A+ R A-
26 May 2020

Imam Khamenei: Lalatacciyar Zuriyar Al Saud Ba Ta Cancani Kula Da Lamurran Haramomin Makka Da Madina Ba

A safiyar yau Laraba (08-09-2016) ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da iyalan shahidan Mina da Masjidul Haram inda ya bayyana cewar gazawa da rashin cancantar da Al Sa’ud suka nuna cikin wannan lamarin ya sake tabbatar da rashin cancantar wadannan la’ananniya kana maketaciyar zuriya wajen kula da kuma gudanar da lamurran haramomin nan guda biyu masu tsarki; daga nan sai ya ce: Idan har da gaske suke yi ba su da hannu cikin wannan lamarin, to su bari mana wani kwamitin bincike na kasashen musulmi da kuma na kasa da kasa ya gudanar da bincike da kuma fitar da sakamakonsa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ganawa da iyalan shahidan Mina da Masjidul Haram a matsayin wani lamari mai sake tunatar da wannan lamari mai sosa rai da ya faru a bara inda ya ce: Hatsarin Mina da rasuwar alhazan kasar Iran suna cikin ibada sannan kuma ga kishirwa da kuma zafin rana mai tsanani, lalle wani lamari ne mai sosa rai wand aba za a taba mantawa da shi ba. Tabbas wannan lamarin yana da bangarori daban-daban a mahanga ta siyasa, zamantakewa, kyawawan halaye da addini, wanda bai kamata a mance da wadannan bangarori ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: A shekarar bara, fuskantar iyalai da ba su labarin mutuwar iyalansu da kuma dawo da gawawwakinsu wani lamari ne mai wahalar gaske, to amma duk da hakan bisa la’akari da cewa wadannan iyalai na su shahidai ne wadanda suke karkashin inuwar gafara da rahama da ni’ima ta Ubangiji, hakan yana sanya musu kwanciyar hankali a gare su da kuma rage damuwar da suke ciki.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da shahadar kimanin alhazai dubu 7 a yayin wannan turmutsutsu na Mina, Ayatullah Khamenei yayi kakkausar suka dangane da halin ko in kula da kasashe da gwamnatoci suka nuna dangane da wannan lamari mai girman gaske.

Jagoran ya bayyana shirun da gwamnatoci hatta ma da malamai, ‘yan siyasa, masana da masu fadi a ji na kasashen musulmi suka yi dangane da shahadar alhazai kimanin dubu 7 a matsayin wani babban bala'i da ya sami al’ummar musulmi, yana mai cewa: Nuna halin ko in kula dangane da lamurra mai sosai da tada hankali irin abin da ya faru a Mina, shi ne babban bala’in da ke fuskantar duniyar musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kin neman afuwa hatta ta fatar baki da mahukuntan Saudiyya suka yi kan wannan lamari na Mina a matsayin babban wauta da rashin kunyarsu yana mai cewa: Koda a ce babu ganganci cikin lamari, to amma shi kansa irin wannan rashin tsari da rashin cancanta na mahukuta da 'yan siyasa babban laifi ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da wannan jawabi nasa a yayin ganawa da iyalan shahidan na Mina da gabatar da wata tambaya cewa: A lokacin da wata gwamnati ta nuna gazawa wajen kula da bakin Dakin Allah wadanda su din wata hanyar samun kudin shiga ne ma a wajenta,  shin wani lamuni ake da shi cewa irin wannan abin da ya faru a Mina din ba zai sake faruwa a irin wannan lokacin ba?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Al'ummar Iran  dai cikin dukkanin jaruntakan sun tsaya kyam wajen tinkarar wannan jahilci da bata na Al Sa'ud da kuma bayanin mahangar Alkur'ani a kan su a fili. Don haka wajibi ne sauran al'ummomi ma cikin dukkan jaruntaka su ci kwalar mahukuntan Saudiyya.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A hakikanin gaskiya gazawar mahukuntan Saudiyya da kuma rashin tsaron da suka sanya alhazan Dakin Allah ciki, wata alama ce da ta ke nuni wannan hukumar ba ta cancanci kula da kuma gudanar da ayyukan haramomi guda biyu masu tsarkin nan ba. Don haka wajibi ne duniyar musulmi ta fahimci haka.

 

Ayatullah Khamenei ya bayyana irin shiru da halin ko in kulan da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama na duniya suka yi dangane da wannan lamari na Mina a matsayin wani bangare na wannan lamari.

Yayin da yake ishara da irin yadda kungiyoyi masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi suka cika duniya da maganganu dangane da zartar da wasu hukunci na shari'a a wasu kasashen, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Shiru da halin ko in kula da kungiyoyin kasa da kasa masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suka yi dangane da gazawar wata hukuma wajen sauke nauyin da ke wuyan da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 700 da ba su ci ba su sha ba, wani lamari ne da tabbatar da rashin gaskiyar wannan ikirari na su na kare hakkokin bil'adama. Don haka wajibi ne  mutanen da suke da wata fata kan irin wadannan kungiyoyi na kasa da kasa su dau darasi daga wannan lamari mai sosa rai.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kafa wani kwamitin bincike na kasa da kasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da ya hau kan kasashen musulmi da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama inda ya ce: Duk da shekara guda kenan da faruwar wannan lamari mai bakanta rai, to amma gudanar da bincike kan bayanai na faifayin bidiyo da sautuka da kuma abubuwan da aka rubuta za su taimaka sosai wajen gano hakikanin abin da ya faru.

Haka nan yayin da ya ke kiran jami'an Iran da su ci gaba da bin wannan lamari na ganin an kafa kwamitin binciken, Jagoran cewa yayi: Idan har Al Sa'ud suna da tabbaci kan ikirarin da suke yi na rashin hannu cikin wannan lamari na Mina, to su kuji rufe bakin mutane ta hanyar ba su cin hanci, su bari kwamitin bincike ya gudanar da bincikensa kan lamarin mana.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana masu daure wa mahukuntan Saudiyya gindi a matsayin wadanda suka yi tarayya da su cikin wannan lamari na Mina inda ya ce: Gwamnatin marasa kunya ta Saudiyya, bisa goyon bayan Amurka, tana ci gaba da zubar da jinin al'ummomin kasashen Yemen, Siriya, Iraki da Bahrain. A saboda haka Amurka da sauran masu goyon bayan Saudiyya sun yi tarayya cikin wannan danyen aiki na mahukutan Saudiyyan.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da kokarin da kafafen watsa labaran da suke da alaka da gidan sarautar  Saudiyyan wajen bayyana abin da ya faru a Mina a matsayin daya daga cikin misalan sabanin da rikicin "Sunna da Shi'a" ko kuma "Larabawa da wadanda ba larabawa ba", Ayatullah Khamenei cewa yayi: Kafafen farfagandan Saudiyya suna  nanata wannan tsagoron karya din ne alhali kuwa daga cikin sama da shahidan Mina dubu 700, wadanda wani adadi mai yawa na su Iraniyawa  ne, 'yan Ahlusunna ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Al Sa'ud da 'yan ta'adda marasa imani wadanda su suka samar da su suna ci gaba da zubar da jinin larabawan a Yemen da Siriya da Iraki. A saboda haka sabanin wannan bakar fargandar, mahukutan Saudiyya ba masu kare larabawa ba ne, sannan kuma abin da  ya faru a Mina ba shi da alaka da wannan sabani da rikici na boge tsakanin larabawa da wadanda ba larabawa ba.

Jagoran ya jaddada cewar: Hakikanin lamarin dai shi ne cewa mahukutan Saudiyya abin kyama a zukatan al'umma, wata jama'a ce cikin duniyar wadanda wasu daga cikinsu sun sani ko ba su sani ba sun shagaltu da kiyayya da musulmi. Don haka ya zama wajibi al'ummar musulmi su bayyanar da bara'a da kiyayyarsu ga iyayengijin Saudiyyawan wato Amurka da Ingila lalatacciya ta hanyar tinkarar wadannan mahukutan na Saudiyya.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook