A+ R A-
29 February 2020

Aikin Hajji A Mahangar Jagora Ayatullah Sayyid Imam Khamenei

A wata ganawa da yayi da jami'an aikin hajjin bana na Iran a safiyar jiya Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar aikin hajj wata dama ce ta bayyanar da matsaya dangane da lamurran da suka shafi al'ummar musulmi.

Har ila yau a cikin jawabin da yayin wannan ganawar, Jagoran yayi ishara da girman kan sahyoniyawan haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma ci gaba da keta hurumin Masallacin Kudus da suke yi da hana asalin ma'abota masallacin shigarsa don gudanar da ayyukan ibadunsu don haka sai ya ce: Bai kamata al'ummar musulmi su gafala da kuma rufe ido kan matsalar Palastinu ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Shin akwai wani wajen da ya fi dacewa da bayyanar da akida da kuma matsayar al'ummar musulmi kan abin da ya shafi Palastinu da kuma Masallacin Kudus kamar Dakin Allah Mai Alfarma da garin Makka da Madina da Arafat da Mash'ar da kuma Mina?

Ko shakka babu wannan jawabi na Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da aikin Hajj musamman a bangaren sake tunatar da al'ummar musulmi nauyin da ke wuyansu kan batun Palastinu da Masallacin Kudus, wani lamari ne da ke nuni da irin tasirin da aikin Hajji yake da shi dangane da makomar duniyar musulmi ta bangarori daban-daban.

A halin yanzu dai duniyar musulmi tana fuskantar kalubale masu girman gaske irin su ayyukan ta'addanci kungiyoyin 'yan takfiriyya masu kafirta al'umma, wanda ya zama wajibi, a yayin aikin Hajjin, al'ummar musulmi su bayyanar da matsayarsu kan wannan annobar.

Ko shakka babu aikin hajji wata dama ce ta bayyanar da irin karfi da daukakar  al'ummar musulmi da kuma kalubalantar lalatattun gwamnatocin da babu abin da suka sa a gaba in ban da kokarin biyan bukatun gwamnatocin ma'abota girman da mika wuya ga Amurka da sahyoniyawa don dai su ci gaba da zama a kujerar mulkinsu.

A saboda haka ne ma Ayatullah Khamenei ya bayyana batun hadin kan al'ummar musulmi a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske kana kuma na wajibi, inda ya ce: A daidai lokacin da ake ci gaba da kashe biliyoyin daloli da nufin haifar da fitina da rarrabuwar kai tsakanin musulmi, wajibi ne musulmi su yi taka tsantsan wajen ganin ba su taimaka wa wannan kokari na gwara kan musulmi ba.

Wajibi ne kasashen musulmi su fahimtar ummul aba'isin din wadannan matsaloli da ake fuskanta kana kuma su amince da hakikar da take kasa. Ko shakka babu daya daga cikin manufofin ma'abota girman kai na haifar da rashin tsaro da yake-yake a kasashen daban-daban na musulmi ita ce mancewa da lamarin Palastinu. Sakamakon irin wannan yanayi na rikici da yake-yake da aka haifar a kasashen Siriya, Yemen da Iraki, hakan ya ba wa haramtacciyar kasar Isra'ila damar ci gaba da aikata aika-aika a kan al'ummar Palastinu da kuma ci gaba da aiwatar da siyasarsu ta mamaya.

Ko shakka babu jaddadawar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin yake yi dangane da irin rawar da aikin Hajji zai iya takawa wajen tona asiri da kuma maganin makirce-makircen ma'abota girman kai da kuma yahudawan sahyoniya a kasashen musulmi lamari ne da ke nuni da irin mahangarsa kan muhimmancin aikin hajji wajen magance matsaloli daban-daban da al'umma suke fuskanta. A saboda haka ya zama wajibi a yi amfani da wannan gagarumar dama wajen kara karfafa irin karfin da al'ummar musulmi suke da shi. Don kuwa Hajj na dukkanin musulmi wanda yake da fagage na zamantakewa da siyasa da za a iya amfanuwa da su wajen ciyar da al'umma gaba da tabbatar da hadin kai a tsakaninsu.

Tarihin Janar Qasim Soleimani

Taƙaitaccen Tarihin ...

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Tarihin Rayuwar Abu Mahdi Al-Muhandis

Taƙaitaccen Tarihin ...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook