A+ R A-
25 May 2020

An Yi Wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Aikin Tiyata A Wani Asibitin Tehran

A safiyar yau Litinin (08-09-2014) ne aka yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei aikin tiyata a wani asibitin gwamnati da ke nan birnin Tehran, inda alhamdu lillahi an gama aikin cikin nasara.

Jim kadan kafin barinsa gida zuwa asibitin, Ayatullah Khamenei ya shaida wa dan jaridar gidan radiyo da talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa: A halin yanzu ina kan hanya ta ne na zuwa asibiti don wani aiki na tiyata.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas ba lamari ne abin damuwa ba, ko da yake hakan ba yana nufin mutane ba za su yi min addu’a ba ne, amma dai babu abin damuwa cikin hakan. Wata tiyata ce karama da aka saba da ita.

Daga karshe Ayatullah Khamenei ya ce: Insha Allahu cikin yardar Allah za a yi a gama lafiya.

Alhamdu lillahi cikin dan karamin lokaci an gama tiyatar lafiya kuma cikin nasara.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook