A+ R A-
22 February 2024

Dakarun IRGC Na Iran Sun Dakile Makarkashiyar Kashe Janar Soleimani

Sashen tattaro bayanan sirri na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) ya sami nasarar dakile wata makarkashiyar kashe kwamandan dakarun Qudus (Qud's Forces) na IRGC din, Manjo Janar Qasim Soleimani, wanda ya taka gagarumar wajen kawo karshen kungiyar ta'addancin nan na Daesh (ISIS) a Iraki da Siriya kana kuma ya taimaka wa kungiyoyin gwagwarmayar Labanon da Palastinu a nasarorin da suke samu a kan 'Isra'ila'.

Shugaban sashen tattaro bayanan sirri na dakarun IRGC din Hujjatul Islam Hossein Taeb ne ya sanar da hakan a yau Alhamis inda ya ce makarkashiyar dai kungiyoyin leken asirin da ya kira na 'yahudawa-larabawa (Hebrew-Arab) ne suka shirya da kuma kokarin aiwatar da shi a lardin Kerman yayin da Janar din yake halartar taron Tasua da Ashura a Husainiyyar mahaifinsa da ke wajen. An dai shirya tayar da wasu bama-bamai ne da suka kai nauyin kilogram 350 zuwa 500 a wajen don a samu damar kashe shi.

Taeb ya ce tun bayan da mutanen da aka shirya za su aiwatar da wannan danyen aikin suka shigo Iran ake sa ido kansu kuma kafin su aiwatar da shi aka kama su.

A watan Nuwambar shekarar bara 2018, jaridar New York Times ta Amurka ta buga wani labari wata makarkashiya da Saudiyya ta kulla na kashe Janar Soleimanin a 2017 wanda take ganinsa a matsayin wanda ya ke kawo mata cikas wajen cimma manufofinta a yankin kama daga Iraki, Siriya, Labanon da kuma Yemen.

Ashura

Takaitaccen Bayani K...
Shafin Jagora Imam K...
Shafin Elwahabiya
Nemo Mu A Facebook