A+ R A-
28 February 2020

Jagora A Taron Tunawa Da Imam (r.a): Masu Goyon Bayan Masu Kafirta Musulmi Su Ne Makiyanmu Na Asali

A safiyar yau Laraba (04-06-2014) ce masoya marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya assasa juyin juya halin Musulunci na Iran, da suka fito daga duk fadin kasar Iran da sauran bangarori na duniya suka taru a hubbaren marigayi Imam don sake jaddada mubaya'arsu a gare shi da kuma tafarkin da ya bari.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan taro na tunawa da shekaru 25 da rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a), Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi karin haske dangane da tushe da kuma dalilin da ya sanya al'mmomi suke ci gaba da shaukin sanin dalilin irin nasarori da ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu a kullum, yana mai bayyana ‘shari'ar Musulunci' da ‘tsarin demokradiyya da ya ginu bisa koyarwar shari'a ta Musulunci a matsayin tushe guda biyu na asali na tafarkin marigayi Imam Khumaini daga nan sai ya ce: Makirce-makircen da Amurka ta ke kulla wa Iran da kuma raguwar tasirin wannan yunkuri na marigayi Imam, su ne manyan kalubale guda biyu wadanda idan har al'ummar Iran ta fahimce su da kuma yin galaba a kansu, to kuwa za su iya ci gaba da bin wannan tafarki na marigay Imam Khumaini da ke cike da abubuwan alfahari da kuma sa'ada.

A bangaren farko na jawabin nasa a wajen wannan gagarumin taron, Ayatullah Khamenei ya bayyana ina matsayin da Imam Khumaini da Jamhuriyar Musulunci su ke ci gaba da samu a zukatan al'ummomin duniya musamman al'ummar musulmi a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske yana mai cewa: Shekaru 25 da rasuwar babban jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, amma har yanzu al'ummomi daban daban musamman matasa da masanan duniyar musulmi cikin shauki suke neman masaniya kan tsarin demokradiyya na addini, nazariyar Wilayatul Fakih da sauran batutuwa da suka shafi juyin juya halin Musulunci.

Jagoran ya bayyana irin hare-hare da cutarwa mai girman gasket a siyasa da farfaganda da makiya suke yi a kan Jamhuriyar Musulunci a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka kara wa al'ummomin duniya neman karin masaniya kan juyin juya halin Musulunci inda ya ce: A halin yanzu zukatan al'ummomin duniyar musulmi, sama da shekarun baya, suna shaukin sanin hakikanin irin wannan hukuma da ake yada irin wadannan farfaganda da cutarwa maras tamka a kanta da kuma sanin sirrin irin wannan tsayin daka da kuma nasarorin da take samu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana farkawa ta Musulunci da irin kyamar ma'abota girman kai da ake yi (a duniyar musulmi) a matsayin daya daga cikin sakamakon irin wannan neman sani da fahimtar juyin juya halin Musulunci da al'ummomi suka yi daga nan sai ya ci gaba da cewa: Ma'abota girman kai cikin kuskuren suna tunanin sun kawo karshen farkawa ta Musulunci da aka samu (a kasashen musulmi), to amma irin fahimtar da ta haifar da irin wannan farkawa ta Musulunci, ba abu ne da za a iya kawar da shi ba. Ko ba dade ko ba jima zai bayyana da sake fadada.

Jagoran ya bayyana tsayin daka da ci gaban da al'ummar Iran take ci gaba da samu a kowace rana a matsayin wani dalilin da na ya sanya al'ummomi neman karin bayani kan Jamhuriyar Musulunci da tsarin demokradiyya na addini inda ya ce: Matasan duniyan musulmi suna neman amsar wannan tambaya mai muhimmancin gaske na cewa me ya ya aka yi Jamhuriyar Musulunci ta yi tsayin daka na shekaru 35 a gaban irin wadannan makirce-makirce da kiyayya da hare-hare na soji, siyasa da farfaganda ta makiya ga kuma takunkumi maras tamka na Amurka, amma kuma a kowace rana sai kara ci gaba da karfi ta ke yi?

Yayin da yake karin haske dangane da irin wannan yanayi na kauna da al'ummomi suke nuna wa Jamhuriyar Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Al'ummomi da matasa da masanan duniyar musulmi suna ganin irin ci gaban da al'ummar Iran suka samu a fagen ilmin sararin samaniya, kasantuwar Iran cikin kasashe 10 da suka ci gaba a fagen ilimi, irin ci gaba cikin gaggawa da Iran ta samu ninkin ba ninkiya har sau 13 idan aka kwatanta da ci gaban ilimi na duniya, haka nan kuma suna fahimtar cewa Iran ita ce babbar mai fadi a ji a fagen siyasar yankin nan, sannan kuma ta hanyar tinkarar haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa, tana ci gaba da goyon bayan wanda aka zalunta da kuma fada da azzalumi.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wadannan abubuwa sukan janyo hankulan duk wani mutum mai neman sani sosai kan Jamhuriyar Musulunci.

Har ila yau Jagoran ya bayyana gudanar da zabubbuka 32 cikin shekaru 35 da suka gabata a Iran shi din ma da irin wannan fitowar al'umma haka nan da kuma irin fitowar da mutane suke yi kwansu da kwarkwatansu a lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman da Ranar Kudus a matsayin wani abu na daban da ke jan hankulan mutanen duniya zuwa ga Iran, inda ya ce: Lalle mu mun saba da irin wadannan abubuwan, ba ma ganin girma da daukakarsu. Amma wadannan hakika masu kyaun gaske wasu abubuwa masu ban mamaki da bukatar bayani a wajen masu sanya ido na duniya da sauran al'ummomin kasashen duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa dukkanin wadannan abubuwa masu janyo hankula an samar da su ne albarkacin karfi da tunani na marigayi Imam Khumaini (r.a), don haka ne ma ya ci gaba da karin haske kan tafarki da kuma koyarwar marigayi Imam din.

Batun da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fi ba shi muhimmanci a wannan bangare na jawabin na sa shi ne bayanin cewa matukar ana son isa ga wata manufa to wajibi ne a yi taka tsantsan kada a bace daga kan hanya sannan kuma akwai bukatar a fahimci tafarkin wannan masani (Imam Khumani) wanda ya tsara wannan tafarkin matukar ana son riko da tafarkin nasa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana gina wani tsari na siyasa karkashin koyarwar Musulunci a matsayin babban tushe na asali na tafarkin Imam daga nan sai ya ce: Rugujewar lalatacciyar gwamnati ta kama karya ta gidan sarauta (Shah) da kuma tumbuke irin siffofin da ta ginu a kai wani share fage ne na samar da gagarumin ginin da Imam ya samar albarkacin irin himma da tsayin dakarsa da kuma goyon bayan mutane.

Haka nan yayin da yake karin haske kan tushe na asali na wannan tsari na siyasa irin wanda Imam ya kafa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara ne da wasu batutuwa guda biyu na asali wadanda kuma suke da alaka da junansu inda daga nan sai ya ce: Na farko shi ne shari'ar Musulunci a matsayin ruhi kana kuma tushen Jamhuriyar Musulunci sannan na biyu mika lamurra ga hannun mutane ta hanyar zabe da aiwatar da tsarin demokradiyya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kada wani ya yi zaton cewa Imam ya zabi zabe ne daga al'adun kasashen yammaci sannan ya hada shi da koyarwar Musulunci. Ko shakka babu idan da a ce zabe da tsarin demokradiyya ba ya cikin shari'ar Musulunci, da kuwa ya yi mana bayanin hakan ba tare da wani noke-noke ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Bisa koyarwar Imam Khumaini, wajibi ne shari'ar Musulunci a matsayin wata hakika sannan kuma tushen tsarin Musulunci, ta kasance cikin dukkanin ayyuka dokoki, tsarin siyasa, nadi da saukewa, halaye na zamantakewar mutane da sauran batutuwa. Haka nan kuma gudanar da ayyuka cikin wannan tsari na siyasa da zamantakewa karkashin wannan tsari na demokradiyya da ya samo asali daga shari'ar Musuluncin. Mutane kai tsaye ko ta wata hanya su ne suke zaban jami'an gwamnati.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar aiwatar da shari'a gaba daya shi ne abin da zai samar da abubuwa guda hudu na asali, su ne kuwa: ‘yancin kai, ‘yanci, adalci da kuma kyawawan halaye masu kyautata zukata. Daga nan sai ya ce: Riko da shari'ar Musulunci, baya ga samar da ‘yanci na daidaiku da na zamantakewa, haka nan kuma yana ‘yantar da al'ummomi daga kangin ma'abota girman kai, wato yana tabbatar da ‘yanci na kasa, haka nan yana tabbatar da adalci tare da kyawawan halaye masu kusata mutum zuwa ga Ubangiji.

Daga nan sai Ayatullah Khamenei ya yi bayani wani tushe mai muhimmanci na daban na tafarkin Imam yana mai cewa: A tafarkin Imam ba a yarda da duk wani iko da galaba da aka same su ta hanyar amfani da karfi da tursasawa ba, face dai karfi da ikon da aka same shi ta hanyar zabe na mutane. Babu wani da ya ke da hakkin yin karen tsaye ga hakan, idan kuwa ya yi hakan, to ya haifar da fitina.

Ayatullah Khamenei ya ce salon siyasa da zamantakewa da Imam ya zo da shi wani sabon salo ne cikin siyasar duniya, don haka ne ya yi karin haske kan wani bangare na wannan salon yana mai cewa: Taimakon wanda aka zalunta da kuma fada da azzalumi wani tushe ne na tafarkin Imam.

Don haka ne ma Ayatullah Khamenei ya yi ishara da goyon baya dari bisa dari ba tare da jin tsoro ba da Imam Khumaini ya ke yi wa al'ummar Palastinu da ake zalunta, inda ya ce: Tsayin daka a gaban a gaban azzalumi da ruguza kashin bayan zaluncinsu tushe ne na asali na koyarwar Imam, wanda wajibi ne al'umma da jami'an gwamnati su lura da hakan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yiyuwar aiwatar da salo na siyasa da zamantakewa da Imam ya zo da shi a aikace a matsayin daya daga cikin fitattun bambancin da ke tsakanin wannan tafarki na Imam da sauran salo na tsari na siyasa, don haka ne sai ya gabatar da tambayar cewa: Shin ana iya cewa wannan aiki da Imam ya aiwatar da shi, abu ne da za a iya ci gaba da riko da shi?

Ayatullah Khamenei ya ce lalle za a iya ci gaba da riko da shi din amma da wasu sharudda.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A dabi'ance ana iya samun wasu wajajen da ake bukatar cike su cikin wannan aiki da Imam ya yi, wanda kuma yin hakan wani lamari ne mai yiyuwa, amma da sharadin ba da himma da fahimtar mutane da kiyaye dokokin wannan tafarkin.

Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa irin sadaukarwar da al'ummar Iran suka yi wajen riko da manufofi da koyawar marigayi Imam Khumaini, Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Halayen da al'ummar Iran suka nuna tsawon wadannan shekaru 25 da rasuwar Imam mai girma, hakan yana nuni da cewa ana iya cike dukkanin gibin da ake da su, sannan kuma bisa riko da wannan tafarkin, cikin yarda da taimakon Ubangiji za ta kai ga kololuwar karfinta.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ja hankulan mahalarta taron da sauran al'ummomi zuwa ga wani batu mai muhimmanci, shi ne kuwa: Riko da tafarkin Imam Khumaini da cimma manufofinsa, tamkar sauran manufofi na daban, yana da kalubale da abubuwan da suke kokarin kawo masa cikas, wadanda matukar ba mu fahimce su da kuma kawar da su ba, to kuwa ci gaba da bin wannan tafarkin zai zamanto da wahalar gaske ko kuma ma ba zai yiyu ba.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da wasu kalubale guda biyu na ‘ciki' da ‘waje' a matsayin manyan kalubalen da ake fuskanta, yana mai cewa wajibi ne matasa da masana su yi la'akari da kuma ba su muhimmanci.

Yayin da yake magana kan kalubale na wajen, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin kafar ungulun da ma'abota girman kan duniya musamman Amurka suke yi inda ya ce: Wasu daga cikin masanan siyasa na kasashen yammaci suna fadin cewa: wadannan kafar ungulun dai aikin baban giwa ne, to amma duk da haka Amurka tana ci gaba da gudanar da wannan siyasa nata.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa sun kasa kasashe da kungiyoyi na siyasa da jami'an kasashen duniya zuwa gida uku su ne kuwa ‘kasashe ‘yan amshin shata' sai kuma ‘gwamnatoci da kungiyoyin da a halin yanzu suka rufe ido kansu' da kuma ‘gwamnatoci da kungiyoyin ‘yan tawaye da kin binsu'. Jagoran ya ci gaba da cewa: Salon mu'amalar da Amurka ta ke yi da irin wadannan gwamnatoci ‘yan amshin shatansu shi ne basu goyon baya da kuma halalta munanan ayyukan da suke yi a cibiyoyin kasa da kasa. Koda yake, suna kare manufofinsu ne ta hanyar irin wannan goyon bayan.

Jagoran ya yi ishara da wasu gwamnatocin da suka ci baya ‘yan mulkin kama-karya da suke samun goyon bayan Amurkan inda ya ce: Amurkawa suna bayyana irin wadannan kasashen wadanda ba a taba gudanar da zabe a cikinsu ba haka nan kuma al'ummominsu ba su da bakin fadin albarkacin bakinsu a matsayin kasashe masu bin tafarkin iyaye amma ba wai ‘yan mulkin kama karya ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kasashe na biyu cikin wannan kashi da Amurkawa suka yi a matsayin kasashen da Amurkan take rufe ido kansu saboda tarayyar da suka yi cikin manufofinsu, duk kuwa da cewa idan har suka sami dama to su kan yi musu bugun mummuke.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kasashen Turai a matsayin misalin irin wadannan kasashen inda ya ce: A daidai lokacin da Amurka take rufe ido kan kasashen Turai saboda tarayyar manufofi da suka yi, amma a bangare guda kuma tana ci gaba da leken asirin jami'an da ‘yan wadannan kasashen. Hatta kuma ba a shirye suke su nemi afuwarsu ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas kasshen Turai sun tafka gagarumin kuskure saboda biyan bukatun Amurka, ba tare da la'akari da manufofi da amfanin kasashensu ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kasashe na uku cikin wannan kaso na Amurkan a matsayin da suka ki mika kai ga bukatun Amurkan yana mai cewa: Siyasar Amurka a kan wadannan kasashen shi ne amfani da dukkanin karfin da suke da shi wajen cutar da su.

Haka nan kuma yayin da yake karin haske dangane da yadda Amurka take fada da kasashen da suka ki mika mata wuya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Koda yake sakamakon irin hasara da kashin da Amurka ta sha saboda harin da ta kai Iraki da Afghanistan, a halin yanzu dai harin soji ba ya daga cikin tsare-tsare na gaba-gaba na Amurka.

Jagoran ya bayyana amfani da wasu ‘yan amshin shatan na cikin gida na kasashen da suka mika wuya ga Amurka a matsayin wani salo mai muhimmanci da Amurka take bi wajen cutar da su yana mai cewa: Kokarin yin juyin mulki na soji ko kuma sanya mutane su yi bore su ne mafi muhimmancin ayyukan da Amurka take sanya ‘yan amshin shatanta na cikin gida aiwatarwa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Amurka tana amfani da ‘yan tsirarrun da suka kaye a zaben da aka gudanar a kowace kasar (da suke adawa da ita) wajen tunzura wadannan ‘yan tsirarun su yi bore wa wannan gwamnati da ta dare karagar mulki ta hanyar zabe.

Jagoran ya ce: A fili ana iya ganin misalin hakan a yau a wani bangare na kasashen Turai, koda yake mu dai ba za mu yi hukumci kan hakan ba. To amma me sanatan Amurka yake yi a cikin masu zanga-zangar da suka fito kan tituna?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana karfafa kungiyoyin ‘yan ta'adda a matsayin wata hanyar da Amurka take bi wajen fada da kasashen da ba a shirye suke su mika wuya ga Amurka ba. Jagoran ya ci gaba da cewa: Iraki, Afghanistan da wasu daga cikin kasashen larabawa da wannan kasa ta mu ta Iran sun kasance wadanda suka cutu daga wannan salo na Amurka.

Yayin da yake ishara da irin goyon bayan da Amurka take ba wa kungiyoyin ‘yan ta'adda na munafukai da kuma irin alakar da ‘yan wadannan kungiya suke da ita da cibiyoyi masu gudanar da Amurka ciki kuwa har da majalisar kasar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Munafukai wadanda suka kashe wani adadi mai yawa na masana da ‘yan siyasa da mutanen kasar Iran, suna karkashin kulawa da goyon bayan Amurka ne.

Wata hanyar kuma da Amurka take bi wajen fada da wadanda suka ki mika mata wuya da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ita, ita ce haifar da sabani cikin jami'ai da al'ummomin irin wadannan kasashen da kuma kokarin lalata tunani da akidar mutane inda ya ce: Cikin taimakon Allah Amurkawa a dukkanin fagage sun kashi a gaban al'ummar Iran, sannan kuma dukkanin wadannan makirce-makirce na su da suka hada da kokarin juyin mulkin soji, goyon bayan masu fitina, kokarin tunzura wasu mutane su fito kan titi da kuma haifar da rikici tsakanin jami'ai sun zaman aikin baban giwa sakamakon imani da kuma farkawar al'ummar Iran.

Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya koma kan kalubale na cikin gida inda ya ce: Wannan kalubale mai girma da kuma hatsarin gaske zai yi nasara ne a lokacin da al'umma da kuma jami'an gwamnati suka yi watsi da mahangar yunkurin marigayi Imam Khumaini da kuma mantawa da ita.

A saboda haka ne Jagoran ya yi ishara da matsalar yin kuskure wajen fahimtar aboki da makiyi da kuma gazawa wajen fahimtar makiyi na asali da kuma na bayan fage inda ya ce: Wajibi a yayin faruwar abubuwa daban-daban ya zamana ba a gafala da makiyi na asali ba.

A ci gaba da bayanin wannan lamari, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu halaye abin kyama da wasu kungiyoyi na jahilai masu kafirta musulmi, masu riko da akidar wahabiyanci da salafiyanci suke yi wajen fada da akidar Shi'anci inda ya ce: wajibi ne kowa ya fahimci cewa makiya na asali su ne kungiyoyin leken asiri na kasashen waje da sauran mutanen da suke juya wadannan kungiyoyi da ba su kudade da makamai.

Jagoran ya ce: Tabbas duk wani mutumin da yake tunanin wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ko shakka babu zai fuskanci gagarumin bugu daga wajen al'umma, to amma duk da haka mun yi amanna da cewa wadanda suke tunzura wasu musulmi ta bayan fage wajen fada wani bangare na musulmin su ne asalin makiyanmu, ba wai wadannan kungiyoyi da aka yaudara ba.

Daga karshe dai Jagoran ya ce ambaton sunan marigayi Imam Khumaini da kuma riko da abin da ya bari ko shakka babu zai taimaki al'ummar Iran wajen cimma manufofin da ta sa a gaba da kuma sanya mata fata zuwa ga kyakkyawar makoma.

Mun Sami Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei

 

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook