A+ R A-
25 May 2020

Kwamandan IRGC: Iran Ba Ta Son Yaki Amma Ba Ta Tsoron Faruwarsa

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC), Manjo Janar Husain Salami ya bayyana cewar Iran dai ba ta son yaki, sai dai kuma ba ta tsoronsa.

Janar Salami ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a yau din nan Lahadi (19-05-2019), inda ya ce a halin yanzu dai Iran tana fuskantar barazana a kusa da kan iyakokinta, don haka dakarun kare juyin sun shirya don tinkarar wannan barazanar.

Babban kwamandan dakarun na IRGC ya ci gaba da cewa: Mu dai ba ma neman yaki, to sai dai ba ma tsoronsa, duk da cewa makiyan na mu ba su da kwarin gwiwan kaddamar da yakin kamar yadda kuma suna tsoron yakin.

Don haka sai ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin dukkanin shirin da ya kamata ta kasance cikinsa don kare kanta daga duk wata barazana.

Babban kwamandan dakarun kare juyin yana mayar da martani ga ci gaba da barazanar da gwmnatin Trump ta Amurka take yi ne wa Iran da kuma ci gaba da kada kugen yakin da take yi lamarin da ke ci gaba da fuskantar nuna tashin amincewa daga ciki da wajen Amurkan.

Kafin hakan ma dai, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi watsi da batun abkuwar yaki tsakanin Iran da Amurka yana mai cewa Amurka ta san cewa kaddamar da yaki a kan Iran wani lamari ne da ba zai haifar mata da da mai ido ba.