A+ R A-
25 May 2020

Nasrallah: Hizbullah Za Ta Ci Gaba Da Kokari Wajen Ganin Amurka da Isra’ila Ba Su Cimma Bakar Aniyarsu Ba

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na kokari ne wajen raunana irin goyon bayan da kungiyar take da shi da kuma mai da ita saniyar ware a duniya.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa dubun dubatan magoya bayan kungiyar a yammacin jiya Asabar (25-05-2019) inda ya ce haramcciyar kasar Isra’ilan tana bayyana kungiyar Hizbullah a matsayin babbar barazana a gare ta ne da nufin samun goyon bayan kasashen duniya don fada da kungiyar.

Sayyid Nasarallah ya ce kungiyar Hizbullah dai ta tsaya kyam wajen fada da kuma hana Amurka da ‘Isra’ila’ cimma burinsu na mallake yankin Gabas ta tsakiya, kuma za ta ci gaba da yin hakan.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ci gaba da cewa: Idan da ba don kungiyar Hizbullah ba, da kuwa Amurka ta mika kudancin kasar Labanon ga Isra’ila. Don haka sai ya ce al’ummar Labanon za su ci gaba da neman hakkokinsu da kuma kwato yankunan kasar da suke karkashin mamayar sahyoniyawa.

A bangare guda kuma Sayyid Nasrallah ya sake jaddada aniyar kungiyarsa ta ci gaba da goyon bayan hakkokin al’ummar Palastinu da kuma hakkin da suke da shi na dawowa kasarsu.

Haka nan kuma Sayyid Nasrallah ya kirayi al’umma da su fito don raya Ranar Qudus ta duniya da za a gudanar a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramalana don nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da masallacin Kudus da kuma yin Allah wadai da sahyoniyawan duniya da masu goya musu baya.

Labaran Da Suka Yi Kama Da Wannan

Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook