A+ R A-
01 April 2020

Imam Khamenei Ya Sha Alwashin 'Ɗaukar Fansa Mai Tsanani' Kan Waɗanda Suka Kashe Janar Qassim Sulaimani

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali  Khamenei, ya bayyana cewar wadanda suka kashe kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran, Janar Qassim Sulaimani su kwana da shirin fuskantar ɗaukar fansan jininsa mai tsanani.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon ta'aziyya da ya fitar a safiyar yau Juma'a (3/1/2020) sakamakon shahadar Janar Sulaimani biyo bayan harin ta'addancin da Amurka ta kai masa a hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Baghdad, babban birnin ƙasar Iraƙi inda ya bayyana Janar Sulaimani a matsayin babban ɗan gwagwarmaya na ƙasa da ƙasa wanda ko shakka babu masoyan gwagwarmaya za su buƙaci ɗaukar fansar jininsa daga wajen waɗanda suka aikata wannan aika-aikan.

Abin da ke biye fassarar wannan saƙo na Jagoran ne:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai

 

Al'ummar Iran masu girma!

Babban kwamandan Musulunci abin alfahari ya koma ga (Mahaliccinsa). A daren jiya ruhin shahidai masu tsarki sun yi maraba da ruhin Qassim Suleimani mai tsarki. Bayan shekaru na jihadi cikin tsarkin niyya da kuma jaruntaka a fagagen gwagwarmaya daban-daban da shaiɗanu da ashararan duniya bugu da ƙari kan shekaru na fatan samun shahada a tafarkin Allah, daga ƙarshe Suleimani abin ƙauna ya kai ga samun wannan matsayi mai girma. Mafi taɓewar mutane sun zubar da jininsa mai tsarki.

Ina miƙa sakon taya murnar wannan shahadar mai girma ga Wanzajjen Allah a bayan ƙasa (Imam Mahdi), rayukanmu su zamanto fansa a gare shi, da kuma ruhinsa (shi Qassim Sulaimani) mai tsarki, haka nan da ta'aziyya ta ga al'ummar Iran.

Shi ɗin nan ya kasance kyakkyawan misali ne na waɗanda suka sami cikakkiyar tarbiyyar Musulunci da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini. Ya gudanar da dukkanin rayuwarsa ne a fagen jihadi saboda Allah. Lalle shahada ita ce kyautar irin wannan ƙoƙari da ƙwazo ba kama hannun yaro da yayi tsawon waɗannan shekaru. Da yardar Allah da kuma taimakonSa tafiyarsa (shahadarsa) ba za ta dakatar da aikinsa da kuma tafarkin da yake kai ba, za su ci gaba da tafiya, to sai dai ɗaukar fansa mai tsanani tana jiran waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki, waɗanda hannayen su ke jiƙe da jininsa da kuma jinin sauran shahidan wannan lamarin dumu-dumu.

Shahid Sulaimani ɗan gwagwarmaya ne na ƙasa da ƙasa, don haka dukkanin masoya gwagwarmaya za su buƙaci ɗaukar fansar jininsa. Wajibi ne dukkanin masoya – haka nan da ma maƙiya – su san cewa tafarkin jihadi da gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa tare da sabon jini a jika, sannan kuma nasara ƙarshe tana jiran masu jihadi bisa wannan tafarki mai cike da albarka.

Ko shakka babu rashin wannan kwamanda mai sadaukarwa kuma abin ƙauna lamari ne mai baƙanta rai, to sai dai ci gaba da gwagwarmaya da kuma samun nasara ta ƙarshe za ta sanya baƙin ciki cikin zukatan waɗannan mashaya jini.

Al'ummar Iran za ta ci gaba da tunawa da kuma girmama ambato da kuma sunan wannan shahidi mai girman matsayi Laftanar Janar Qassem Sulaimani da shahidan da suke tare da shi musamman babban mujahidin Musulunci, Abu Mahdi Al-Mohandis. Don haka ina sanar da kwamani uku na zaman makoki a duk faɗin ƙasar Iran, sannan ina miƙa saƙon taya murna da kuma ta'aziyya ga mai ɗakinsa da 'ya'yansa masu girma da sauran danginsa.

 

Sayyid Ali Khamenei

13/Dey/1398

(03/Janairu/2020)