A+ R A-
18 September 2020

Imam Khamenei Ya Gana Jami’an Iran Da Jakadun Kasashen Musulmi Ran Karamar Salla

A yau Talata (29-07-2014), wacce ta yi daidai da ranar idin karamar salla ta bana, ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan jami’ai da al’ummomin daban-daban na Iran, bugu da kari kan jakadu da ma’aikatan ofisoshin jakadancin kasashen musulmi da suke Iran inda ya kirayi dukkanin musulmi zuwa ga taimakon al’ummar Palastinu da ake zalunta. Jagoran ya bayyana cewar: Ta hanyar yin watsi da dukkanin sabani, wajibi ne kasashen musulmi su yi amfani da dukkanin karfin da suke da shi wajen sama wa al’ummar Gaza abubuwan da suke bukata. Sannan kuma wajibi ne su yi fada da wannan zalunci na sahyoniyawa ta hanyar yin Allah wadai da nuna kyamarsu ga masu goya wa sahyoniyawan baya musamman Amurka da Ingila.

Yayin da yake isar da sakon tayar murnarsa na karamar salla ga dukkanin al’ummar musulmi, Jagoran ya bayyana wannan idin a matsayin ranar idin wata al’umma tsintsiya madaurinki guda yana mai cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa sabanin koyarwar Musulunci, a halin yanzu manufa ta siyasa da neman mulki su rarraba kan al’ummar musulmi.

Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kirayi jami’an kasashen musulmin da su yi watsi da irin wadannan tunani da kuma kafa wata al’umma guda ma’abociyar hadin kai da kuma karfi. Jagoran ya ce: Idan har irin wannan neman mulki, dogaro da wasu da kuma lalata ba su iya tarwatsa al’ummar musulmi ba, to kuwa ma’abota girman kai ba za su sami jaruntakar wuce gona da iri kan kasashen musulmi ko kuma neman gwamnatocin kasashen musulmin su mika musu kai ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana aika-aikan da sahyoniyawa suke yi a Gaza a halin yanzu a matsayin sakamako na rarrabuwan kan da ake samu a kasashen musulmi ne, don haka sai ya ce: Irin takunkumin da gwamnatocin kasashen yammaci suke sanya wa kafafen watsa labaransu ne ya hana al’ummominsu fahimtar hakikanin abin da ke faruwa a Gaza. To amma wannan aika-aikan ya yi munin da bayyanar da ko da wani bangare nasa ne a kafafen watsa labaran yammaci kawai, ya isa ya motsa wadanda ba musulmi ba ma su fito kan tituna.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin yadda aka yi watsi da al’ummar Gaza da barin su su kadai, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Sakonmu ga gwamnatocin kasashen musulmi shi ne ku taimaki wadanda ake zalunta. Mu farka mu nuna cewa kasashen musulmi fa ba za su taba zama da zuba ido wajen fada da zalunci ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajen cimma wannan manufar, wajibi ne gwamnatocin kasashen musulmi su yi watsi da sabani na siyasa da wanda ba na siyasa ba a tsakaninsu. Dukkaninmu mu hada hannunmu waje guda wajen taimakon wadanda ake zalunta da kwato su daga bakin wannan bakar kura, sahyoniyawa mashaya jini.

A saboda haka ne ma Jagoran ya ambaci wasu abubuwa guda biyu a matsayin nauyi da kuma ayyukan da suka wajaba a kan kasashen musulmi inda ya ce: Na farko shi ne samar da abubuwan bukata na rayuwa ga mutanen Gaza. Na biyu kuma shi ne daukar tsauraran matakai kuma wanda ya dace a kan gwamnatin sahyoniyawa masha jini da kuma masu goyon bayanta.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da gagarumar bukatar da mutanen Gaza suke da ita na abinci, ruwan sanya, magani, kayayyakin asibiti da na sake gina gidajensu da aka rusa, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Haka nan kuma wannan al’umma tana bukatar makami wajen kare kanta.

 

Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake kiran gwamnatocin kasashen musulmin da cewa: Ku zo mu hada hannayenmu waje guda don taimakon mutanen Gaza da kawo karshen takunkumin da sahyoniyawa suka sanya musu. Mu yi aiki da nauyi na addini da dan’adamtaka da ke kanmu.

Jagoran ya bayyana fada da kuma nuna kyamar wadanda suke da hannu tsawon tarihi cikin irin wannan zalunci da ake yi wa mutanen Gaza a matsayin wani nauyi na biyu da ke wuyan kasashen musulmi inda ya ce: Lalatattun sahyoniyawa da masu goya musu baya cikin kashe kananan yara da suke yi, cikin rashin kunya da rashin mafadi suke halalta wannan danyen aiki na su. Lalle hakan lamari ne da ke tabbatar da kolin lalata da rashin kunyarsu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin goyon baya a fili da ma’abota girman kan duniya musamman Amurka da Ingila da kuma irin shiru da gangan da cibiyoyin kasa da kasa cikin kuwa har da Majalisar Dinkin Duniya kan irin aika-aikan da sahyoniyawa suke yi, hakan yana a matsayin tarayya cikin wannan danye aiki da zubar da jini ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Al’ummomin musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi suna da nauyi a wuyansu na barranta da nuna kyamarsu ga masu goyon bayan ‘yan ta’addan da suke mulki a Tel Aviv. Idan kuma har zai yiyu su sanya musu takunkumi na siyasa da tattalin arziki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa al’ummar Iran saboda tsayin dakan da suka yi wajen bayyanar da goyon bayansu a fili ga al’ummar Gaza da kuma tsayin dakan da suka yi wajen tinkara masu wuce gona da iri a kansu yana mai cewa: A Juma’ar karshe ta watan Ramalana, duniya ta ji muryar nuna goyon baya ga wadanda aka zalunta daga Iran. Don haka wannan al’umma ta Iran, baya ga irin wannan goyon bayan, har ila yau kuma duk wani abin da za ta iya a wannan fagen za ta yi shi da dukkan karfinta.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Sheikh Hasan Ruhani a gabatar da jawabinsa inda ya isar da sakon taya murnar wannan idi ga al’ummar musulmi da kuma bayyana shi a matsayin idin al’ummar musulmi.

Shugaba Ruhani ya yi ishara da aika-aikan da ke faruwa a Gaza inda ya ce: Ko shakka babu azumi ba zai taba tafiya tare da munanan halaye ko kuma yin shiru a gaban tsokanar yaki da aikata aika-aika.

Sheikh Ruhani ya ci gaba da cewa: A wadannan ranaku sahyoniyawa suna ci gaba da kai hare-hare Gaza da zubar da jinin kananan yara da ba su ci ba su sha ba.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wata matsalar da take fuskantar kasashen musulmi wacce ita ce yadda wasu suke amfani da “sunan Musulunci, addini da halifanci” suke kashe musulmi da sauran bil’adama, shugaba Ruhani cewa yayi: Dukkanin sharhin da ake yi na nuni da cewa tushen wadannan matsaloli biyu (ta sahyoniyawa da ta masu kafirta musulmi) guda ne.

Shugaban na Iran ya bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin wani kisan kiyashi da kuma laifin yaki inda ya ce: Wajibi ne a kan dukkanin cibiyoyi da kungiyoyi na kasa da kasa da suke magana kan kare hakkokin bil’adama su shirya hukumta wadannan masu laifin wadanda a kullum rashin imani da tausayinsu sai dada fitowa fili suke yi.

Sheikh Ruhani ya ci gaba da cewa: Babu wata hanyar magance wannan matsalar da ta wuce hadin kan duniyar musulmi, bayanin koyarwar Musulunci da ke cike da rahama da tausayi da kuma nesantar gurguwar fahimta.

Shugaba Ruhani ya ce siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duniya ita ce tabbatar da sulhu da adalci, sannan a duniyar musulmi kuma ‘yan’uwantaka da hadin kai da samar da al’umma guda ta Musulunci. Shugaban ya ci gaba da cewa: Mutanen da suke mafarkin raunana Musulunci da musulmi, ko shakka babu ba za su cimma wannan manufa ta su ba.

Daga karshe shugaba Ruhani ya jaddada cewar: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da kokari da dukkan karfinta wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro da kawo karshen kisan gilla da zubar da jini da tabbatar da sulhu cikin adalci a wannan yankin. Sannan kuma duniyar musulmi, da yardar Allah da kuma farkawa da taka tsantsan din da za ta yi bugu da kari kan hadin kai, za ta yi nasara.

Mun Samo Wannan Labarin Ne A Shafin Jagora Imam Khamenei

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook