A+ R A-
13 July 2020

Jagora Imam Khamenei: Wajibi Ne Duniya Ta Taimakawa Palastinawa Da Makamai

A safiyar yau Talata (29-07-2014) ce aka gudanar da sallar idin karamar salla a duk fadin kasar Iran bayan wata guda na azumin watan Ramalana. A birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran din, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ya jagoranci sallar idin karamar sallar.

A lokacin da yake gabatar da hudubar farko ta sallar idin, Ayatullah Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar wannan rana mai albarka ta karamar salla yana mai bayyana irin tarurrukan karatun Alkur’ani, zikiri da shan ruwa da aka gudanar tsawon watan, haka nan kuma da ibadu da kaskantar da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki da aka yi a dararen Lailatul kadari sannan da kuma irin gagarumar fitowar da al’ummar Iran suka yi a Ranar Kudus ta duniya, a matsayin wani share fage na samun rahama da albarkoki na Ubangiji. Jagoran ya ci gaba da cewa: Wadannan lamurra masu kyaun gaske sun sanya al’ummar Iran hada irin daukakar da take cikin watan Ramalana da kuma wannan rana mai albarka tai din karamar salla.

Haka nan kuma yayin da yake kiran dukkanin al’umma zuwa ga kiyaye abubuwan da aka samu (na kusaci da Allah) cikin watan Ramalanan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake tunatar da mutane bukatar da ya gabatar a shekarar bara na nesantar almubazzaranci yayin bukukuwan shan ruwa da ake gudanarwa inda ya ce: Abin farin cikin shi ne cewa a wannan shekarar ana iya ganin yadda aka nesanci irin wannan yanayi ta hanyar gudanar da irin wadannan bukukuwa cikin sauki a kan tituna da wajajen taron al’umma da kuma na addini.

Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi mutane da cewa: Yana da kyau a karfafa irin wadannan abubuwa wadanda suke da tasiri cikin rayuwar mutane.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana Ranar Kudus ta wannan shekarar a matsayin lamarin da ke nuni da himmar al’ummar Iran, sannan kuma yayin da yake magana kan irin fitowar da al’ummar Iran kwansu da kwarkwatarsu da suka yi a wannan rana musamman ma iyaye matan da suka fito tare da jariransu yayin jerin gwanon ranar Kudus din, Jagoran cewa ya yi: A hakikanin gaskiya, Ranar Kudus ta wannan shekarar, rana ce mai girman gaske, sannan kuma al’ummarmu masu girma sun tabbatar wa duniya cewa suna nan raye sannan kuma daram kana bin da suka rika.

A hudubar sallar idin ta biyu kuwa, Ayatullah Khamenei ya ware dukkanin lokacin ga lamarin Gaza ne saboda muhimmnacin da yake da shi.

Jagoran ya bayyana abin da ke faruwa a Zirin Gazan a matsayin ‘babban lamarin da a halin yanzu ya shafi duniyar musulmi da ma duniyar bil’adama’. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin kisan gillan rashin imani da sahyoniyawa suke yi wa kananan yara da iyaye matan da ba su ci ba su sha ba a Gazan, Jagoran cewa a yayi: Wannan tsohuwar azzalumar kura mai suna gwamnatin sahyoniyawa tana ci gaba da kisan kiyashi a Gaza. A saboda haka wajibi ne bil’adama su tinkari da kuma yin fada da wannan danyen aiki na wannan kafirar gwamnati masha jini.

A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da wasu batutuwa guda uku masu muhimmanci dangane da lamarin Gaza. (1). Wajibcin yin Allah wadai da kuma hukumta sahyoniyawan da suke aikata wannan danyen aiki da kuma masu daure musu gindi. (2). Jinjinawa irin gwagwarmaya da tsayin daka maras tamka na al’ummar Gaza. (3) Wajibcin karfafa da kuma ba wa al’ummar Palastinu makaman kare kansu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin aika-aikan da shugabannin sahyoniyawa suke aikatawa a Gaza a matsayin wani kisan kiyashi sannan kuma wani babban aika-aika na tarihi inda ya ce: Wajibi ne a yi Allah wadai da kuma hukumta masu aikata wannan aika-aika da kuma ma’abota girman kan duniya masu goya musu baya. Shin wadannan masu laifin suna kan karagar mulki ne ko kuma bayan an sauke so. Wannan kuwa wani lamari ne da masu magana da yawun al’ummomi da masu nuna damuwarsu na duniya ya wajaba su bukaci a aiwatar da shi.

Batu na biyu mai muhimmanci da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi magana kansa shi ne irin hakuri, juriya da tsayin daka mai ban mamaki da al’ummar Gaza suka yi inda ya ce: Mutanen Gaza suna a wani yanki ne da aka killace shi ta kowace kusurwa, sannan kuma dukkanin abubuwan da suke da shi wadanda ba su taka kara sun karya ba suna fuskantar barazanar hare-haren wadannan lalatattu kuma najasa, marasa imanin sahyoniyawa, amma duk da haka, haka suka tsaya kyam cikin jaruntaka suna ci gaba da gwagwarmaya.

Ayatulllah Khamenei ya bayyana gwagwarmaya da tsayin dakan da mutanen Gaza da ake zalunta suka yi a matsayin wani babban darasi ga dukkanin al’ummomi inda ya ce: Wannan gwagwarmaya da ta dara yadda ake zato, lamari ne da ke nuni da irin karfin tsayin dakan wani mutum da kuma karfin gwagwarmayar wata al’umma ce. Sannan kuma cikin yardar Allah da izininsa, wannan al’umma za ta yi nasara a kan makiyanta.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin da haramtacciyar kasar Isra’ila da masu goya mata baya na daga Amurkawa da mutanen Turai suke yi wajen tilasta wa al’ummar Gaza tsagaita wuta, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: A halin yanzu da wadannan makiya masu wuce gona da irin, tamkar kare, suka gagara cimma abin da suke so, don haka suna neman a tsagaita wuta. Hakan kuwa wata alama ce ta nasara ga bangaren ‘yan gwagwarmaya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A saboda haka ne, masu goyon bayan sahyoniyawan suke ta kokari wajen ceto wannan gwamnatin ta hanyar tilasta wa mutanen Gazan tsagaita wuta.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan batu na ukun, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da maganganu da kokarin shugabannin gwamnatocin girman kan duniya irin shugaban Amurka na batun kwance damarar kungiyoyin Hamas da Jihadi Islami na Palastinu inda ya ce: Manufar kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar ita ce kwace ‘yan makaman da kungiyoyin gwagwarmaya suke amfani da su wajen kare al’ummar Palastinu. Don ba wa sahyoniyawa damar kai hari kan Palastinu a duk lokacin da suka ga dama ba tare da Palastinawan suka da damar kare kansu ba.

A karshen hudubar tasa, Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Sabanin tunani da ra’ayi da kuma kokarin masu goyon bayan wannan gwamnati mai kashe kananan yara ta sahyoniyawa, wajibi ne a kan dukkanin duniya ciki kuwa har da duniya musulmi da za su taimaka wajen karfafa Palastinawa da makamai.

Mun Samo Wannan Labarin Ne A Shafin Jagora Imam Khamenei

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook