A+ R A-
18 September 2020

Shawarwarin Sayyid Nasrallah Ga Al'umma Da Shugabannin Kasashen Musulmi Kan Matsayar Donald Trump Kan Qudus

A jawabin da yayi dazu-dazun nan kan matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin 'Isra'ila' da kuma sanar da shirin Amurkan na mayar da ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya gabatar da wasu shawarwari da al'umma da shugabannin kasashen larabawa da na musulmi dangane da yadda za a bullo wa wannan lamarin, a matsayin farko don tilasta wa shugaban Amurkan janye wannan mataki da ya dauka.

A takaice ga su nan:

- Shirya zanga-zangogi da jerin gwano da tarurruka don nuna rashin amincewa da wannan matakin da kuma nuna goyon baya ga Qudus da al'ummar Palastinu.

- Amfani da kafafen watsa labarai na sada zumunci na zamani (social medias) irin su Twitter, Facebook etc wajen bayyana rashin amincewa da wannan mataki da kuma nuna goyon baya ga Qudus da al'ummar Palastinu.

- Gwamnatocin kasashen larabawa da na musulmi su kirayi jakadun Amurka a kasashen na su don nuna musu rashin amincewa da wannan mataki.

- Rufe ofisoshin jakadancin 'Isra'ila' a kasashen larabawa da na musulmi da suke da alaka da ita da kuma korar jakadunta daga wadannan kasashe.

- Dakatar da duk wata alaka da tattaunawa da 'Isra'ila' ta fili da ta boye da wasu kasashen larabawa su ke yi.

- Dakatar da duk wani shiri na zaman lafiya da 'Isra'ila' da larabawa suke yi har sai Amurka ta janye wannan matsaya da ta dauka.

- Kungiyoyin Hadin kan kasashen Larabawa da na Hadin kan kasashen Musulmi (OIC) da su fitar da kuduri da wajibi ne kowace kasar da ke cikin kungiyoyin biyu su aiwatar da shi da ya kumshi bayyanar da Qudus a matsayin babban birnin kasar Palastinu.

 

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook