A+ R A-
23 October 2019

Sayyid Nasrallah: Amurka Ce Take Hana Yakar Da'esh/Saudiyya Ce Tushen Fitina

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar Amurka ce take hana kokarin da ake yi na ganin karshen kungiyar ta'addancin nan ta Daesh, kamar yadda kuma Saudiyya da H.K.Isra'ila su ne ummul aba'isin din rashin tsaron da ake fuskanta a yankin Gabas ta tsakiya.

Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau din nan wajen tunawa da daya daga cikin kwamandojin kungiyar Ali al-Hadi al-Asheq da kuma daya daga cikin dakarun kungiyar Mohammad Nasserdine da suka yi shahada yayin fada da 'yan ta'adda a kasar Siriya inda ya ce Amurka ce ta ke hana kokarin da ake yi na ganin bayan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh.

Sayyid Nasrallah ya ce Amurka tana taimakon 'yan ta'addan na Daesh ta hanyar sansanin sojinsu da ke garin Raqqah na kasar Siriya da kuma wani sansanin da suke da shi da ke kan iyakan kasar Siriya da Jordan inda suke ba wa 'yan Daesh din horon soji yana mai cewa jiragen yakin Amurkan su ne suke hana sojojin Siriya da dakarun Hizbullah ci gaba da kwato yankunan da 'yan Da'esh din suke rike da su a kasar Siriyan.

Yayin da ya koma kan batun rashin tsaro da ake fuskanta a yankin Gabas ta tsakiya, Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar Saudiyya da Haramtacciyar kasar Isra'ila su ne tushen duk wani rashin tsaro da yake-yake da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya yana mai ishara da irin rawar da Saudiyya din take takawa wajen yakin da ke faruwa a kasashen Siriya, Iraki da Yemen.

Yayin da ya koma kan rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran kuwa, Shugaban kungiyar Hizbullah din ya ce matsalar Amurka da Iran ba shi ne batun shirin nukiliya ba face dai matsalar ita ce nasarar da Iran ta samu a kan makirce-makircen Amurka da Saudiyya.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan takunkumin da Amurka ta sanya wa kungiyar tasa kuwa, Sayyid Nasrallah ya ce hakan babu wani abin da zai sauya wajen azamar kungiyar na ci gaba da ayyukanta na gwagwarmaya.

 

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Samun Labaranmu Ta H...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook
Labaranmu Ta Google+