A+ R A-
13 July 2020

Jagora Imam Khamenei: Gwagwarmaya Ta Makami, Ita ce Hanya Guda Ta Fada Da ‘Israila'

A yammacin yau Laraba (23-07-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da kimanin dalibai dubu na jami'oi da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi na Iran na tsawo sa'oi biyu da rabi inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi Iran, yankin Gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya bugu da kari kan batutuwan da suka shafi karatun jami'an.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa bayan da ya saurari jawaban wakilan daliban jami'oin na tsawon mintuna 90, Ayatullah Khamenei ya jinjinawa irin ruhin ‘dake cike da nishadi, tunani, bayyana ra'ayi da kuma jin nauyin da ke wuya' da ke tattare da daliban jami'oin, daga nan kuma sai yayi karin haske kan dangane da tushe da kuma dalilan hare-haren wuce gona da iri da sahyoniyawa suke kai wa al'ummar Zirin Gaza yana mai cewa: Wannan danyen aikin da ya saba wa hankali, shi ne hakikanin wannan gwamnati mai siffar Kerkeci da kashe kananan yara wanda maganin hakan shi ne kawai kawar da ita. Koda yake tabbas kafin hakan, hanya guda kawai ta fada da wannan gwamnati maras tausayi ita ce gwagwarmaya ta makami da fadada hakan har zuwa yankin yammacin Kogin Jordan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a dauki irin goyon baya da kariyar da Amurka da kasashen yammaci suke ba wa wadannan danyen aikin sahyoniyawan a matsayin wani lamari mai muhimmanci cikin ‘fahimta, mahanga da kuma irin mu'amalar' da dukkaninmu za mu yi da kasashen yammacin. Sannan kuma mu fahimci cewa wannan shi ne hakikanin Amurka. Al'ummar Iran kuwa a Ranar Kudus, ta hanyar fitowar da za su yi, za su nuna wa duniya cewa su din nan masu goyon wanda aka zalunta ne da kuma kiyayya da azzalumi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin mummunan yanayin da mutanen Gaza suke ciki, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Hakan lamari ne da ke nuni da ‘siyasar amfani da karfi da zalunci' da wannan haramtacciyar gwamnati take aiwatarwa tsawon shekaru 66 na kasantuwarta, sannan kuma a lokuta da dama ma tana alfahari da hakan ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda marigayi Imam Khumaini ya ke fadi ne cewa wajibi ne a kawar da Isra'ila daga doron kasa, tabbas kawar da Isra'ila a matsayin hanya guda ta magance wannan matsalar ba tana nufin kawar da yahudawan da suke wannan yankin ba ne. Face dai akwai hanyar da za a bi wajen tabbatar da wannan aiki da ya yi daidai da hankali, wanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da ita ga cibiyoyin kasa da kasa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wannan hanya kuwa wacce al'ummomin suka amince da ita, ita ce cewa a gudanar da kuri'ar jin ra'ayi tsakanin asalin mutanen wannan yankin (Palastinu) kan gwamnatin da suke so. Ta wannan hanyar za a kawar da wannan haramtacciyar gwamnatin.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas har zuwa lokacin da insha Allahu bisa taimakon Ubangiji za a kawar da wannan haramtacciyar gwamnati mai shan jinin mutane, gwagwarmaya ta makami ita ce kawai hanyar guda ta fada da wannan azzalumar gwamnati.

Jagoran ya kara da cewa: bai kamata wani ya yi tunanin cewa idan da ba don makamai masu linzamin da suke Gaza ba, da kuwa gwamnatin sahyoniyawa ba ta kai musu hari ba. Ko da wasa don kuwa ai babu irin wadannan makamai da bindigogi a Yammacin Kogin Jordan, duwatsu su ne makaman mutane, amma tana ci gaba da kashe mutanen wajen da kuma wulakanta su.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wulakancin da sahyoniyawan suke yi wa Yassar Arafat (tsohon shugaban Palastinawa) da kuma kashe shi da suka yi ta hanyar amfani da guba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Su dai wadannan ‘yan share guri zaunan hatta masu neman sulhu da su ba sa raga musu. Don haka gwagwarmaya da tsayin dakan Palastinawa ne za ta iya sanya su sassautowa.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan kokarin haramtacciyar kasar Isra'ila na ganin an tsagaita wuta a yakin da ta kaddamar kan Gaza, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wannan gwamnati wacce ta ke aikata danyen aikin da ya saba wa tunanin bil'adama, sai ga shi ta zamanto kaskantacciya a gaban gwagwarmaya da tsayin dakan al'ummar Palastinu, tana neman hanyar tsira. Hakan kuwa lamari ne da ke tabbatar da cewa karfi shi ne kawai abin da zai iya maganin sahyoniyawan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Bisa la'akari da hakan, mu mun yi amanna da cewa wajibi ne ba karfafa Yammacin Kogin Jordan da makamai kamar yadda aka yi wa Gaza. Don haka kamata ya yi mutane da suke nuna damuwarsu ga makomar Palastinu su yunkura a wannan bangaren don tsamar da al'ummar Palastinu daga irin wannan mummunan yanayi da suke cid a kuma raunana sahyoniyawa abokan gaba.

Jagoran ya bayyana nuna goyon baya na siyasa ga mutanen Gaza a matsayin wani nauyi da ke wuyan dukkanin al'ummar musulmi da ma wadanda ba musulmi ba. Sannan kuma yayin da yake ishara da irin kyamar da al'ummomin duniya suke nuna wa gwamnatin ‘yan ta'adda ta Isra'ila cewa ya yi: Da yardar Allah, a Ranar Kudus, duniya za ta shaidi irin fitowar al'ummar Iran, sannan kuma al'ummar Iran za su nuna wa duniya cewa har ya zuwa yanzu wannan kumaji na nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu na nan daram dinsa.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan taken da wasu masu kokarin haifar da fitina a Iran suke rerawa a shekarun baya kan ba su yarda da goyon bayan da Iran ta ke ba wa Gaza ko Labanon ba, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wasu ‘yan tsiraru suna son nuna akasin yanayin al'ummar Iran ta hanyar rera wannan taken, to amma mutanen Iran ba su bar su sun cimma wannan manufar ba. A ranar Juma'a mai zuwa din nan ma za su sake tabbatar wa da duniya cewa su din nan a koda yaushe sun kasance masu taimakon wanda aka zalunta da kuma kiyayya da azzalumi ne.

Har ila yau kuma yayin da yake kakkausar suka ga irin goyon bayan da ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suke ba wa irin wannan danyen aiki na dabbacin da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa take yi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Ko shakka babu abin da ke faruwa a Gaza lamari ne mai sosa rai ainun. To amma abin da ke da muhimmanci shi ne cewa dubi da idon basira kan abin da ke faruwa a Gazan, zai tabbatar mana da yanayi da kuma dabi'ar ‘yan mulkin mallakan ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wasu gwamnatocin kasashen yammaci musamman Amurka da Ingila lalatacciya a fili suke goyon bayan wannan danyen aikin da babu wani mutumin da zai yarda da shi. Hatta ma shugaban Amurka, a gaban irin wannan kisan kiyashi na rashin imani da sahyoniyawan suke yi wa kananan yaran Gaza, cikin isgili yake fadin cewa Isra'ila tana da hakkin kare kanta da tsaronta. To amma shin su Palastinawa ba su da hakkin kare tsaron su da kuma rayuwarsu?

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Jami'an kasashen duniya ma'abota girman kai ba su fahimci cewa ta hanyar irin wannan goyon baya ido rufe da suke ba wa sahyoniyawa ‘yan ta'adda suna zubar da mutumcinsu da na al'ummarsu a gaban al'ummomin duniya ba ne. Ko shakka babu tarihi zai yi hukumci mai tsanani kan tarayyar da suka yi cikin wannan danyen aikin.

Haka nan kuma yayin da yake karin haske kan tushen irin wadannan ayyukan rashin mafadi na kasashen yammacin, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Goyon bayan aika-aikan sahyoniyawa (da kasashen yammacin suke yi) yana da tushe ne cikin tsarin demokradiyyar sassauci da suke bi, wanda ba shi da komai kashin tushe na kyawawan halaye da kuma tausayi a cikinsa.

Don haka ne daga karshe Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Wannan dai ita ce hakikanin Amurkan da take da matsala da Jamhuriyar Musulunci cikin batutuwa daban-daban. Wajibi ne mu fahimci Amurka da kyau cikin wannan lamarin da ke faruwa. Sannan kuma mu sanya hakan ya zamanto ma'aunin mu'amala da kuma mahangarmu kan Amurka.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin mu'amalar da ‘yan mulkin mallaka suke yi da irin wannan zaluncin da ake yi wa mutanen Gaza yana tabbatar mana da cewa babu ruwansu da wani batun bil'adama da hakkokin bil'adama. Dukkanin abin da suke fadi dangane da ‘yanci da hakkokin bil'adama isgili da wasa da hankalin mutane ne kawai.

Jagoran ya sake jaddada cewar: Ba ina fadin wadannan maganganu a matsayin nasiha ga jami'an Amurka ba ne, face dai ina fadin hakan ne saboda mu kanmu, don mu san nauyin da ke wuyanmu sannan kuma yayin hukumci da sharhin da za mu yi mu fahimci da wa muke magana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Irin taken nuna kiyayya ga Amurka da kasashen yammaci da ma'abota girman kai da ake ji a kasar Iran, yana nuni ne da irin fahimtar hakikanin Amurka da aka yi ne. To amma wasu cikin kuskure suna zaton cewa wadannan taken tsaurin ra'ayi ne da ya saba wa hankali. Wannan mahanga ta kyamar Amurka da kasashen yammaci a Iran wani lamari ne da ya yi daidai da hankali sannan kuma wanda ya ginu bisa ingantaccen lissafi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin da yayi a lokacin ganawarsa da manyan jami'an gwamnatin Iran a kwanakin baya, Jagoran cewa ya yi: Kamar yadda na fadi, babbar manufar makiya ita ce haifar da gibi cikin lissafi da mahangarmu. Don kuwa matukar aka samu gibi cikin lissafi da mahanga, to kuwa sakamakon da za a fitar zai zamanto bisa kuskure, kwarewar da ake da ita kuwa ba za ta yi amfani ba.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin kwarewar da al'ummar Iran suka samu tsawon shekarun da suka gabata daga irin mu'amala da dabi'un kasashen yammaci inda ya ce: Kafa mulkin kama-karya mai ban mamaki ta Ridha Khan, mamaye Iran a shekarun 1920, sace albarkatun man fetur din Iran, juyin mulkin ranar 28 ga watan Mordad, goyon baya ido rufe ga dan kama karya Muhammad Ridha, zagon kasa bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, goyon baya da taimako ido rufe ga Saddam da sauran makirce-makirce masu yawa, dukkanin wadannan wasu kwarewa ne da al'ummar Iran suka samu dangane da Amurka. Duk da cewa wasu masanan da suka rudu da kasashen yammaci wadanda kuma suka samu gibi cikin lissafi da tunaninsu sun gagara fahimtar wannan wadannan abubuwa masu sosa raid a kyau.

A bangaren farko na jawabin nasa, a yayin wannan ganawa da daliban jami'oi da cibiyoyin ilimi mai zurfi na Iran din, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan ganawar a matsayin ganawa mai kyaun gaske da ke nuni da ruhi na imani da shauki na aiki a tattare da matasa daliban jami'a na Iran din inda ya ce: Batutuwan da a yau wakilan kungiyoyin daliban jami'an suka yi bayaninsu, lamari ne da ke nuni da samuwar irin wannan ruhi na imani a tsakanin daliban jami'oin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne wasu batutuwan da aka gabatar din su zamanto ba su daidai da hankali ko kuma ba za a iya aiwatar da su ba ko kuma ba daidai ba ne. To amma abin da ke da muhimmanci, shi ne samun wannan ruhi da ke cike da nishadi da kumaji tsakanin daliban jami'an, wanda hakan abin faranta rai ne ainun.

Jagoran ya jaddada cewar: Wajibi ne dalibin jami'a ya zamanto me neman a biya masa bukatunsa, ya zamanto mai kumaji, ya zamanto a koda yaushe a fage da kuma sanya ido kan batutuwan da suka shafi kasar nan. Wanda cikin yardar Allah ana iya ganin irin wannan ruhi a tattare da daliban jami'oinmu a yau.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Tabbas wajibi ne ruhin neman biyan bukata da yin suka a tsakanin daliban jami'a ya zamanto tare da kiyaye iyakoki na kyawawan halaye, adalci da kuma shari'a da kuma nesantar fadin abubuwan da ba a da tabbas kansu.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya amsa tambayoyi daban-daban da daliban jami'an suka gabatar cikin jawaban na su da suka hada da lamurran da suka shafi siyasa, gudanar da jami'oi, tattalin arziki, batun auren matasa ‘yan jami'a da sauransu.

Dangane da batun auren kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda ake samun jinkirin aure a tsakanin dalibai ‘yan mata na jami'an inda ya ce: Wajibi ne matasan, iyalansu da kuma jami'an jami'oin su yi iyakacin kokarinsu wajen share fagen auratayya a tsakanin daliban jami'oin da kawo karshen karin shekarun aure a tsakaninsu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce wajibi ne daliban jami'an a matsayin su na masana da masu ruhin tunani su yi tunani kan hanyoyin da za a bi wajen magance wadannan matsaloli na aure da ake fuskanta.

Haka nan kuma yayin da yake amsa tambayar wani dalibin da yayi tambayar cewa shin dole ne mahangar mutane, daliban jami'a da kungiyoyin daliban jami'oin ta yi daidai da ra'ayi da mahangar Jagoran?, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Koda wasa, lalle wannan kuskure ne a ce wajibi ne wajibi ne ra'ayin mutane ciki kuwa har da daliban jami'a su yi daidai da na Jagora.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Dalibin jami'a a matsayinsa na mutum musulmi, mumini, ma'abocin tunani, wajibi ne ya zamanto mai mahanga, sannan kuma bisa wannan mahanga da sharhi nasa ne zai dau matsaya kan mutane, siyasar da ake gudanarwa, kungiyoyi da kuma ayyukan gwamnati.

Jagoran ya ce: Ingantaccen ma'aunin yin sharhin kuwa shi ne tsoron Allah, wato rashin shigar da son zuciya cikin nuna goyon baya ko adawa da wani abu.

Ayatullah Khamenei ya ce: Bai kamata a dauka ce wajibi ne kowa da kowa ya tsaya sai Jagora ya bayyana ra'ayinsa dangane da wani mutum ko wata siyasa, sannan kuma kowa sai ya yi riko da wannan mahangar ba. Jagoran ya ce irin wannan tunanin zai dakile ci gaban lamurra ne kawai.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Jagora dai yana da aiki da nauyin da ke wuyansa, kuma da yardar Allah zai sauke. To amma su ma daliban jami'a suna da na su nauyin wanda wajibi ne su sauke su suna masu la'akari da tsoron Allah da kuma la'akari da irin yanayin da ake ciki.

Jagoran ya kara da cewa: Tabbas idan har Jagora ya yi bayanin wani lamari, mai yiyuwa ne ya yi tasiri cikin mahangar wasu mutane da suke masa kyakkyawan zato, to amma hakan ba yana nufin watsi da mahanga da ra'ayin wasu ba ne.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wasu ‘yan nasihohi ga daliban jami'an.

Daga cikin nasihohin da Jagoran ya yi sun hada: karfafa bincike na addini da siyasa tare da karatun da dalibin jami'an yake yi wanda hakan zai kara masa irin karfi na sharhi da fahimta da yake da shi. Sai kuma kula da sanya ido kan irin maganganu da tunanin dake yawo a jami'oi.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da wasu daga cikin wakilan kungiyoyin daliban jami'an suka gabatar da jawabansu da suka shafi ba da muhimmanci ga lamurran da suka shafi ilimi da hanyoyin da ake koyar da su, sanya ido sosai kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, karin yunkuri na diplomasiyya cikin batutuwan da suka shafi yanki gabas ta tsakiya, nuna rashin amincewa da wasu ayyukan jami'an gwamnati musamman a fagen al'adu, kara ba da muhimmanci ga lamurran matasa, nuna ba sani ba sabo daga bangaren ma'aikatar shari'a a fadar da ake yi da rashawa da cin hanci da ta'annuti ga dukiyar kasa, kara hanyoyi kulla alaka tsakanin limaman juma'a da wakilan Jagora da matasa, fada da rayuwar almubazzaranci, kyautata rayuwa da halayen daliban jami'a da dai sauransu.

Mun Samo Wannan Labarin Ne Daga Shafin Jagora Imam Khamenei

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook