A+ R A-
01 April 2020

Jagora Imam Khamenei Ya Jagoranci Sallar Mamaci Da Aka Yi Wa Janar Sulaimani Da Abokansa

A safiyar yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci jana’iza da sallar mamaci da aka yi wa marigayi Shahid Janar Ƙasim Sulaimani, Abu Mahdi al-Muhandis  tare da abokansu a masallacin Juma’a da ke Jami’ar birnin Tehran.

Tun da safiyar yau din ne dai miliyoyin al’ummar Iran suka yi tururuwa zuwa jami’ar ta Tehran don halartar sallar jana’izar da za a yi wa wadannan shahidai.

Bayan sallar jana’izar an dauki gawawwakin shahidan daga jami’ar ta Tehran zuwa babban shataletalen Azadi, inda daga nan aka wuce da su zuwa birnin Ƙum mai tsarki, inda a kan ma za a kai su Haramin Sayyida Ma’asuma ‘yar Imam Musa al-Kazim (a.s) daga nan kuma a wuce da gawar Janar Sulaimanin zuwa garin su na Kerman don yi masa salla da kuma bisne shi kamar yadda yayi wasiyya.

Rahotanni dai sun ce kimanin mutane miliyan bakwai ne suka gudanar da jana’iza da kuma rakiyar gawawwakin da aka gudanar a birnin Tehran.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai Shahid Janar Ƙasim Sulaimani, kwamandan rundunar Ƙudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da Abu Mahdi Al-Muhandis, mataimakin shugaban dakarun sa kai na kasar Iraki da ake kira da Hashd al-Sha’abi da wasu da suke tare da su suka yi shahada sakamakon harin da Amurka ta kai musu a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na kasar Iraki.