A+ R A-
26 May 2020

Imam Khamenei: An Kirkiro Kungiyoyin Takfiriyya Ne Don Bakanta Sakon Musulunci Na Hakika

A safiyar yau Litinin (17-11-2014) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci bikin rantsuwa da yaye daliban hadin gwiwan jami’oin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran karo na takwas da aka gudanar a Jami’ar jami’an soji ta Imam Ali (a.s).

Jim kadan bayan isowarsa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ziyarar makabartar shahidan da ke jami’ar inda ya karanta musu Fatiha da roka musu karin matsayi da daukaka a wajen Allah Madaukakin Sarki, kana daga baya kuma ya halarci filin faretin da daliban suka shirya.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Ayatullah Khamenei ya bayyana dakarun sojin a matsayin tushen tsayin daka da karfi na kowace kasa inda ya ce: Imani, basira, tsayayyiyar azama da jin nauyi na hakika tare da karfi na dan’adam bugu da kari kan kwarewa ta aiki da kuma kayan aiki na zamani, wani bangare ne da ke tabbatar da karfi da tsayin daka na hakika a cikin soji.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu duniya tana bukatar sakon Musulunci na hakika don haka sai ya ce: masu fatan sharri da ‘yan mulkin mallaka na duniya suna kokari ta hanyar amfani da fasaha da siyasa da karfin soji da dukkanin karfin da suke da shi wajen hana isar wannan sako da murya ta Musulunci zuwa ga al’ummomin duniya. To amma tuni wannan sakon ya isa kunnuwan duniya. Alamar da ke tabbatar da hakan kuwa ita ce irin damuwar da ma’abota girman kai suke ciki a kowace rana.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin ba wa lamarin karfin dakarun soji na kasa muhimmanci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Yawan sojoji da makamai da kwarewa ta soji kawai ba su isa su tabbbatar da karfin sojojin wata kasa ba, face dai wajibi ne a sami kumaji da karfin gwiwa da azama da fahimtar hakikanin nauyin da ke wuya.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin karfi na ruhi da ilimi da azama bugu da kari kan tsayin daka da sojojin na Iran suke da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci wanda kuma shi ne babban kwamandan sojin na Iran ya bayyana cewar: A halin yanzu dai duniya ta zuba ido kan dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran, don kuwa sun san cewa a duk inda ake magana kan fagen daga, to kuwa dakarun Iran suna da bakin magana.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin nasarorin da jami’ar jami’an soji ta Imam Ali (a.s) da shahidan jami’ar suka cimma, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi daliban jami’an da cewa: Ku shirya kanku wajen daukaka da kuma karfafa dakarun soji a matsayinsu na wani bangare na tushen karfin kasar Iran.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa a halin yanzu sama da shekarun da suka gabata bil’adama suna bukatar sakon Musulunci da al’ummar Iran suka gabatar da shi. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: ‘yan mulkin mallaka da masu takama da karfi na duniya suna cikin damuwa dangane da irin yadda sakon Musulunci na hakika ke ci gaba da samun karbuwa a wajen al’ummomin duniya wanda suke ganin hakan a matsayin barazana a gare su da kuma manufofinsu. Don haka ne suke amfani da duk wani karfi da suke da shi musamman karfi na fasaha wajen sanya kyamar Musulunci a zukatan al’ummomin duniya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kirkiro kungiyoyi masu dauke da makami da sunan Musulunci da hukumar Musulunci, inda suke ci gaba da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba a matsayin daya daga cikin hanyoyin da makiya suke amfani da su wajen sanya kyamar Musulunci a zukatan al’ummomin duniya, daga nan sai ya ce: Sakon Musulunci na hakika ga bil’adama, wani sako ne na zaman lafiya, daukaka da rayuwa cikin tsaro da kwanciyar hankali. Don haka ne makiya da masu fatan sharri ba sa kaunar ganin wannan sako ya isa ga al’ummomin duniya.

Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi daliban jami’ar jami’an sojin ta Imam Ali (a.s) da cewa: Zuriyar da suka gabace ku, sun dauki nauyin sakon Musulunci na hakika a wuyansu a fagen daga da siyasa da juyin juya hali da isar da shi zuwa ga al’ummomin duniya. To a halin yanzu ga ku nan magada wadannan shahidai masu girma da mutane madaukaka, kun dauki nauyin isar da wannan sako ga al’ummomin duniya.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da shugaban jami’ar jami’an sojin ta Imam Ali (a.s), Birgediya Janar Fuladi ya gabatar da jawabin maraba da Jagoran da kuma gabatar da rahoto kan tsare-tsare da kuma ayyukan horarwa da tarbiyya da ake gidanarwa a jami’ar da nufin karfafa basira da kuma fahimta ta addini ta sojojin da kuma karfafa irin kwarewa da horarwa ta soji da suke samu.

Har ila yau a yayin bikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba wa kwamandoji, malamai da daliban da suka nuna bajinta bugu da kari kan daya daga cikin uwayen shahidan Iran lambar girma ta girmamawa saboda irin kwazon da suka nuna kamar yadda kuma aka gabatar da daliban da suka kammala karatun na su shaidar gama karatu da kuma karin girma na soji da suka samu.

Daga karshe kuma daliban jami’an sun gudanar da fareti da kuma gwada wani bangare na horarwa da suka samu tsawon lokaci karatun na su.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook