A+ R A-
01 April 2020

Matsayar Jagora Kan Abin Da Ke Faruwa A Iran Sakamakon Karin Farashin Mai

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi karin bayani dangane da batun karin kudin mai da gwamnatin Iran ta yi da kuma batun fitinar da wasu da suke samun goyon bayan ‘yan kasashen waje suke kokarin tayarwa a Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi wannan karin bayanin ne a safiyar yau a lokacin da yake gabatar da darasin Bahasul Kharij da yake gabatarwa dalibansa.

Abin da ke biye fassarar jawabin da Jagoran yayi ne:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin Talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammad tare da Alayensa tsarkaka sannan la’anar Allah ta tabbata a kan makiyansu gaba daya.

Kafin in fara bahasina, ina so in ce wani abu dangane da abubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau sakamakon matakin da shugabannin bangarori uku na gwamnati suka dauka. A jiya, a daren jiya, a shekaran jiya ‘yan wasu matsaloli sun kunno kai a wasu garuruwan kasar nan, wasu sun rasa rayukansu sannan an lalata wasu wajaje da cibiyoyi; wadannan su ne abubuwan da suka faru cikin kwana daya zuwa biyun nan.

Ya kamata a yi la’akari da ‘yan wasu batutuwa: Na farko, a duk lokacin da shugabannin bangarori uku na gwamnati (shugaban kasa, shugaban majalisa da kuma shugaban bangaren shari’a-alkalin alkalai) suka yanke shawarar kan wani abu, kamata yayi a kalli lamarin da ido na kyakkyawan fata. Ni dai ba kwararre ba ne a wannan bangaren, wato ba na da kwarewa a wannan bangaren, na kuma gaya musu; na ce musu da yake an samu sabanin ra’ayi tsakanin kwararru kan wannan lamari na man fetur, wasu suna ganin wannan mataki ne da wajibi ne ma a dauke shi, wasu kuma suna ganinsa a matsayin wani lamari mai cutarwa. A saboda haka ni a matsayina na wanda ba shi da kwarewa kan wannan lamarin, don haka na gaya musu ba na da ra’ayi kan wannan lamarin, amma matukar dai shugabannin bangarori uku na gwamnatin suka dau matsaya to ni kuwa zan goya musu baya.

Wannan shi ne abin da na ce, kuma zan goya musu baya. Shugabannin bangarori uku ne na gwamnati, suka zauna tare da taimakon wasu kwararru, suka dauki wani mataki don ci gaban kasa. Dole ne a yi aiki da wannan matakin da suka dauka; wannan shi ne batu na farko.

Batu na biyu shi ne cewa ko shakka babu wasu mutane dangane da wannan matakin za su shiga damuwa ko kuma za su yi fushi ko kuma hakan zai cutar da su ko kuma za su yi tunanin cewa zai cutar da su. Koma dai yaya ne ba za su ji dadi ba; to amma sanya wuta a banki kaza, wannan ba aikin mutane ne ba ne, wannan aiki ne na ashararai; aiki ne na ashararan mutane. Wajibi ne a lura da wannan.

A yayin faruwar irin wannan lamarin, a mafi yawan lokuta ashararai, masu bakar aniya da makiya su kan shigo fage. A wasu lokuta ma a kan samu wasu matasa saboda kumaji irin na samartaka sukan shiga cikinsu da kuma aikata irin wadannan danyen ayyukan. Irin wadannan ayyuka kuwa koda wasa ba za su gyara lamurra ba, za ta ma kara shigo da matsalar rashin tsaro ne kan ita kanta wancan matsalar da ake da ita. Rikici da rashin tsaro ita ce musiba mafi girma ga kowace kasa, ga kowace al’umma. To wannan ita ce manufarsu.

Idan kuka duba za ku ga cewa tsawon wadannan kwanaki biyun, wato darare biyu da rana guda, dukkanin cibiyoyin ashararanci na duniya sun yunkura don cutar da mu, suna kwadaitar da irin wadannan ayyukan, kama daga lalatattun iyalan tsohuwar gidan sarautar da aka hambarar ta Pahlawi zuwa ga gungun munafukai lalatattu, suna nan suna ta amfani da kafafen watsa labarai na zamani na sada zumunci da sauran wajaje suna ta kwadaitar da wadannan ashararai su ci gaba da abin da suke yi. Abin da nake son fadi shi ne: bai kamata wani ya taimaka wa wadannan ashararan ba; babu wani mutum mai hankali wanda kuma yake son kasarsa, wanda yake son rayuwa cikin kwanciyar hankali da zai taimaka musu; su din nan ashararai ne, wadannan abubuwan da ake yi ba aiki ne na mutanen gari ba.

Koda yake wajibi ne su ma jami’an gwamnati su sanya ido sosai, nauyi ne a wuyansu, su yi kokari wajen rage duk wata matsala da za ta fuskanci mutane a wannan bangaren. Jiya a talabijin na ga wasu daga cikin jami’an gwamnati sun fito sun ce lalle muna sa ido sosai wajen ganin wannan karin farashin mai bai haifar da tashin farashin kayayyaki ba. To wannan lamari ne mai muhimmanci, don kuwa a halin yanzu akwai tsadar kayayyaki. Idan har aka samu tashin farashin kayayyaki to hakan zai haifar da karin matsaloli ga mutane. Don haka wajibi ne su kula da hakan. Ya kamata su ci gaba da wannan sanya idon.

Haka nan jami’an tsaro ma su yi aikinsu. Haka nan su ma sauran al’ummar gari, wadanda alhamdu lillahi sun yi aiki da hankali da basirarsu yayin faruwar lamurra daban-daban a baya, su gano wadannan abubuwa masu bakanta rai daga ina suka fito. Su gano wannan aiki na sanya wuta, lalata kayayyaki, rikici da fadace-fadace da kuma haifar da rikici da rashin tsaro aikin wane ne, ya kamata su fahimci hakan, don haka su nesanta kansu daga wadannan mutanen. Wannan shi ne kiran da muke musu, haka nan su ma jami’an gwamnati su yi kokarin sauke nauyin da ke wuyansu.

A lokacin da shugabannin bangarori uku na gwamnati suka dau matsaya, to ba batun gwamnati a ke yi ko wata ma’aikatar gwamnati ba, shugabannin bangarori uku na kasa ne suka zauna suka dau wata matsaya, bisa dogaro da wani ra’ayi na masana.

Na dai fadi ni ba kwararre ba ne a kan wannan lamarin, amma a matsayin na mutum na ga jami’an kasa sun dau wani mataki. A zamanin marigayi Imam (yardar Allah ta tabbata a gare shi) ma haka lamarin ya kasance. Jami’ai, shugabannin bangarori uku na gwamnati su kan dau matsaya kan wani aiki sannan kuma a aiwatar da shi. A yanzu ma haka lamarin yake.

Muna fatan, insha Allah, da taimakon mutane da aiki tare tsakanin jami’an gwamnati da masu kishin kasa, da taimakon Allah wannan aikin ma za a aiwatar da shi cikin mafi kyawun yanayi.