A+ R A-
13 July 2020

Imam Khamenei: Makiya Na Kokarin Sanya Tazara Tsakanin Iran Da Kasashen Musulmi

A safiyar yau Talata (28-10-2014) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da jami’ai da ma’aikatan aikin hajjin bana na Iran inda ya bayyana tsara shirye-shirye da nufin “fadada ayyukan hajjin” da mahanga ta sauyi da shigo da sabbin abubuwa da nufin biyan “bukatu na ruhi da tunanin mutanen da ake magana da su” haka nan kuma da “fada da bakar farfagandar makiyan Musulunci” a matsayin wani lamari da ya zama wajibi a aikata shi, don haka sai Jagoran ya ce: Kokarin haifar da tazara tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen musulmi, daya ne daga cikin makircin masu adawa da hadin kan al’ummar musulmi. Don haka wajibi ne a yi amfani da aikin hajji a matsayinsa na wajen taron al’ummar musulmi wajen kawar da wannan tazarar da kuma sauya irin gurguwar fahimtar da ake da ita sakamakon bakar farfagandar makiya.

Haka nan kuma yayin da yake karin haske dangane da yadda za a kara fadada ayyukan hajji, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da batutuwa guda biyu, wato ‘karfafa hidima’ da kuma ‘lamunce abubuwa da bayanan da maniyyatan da ake magana da su suke bukata’ inda ya ce: Kyautata yanayin aikin hajji na hakika tana cikin biyan bukatu na ruhi da tunani da mahajjatan suke da su. Hakan kuwa ya kumshi kara kyautata ayyukan da ake gudanarwa irin su taron Du’a Kumail, taron barranta daga mushirikai da sauran tarurrukan da ake gudanarwa, sannan kuma a yi kokarin wajen amsa wa alhazan da ake magana da su tambayoyin da suke da su musamman dangane da abubuwan da suke faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hadin kan musulmi a matsayin babbar bukatar da al’ummar musulmi suke da ita a yau din inda ya ce: hadin kai da ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi wani bangare ne na tushen koyarwar addininmu. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta wasa da wannan bangaren.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa hadin kai na Musulunci ba yanayin nufin sauyawa daga akidar wata mazhaba zuwa ga wata ba ne, Jagoran cewa ya yi: Hadin kai na Musulunci wanda wani tushe ne na taken da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take rerawa, yana nufin kada al’ummar musulmi su yi fada da kuma adawa da junansu ne sannan kuma su dinga goyon bayan juna cikin batutuwa masu muhimmanci na duniya.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da yadda marigayi Imam Khumaini (r.a) ya mayar da taken “hadin kan musulmi” ya zamanto wata siyasa a hukumance kuma ta fili ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da kokarin da makiya suka yi wajen haifar da tazara tsakanin musulmi da nufin kawo karshen wannan take na hadin kai a tsakaninsu inda ya ce: Wajibi ne kowa da kowa ya yi kokari wajen kawar da wannan katanga ta rarrabuwan kai da makiya suka gina. Aikin hajji kuwa a matsayinsa na wajen taruwar musulmi, wata babbar damar ce da kuma yanayin da ya dace wajen wannan kokarin.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da bakar farfagandar da makiya suke yadawa da nufin haifar da gurguwar fahimta da tunani kan Shi’anci da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin daya daga cikin hanyoyin da makiyan suke bi wajen raba Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen musulmi. Daga nan sai ya ce: Rubuta littafi kawai da nufin amsa wadannan shubuhohi da ake gabatarwa ba ta wadatar ba, face dai wajibi ne a gudanar da bincike da gano hanyoyin da za a bi wajen sauya irin wannan fahimta da kuma bakar farfaganda da ake yadawa.

Daga karshe Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin gano abubuwan da suke sanya mutane yarda da bakar farfagandar da makiya suke yadawa da nufin fada da kuma maganin hakan.

Tun da fari dai sai da Hujjatul Islam wal muslimin Qadhi Askar, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma Amirul hajji na Iran ya gabatar da rahoto kan ayyukan da aka gudanar yayin aikin hajjin na bana inda ya ce: Daga cikin ayyukan da aka gudanar sun hada da gudanar da tarurrukan karatun Alkur’ani, tafsiri da kuma haddarsa, gudanar da tarurrukan Du’a Kumail da Du’a Arafa, amfani da masana wajen bayayin koyarwar aikin hajji, jinjinawa iyalan shahidai da girmama wadanda suka sami raunuka a lokacin yaki, gudanar da tarurrukan malamai da sauran masana da alhazai da nufin karfafa alakar da ke tsakanin mabiya mazhabobi, batun Palastinu da Ahlulbaitin Annabi (a.s) da kuma hadin kai tsakanin musulmi.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban hukumar aikin hajji na Iran malam Auhadi ya gabatar da rahoton ayyukan da hukumar tasa ta gudanar inda ya ce alhazan Iran dubu 64 ne suka gudanar da aikin hajjin na bana sannan kuma an gudanar da tsare-tsare masu kyau wajen tabbatar da jin dadinsu da suka hada wajen zama da kuma abubuwan da za su ci.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook