A+ R A-
01 April 2020

Shugaba Asad Yayi Karin Bayani Kan Dalilin Yakin Siriya

A wata hira da yayi da tashar talabijin din RT ta kasar Rasha wacce aka watsa jiya Litinin, shugaban kasar Siriya, Bashar al-Asad, yayi karin bayani masu muhimmanci, watakila a karon farko, dangane da dalilan yakin da wasu kasashe suka tilasta wa kasarsa da nufin kifar da gwamnati don cimma manufar da suke da ita.

Daya daga cikin bangarori masu muhimmanci da shugaba Asad ya tabo yayin amsa tambayoyin da aka masa, shi ne dalilin kaddamar da yaki a kan kasar Siriya a 2011.

A baya dai an ta yada cewar daya daga cikin dalilan wannan yakin ko kuma wanda shi ne a kan gaba shi ne rashin amincewar da shugaba Asad din yayi ga bukatar kasar Qatar na shimfida bututun iskar gas dinta a kasarsa da kuma Turkiyya zuwa kasashen Turai don su yi gasa da kasar Rasha. Don haka da ya ki yarda ne kasar Qatar ta jagoranci wasu kasashe wajen shigowa da ‘yan ta’adda kasar da nufin kifar da gwamnatinsa.

To sai dai shugaba Asad ya musanta hakan inda ya nuna cewa kyakkyawar alakar da Siriya take da shi da Iran musamman batun shimfida bututun iskar gas na kasar Iran da aka yi daga Gabashin Siriyan zuwa Yammaci, wanda ya fito daga kasar Iraki zuwa Siriya zuwa Kogin Mediterranean, shi ne abin da ya sa wadannan kasashe gaggauta kaddamar da yaki a kan kasar da nufin dakatar da shimfida bututun da kawo karshen alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Bayanai dai sun nuna cewa a wancan lokacin wasu kasashen larabawan Tekun Fasha, musamman gwamnatocin Qatar da Saudiyya sun gabatar wa shugaba Asad din shawarar ba shi biliyoyin daloli da nufin ya kawo karshen alakar kasarsa da Iran da kuma kin amincewa da shirin Iran na shimfida wannan bututun.

Amma shugaba Asad ya ki yarda da hakan. Wannan shi ne dalilin da ya sanya aka kirkiro wannan yakin da shigo da ‘yan ta’adda cikin kasar da nufin kawar da gwamnatin duk dai da nufin cutar da Iran, wacce ta zame musu tare da iyayengijinsu, Amurka da ‘Isra’ila, karfen kafa.