A+ R A-
01 April 2020

Dubi Cikin Matakan Da Annabi (s) Ya Dauka Wajen Tabbatar da Hadin Kan Musulmi

Daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci a tsakanin musulmi, musamman a wannan zamanin, shi ne batun hadin kai da samar da al’umma guda ma’abociyar hadin kai. A saboda haka ne a irin wadannan ranaku na maulidin Manzon Allah (s.a.w.a) mu ke so mu yi amfani da wannan damar wajen dubi cikin matakan da Annabi (s.a.w.a) ya dauka wajen tabbatar da al’umma guda da kuma hadin kai tsakaninsu.

Yayin dubi cikin wannan lamari, a takaice muna iya cewa rawar da Annabi (s.a.w.a) ya taka wajen kafa tushen al’ummar musulmi ma’abociyar hadin kai ta ginu ne bisa wasu tushe guda uku: kokari wajen kafa al’ummar larabawa ta Musulunci; tsara shirye-shirye na wayar da kai don kafa tsayayyiyar al’umma guda ta musulmi; daga karshe da kuma tabbatar da tsayayyiyar hanya ko kayan aikin tabbatar da hadin kai a tsakanin al’umma.

Idan muka fara da batu na farko za mu ga cewa tun bayan shigowar Annabi (s.a.w.a) garin Madina, ya fara ne da kulla yarjejeniya tsakanin kungiyoyi da kabilu daban-daban wanda ake ganin hakan a matsayin babbar shaidar kokarin tabbatar da hadin kai da aiki tare cikin al’ummar wancan lokacin, don haka ne ma wasu suke ganin irin wadannan yarjejeniyoyi a matsayin kundin tsarin mulki na farko. Don kuwa daya daga cikin abubuwan da suke kawo cikas ga batun hadin kai da aiki tare tsakanin al’umma, shi ne batun kabilanci da yare. Don haka wannan mataki da Ma’aiki (s.a.w.a) ya dauka ya kasance mataki mai cike da hikima wajen samar da hadin kai na kasa da kuma aiki tare na addini. Don kuwa hado kan kabilun da suke rikici a tsakaninsu hakan wani lamari ne da zai lamunce hakkoki na zamantakewa na dukkanin al’ummomi mabambanta da suke wajen, kamar yadda hakan kuma wani lamari ne da zai share fagen kafa wata hukuma da kuma tsari na siyasa na bai daya.

Bayan tabbatar da matakin farko, mataki na biyu kuma shi ne batun hadin kai da aiki tare tsakanin al’ummar musulmi wadanda suka yi imani da abu guda. Don haka ne ma wasu suke kiran wannan hadin kan da sunan hadin kai na imani ko na addini.

Annabi (s.a.w.a) yayi kokari wajen sanya wa musulmin wancan lokacin jin ‘yan’uwantaka da jin cewa lalle su abu guda ne. A don haka ne ma yake cewa: Muminai tamkar rai guda ne. Haka nan kuma yayi kokari wajen tabbatar da hadin kai hatta cikin lamurra na zamantakewa a tsakanin musulmi. A don haka ne ma daga cikin abubuwan da Annabi (s.a.w.a) yayi  a farko-farkon isarsa Madina shi ne kulla ‘yan’uwantaka tsakanin al’ummar musulmi. Inda ya kulla ‘yan’uwantaka ta addini tsakanin kowane mutane biyu a matsayin ‘yan’uwan juna. Wato ya kulla alaka ta ‘yan’uwantaka tsakanin kowane muhajiri (wadanda suka yi hijira zuwa Madina) da kuma Ansar (wato mutanen Madina). Dukkanin wadanda aka hada su tare din suna jin junansu a matsayin ‘yan’uwa tamkar ‘yan’uwa na jini ko ma sama da haka.

Ta haka ne Annabi (s.a.w.a) ya samu nasarar kafa wata al’umma wacce membobinta suka ginu bisa tushe na saukakkun addinai da kuma ‘yan’uwantaka ta koli wadanda a baya babu wanda ya taba tsammanin za a iya samun jituwa da aiki tare a tsakanin irin wadannan al’ummomi da rayuwarsu ta ginu bisa tushe na kabilanci, rarrabuwan kai na addini da dai sauransu. Amma cikin taimakon Allah da kuma irin wannan hikima ta Ma’aiki aka samu damar kafa irin wannan al’ummar, wacce ta ginu bisa wannan tushe na “Muhammadu Manzon Allah ne, wadanda suke tare da shi masu tsanani ne ga kafirai amma kuma masu rahama da tausayi ne a tsakaninsu”. Tushen da ya ginu bisa cewa: Muminai tamkar wani jiki ne wanda idan wani bangare nasa yana ciwo to nan take sauran bangarorin za su kamu da wannan ciwon’.

Daga karshe dai ta hanyar amfani da wannan dama ta ‘yan’uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar, Manzo (s.a.w.a) ya samu damar tabbatar da al’umma guda wacce take ganin kanta a matsayin abu guda, wacce kuma take shirye ta sadaukar da abin da take da shi saboda dan’uwanta.

Dukkanin wadannan wasu abubuwa ne da suke nuna mana irin rawar da Ma’aiki (s.a.w.a) ya taka wajen samarwa da kuma tabbatar da al’umma guda ta Musulunci da kuma aikin da yayi tukuru wajen ganin wannan al’umma ta zama guda wacce ta yi watsi da duk wani abin da zai haifar da rikici da rarrabuwan kai a tsakanin juna.

Don haka nauyin da ke wuyanmu, a matsayinmu na mabiya kuma al’ummarsa, shi ne kiyaye wannan aiki da yayi na tabbatar da al’umma guda.