanin Kuwaiti da Iraki, sarkin na Kuwait yayi fatan cewa za a magance matsalar kasar Siriya cikin ruwan sanyi kamar yadda kuma al'ummar kasar suke fatan gani.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora

 

 

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook