A+ R A-
29 February 2020

Shugaban Likitocin Da Suka Yi Tiyata Wa Jagora: Jagora Yana Cikin Koshin Lafiya

A wata hira da yayi da manema labarai, shugaban likitocin da suka yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei tiyata a safiyar yau, wato Dakta Marandi, ya bayyana farin ciki da jin dadinsa dangane da yadda aka gudanar da aikin tiyatar yana mai cewa: An gudanar da aikin tiyatar ne ba tare da amfani da allurar sa barci mai karfi ba, lalle Jagoran yana cikin koshin lafiya ba tare da wata damuwa ba.

Dakta Marandi ya kara da cewa: irin wannan tiyatar da aka yi wa Jagoran wani lamari ne da aka saba da shi musamman ga mutane masu shekaru.

Dakta Marandi ya kara da cewa: A wani lokaci a baya ne wannan cuta ta bayyana wa Jagoran, to amma a yanzu ne likitoci suke ganin ya dace a yi masa aiki. Shi ma Jagoran ya yi na’am da wannan hukumci na likitocin.

Dangane da aikin da aka yi kuwa, shugaban likitocin ya bayyana cewar: A safiyar yau ne aka gudanar da wannan aikin cikin kasa da rabin sa’a, kuma an gudanar da aikin cikin nasara ba tare da amfani da allurar sa barci mai karfi ba.

Ya ci gaba da cewa: Tsawon lokacin aikin tiyatar Jagoran juyin juya halin Musuluncin yana cikin hayacinsa, yana ma magana. A halin yanzu ma yana cikin yanayi mai kyau. Ya ma bukace ni da in isar da gaisuwa da sallamarsa ga al’umma.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin jajircewar da Ayatullah Khamenei ya yi na a gudanar da aikin tiyatar a wani asibiti na gwamnati, Dakta Marandi cewa ya yi: Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa bai kamata a matsa wa sauran asibitocin ba, don haka ne aka gudanar da aikin da sanyin safiya.

Yayin da yake amsa tambaya dangane da lokacin da za a sallami Jagoran juyin juya halin Musuluncin daga asibiti, Dakta Marandi ya ce: A dabi’ance bayan irin wannan aikin tiyatar a kan dauki kwanaki uku zuwa biyar ana sa ido a kan mara lafiya a asibiti. A saboda haka shi ma haka za a masa.

Likitan ya ci gaba da cewa: Bayan sallamarsa ma dai, tamkar dukkanin marasa lafiya, akwai ‘yan wasu abubuwa da zai kula da su irin su yawan aiki. Duk da cewa shi din nan mutum ne mai ayyuka da yawan gaske, to amma wajibi ne ya rage ayyukan da yake yi na tsawon makonni, wasu ayyukan ma wajibi ne ya daina su.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook