A+ R A-
25 May 2020

Sabon Makircin Sahyoniyawa Kan Masallacin Kudus

A hakikanin gaskiya ana iya cewa masallacin Al-Aksa (ko kuma Masallacin Kudus kamar yadda aka fi saninsa) shi ne waje na ibada da aka fi zaluntarsa a duniya. Saboda duk da irin muhimmanci da tsarkin da yake da shi a wajen mabiya addini daban-daban na duniya amma yana fuskantar hadarin rugujewa sakamakon ayyukan Allah wadan yahudawan sahyoniya tun lokacin da suka mamaye da sanya shi karkashin kulawarsu a shekarar 1967. Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu yahudawan sun ta kokarin rusa shi ko kuma lalata wani sashi nasa suna masu fakewa da wasu dalilai daban-daban, na baya-bayan nan da suke yi shi ne kokarin da suke yi na rusa katangar gabashin masallacin da suka fara a ranar 6 ga watan Fabrairun nan da muke ciki (2007). Abin da suka fake da shi a wannan karon shi ne gina wata gada da za ta sawwake wa yahudawa isa ga bangaren da suke a Baitul Makdisi kamar yadda suka yi da’awa. Wato a takaice dai suna kokari ne wajen sawwaka wa yahudawa shige da fice a cikin masallacin.

Kamar yadda muka fadi ne a baya cewa ya zuwa yanzu sahyoniyawa sun gudanar da makirce-makirce daban-daban wajen rusa wannan masallaci mai alfarma mafi muhimmanci da ta da hankali shi ne sanya masa wuta da suka yi a shekarar 1969. Tun daga wancan lokacin ya zuwa yanzu haramtacciyar kasar Isra’ila kai tsaye ko kuma ta fakewa da wasu hanyoyi ta aiwatar da makirce-makirce daban-daban da nufi rusa masallacin. Abin tambaya a nan shi ne da wani dalili ne suke yin hakan, ko kuma a ce me suke nema ne a wajen? Abin da yahudawan suke cewa suna yin hakan ne da nufin gano wajen ibadan Annabi Sulaiman (a.s) da suka ce yana kasan masallacin ne, wato an gina masallacin ne a kansa. Yahudawan sun ci gaba da cewa lokacin bayyanar mai cetonsu ya yi, don haka kafin bayyanarsa dole ne su rusa masallacin Al-Aksa da sake gina wajen ibadan Annabi Sulaiman din.

Malaman tarihi sun tabbatar da cewa kimanin shekaru dubu uku da suka wuce ne Annabi Sulaiman (a.s) ya gina wannan wajen ibada, amma bayan kimanin karnoni hudu da gina shi Babilawa suka rusa shi. Sai dai daga baya an sake gina shi, amma kimanin shekaru 70 bayan haihuwar Annabi Isa al-Masihu (a.s) sarkin Rum ya rusa shi. To sai dai duk da hakan, wato batun gina shi wannan wajen ibada da kuma rusa shi, da dama daga cikin malaman tarihi dam asana sun tafi a kan cewa ba a wajen ibadan ne aka gina masallacin Al-Aksan ba, a wani waje ne na daban, don haka batun ruguga masallacin da nemo tushen wajen ibadan bai ma taso ba.  A matsayin misali sannanen masanin ………… bayan gudanar da bincike mai zurfi da kawo ziyara a lokuta daban-daban zuwa masallacin Al-Aksan ya fitar da sakamakon binciken da ya gudanar a watan Satumbar 2004 inda yake cewa: “A hakikanin gaskiya wajen ibadan Sulaiman ba a kasan masallacin Al-Aksa yake ba, don haka labarin cewa yana wajen daya ne daga cikin tatsuniyoyin da sahyoniyawa suka kirkiro don biyan bukatarsu”. Baya ga wannan masani, wasu masanan masun gudanar da nasu binciken inda daga karshe suka tabbatar da gaskiyar abin da wannan masani yake fadi. Kamar yadda har ya zuwa yanzu duk da tone-tonen da suka jima suna yi a masallacin har ya zuwa yanzu sun gagara samo wani abu da ke nuni da cewa wajen ibadan yana kasan masallacin kamar yadda suke da’awa.

Ala kulli hal, yahudawan sahyoniya ta hanyar fakewa da batun neman inda wajen ibadan Annabi Sulaiman din ya ke da sake gina shi, suna ci gaba da kokarin rusa wannan masallaci. Yana da kyau a san cewa ya zuwa yanzu akwai kimanin kungiyoyi 125 na yahudawa ‘yan ta’adda masu tsaurin ra’ayi a yankin Palastinu da aka mamaye ko kuma inda ake kira Isra’ila da yammacin kogin Jordan da suke gudanar da ayyukansu na kokarin rusa masallacin al-Aksa. Daga cikin ayyukan da suke yi har da tona ramummuka a kasan masallacin don raunana tushen ginin masallacin, bude bututun ruwa a kasan masallacin da nufin zaizaye shi da dai sauransu.

Sai dai duk da irin wannan kokarin da yahudawan suke yi na rusa masallacin da shirun da manyan kasashen duniya suka yi musamman Amurka, amma a bangare guda kuma al’ummar musulmi musamman Palastinawan ba su yi shiru sun zuba ido ba duk kuwa da cewa a bangaren gwamnatoci kan ana iya cewa ba a yi abin da ya kamata a yi ba. Ko ba komai dai wannan waje ne da ke da muhimmancin gaske da miliyoyin mabiya saukakkun addinai don haka rusa shi lamari ne da zai tada hankali sosai, baya ga haka ma rusa wannan waje hawan kawara ne ga daya daga cikin muhimman wajajen tarihi. Irin muhimmancin wannan waje ne ya sanya al’ummar Palastinun tsayin daka wajen fuskantar wannan makirci na yahudawa wanda hakan ya yi sanadiyyar shahadar wani adadi mai yawa na Palastinawan da raunana wani adadin. Masana dai suna ganin da ba don tsayin dakan Palastinawan da wasu al’ummomin duniya ba da wata kila masallacin yana cikin wani irin yanayi sama da halin da yake ciki a yanzu. Don haka ne masanan suke ganin daya daga cikin dalilan da ya hana yahudawa rusa wannan waje mai tsarki shi ne irin mayar da martanin da al’ummar musulmi da ma sauran wadanda suke ganin wajen da mutumci musamman abin da suka gani na irin mayar da martanin da Palastinawa suka yi bayan ziyarar tsokanar da tsohon priministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ariel Sharon ya kai masallacin a shekara ta 2000.

Ko ba a fadi ba dai hatsarin da masallacin yake fuskanta a halin yanzu da irin nuna rashin amincewar da al’ummar musulmi suke ci gaba da nunawa ya kara irin nauyin da ke kan gwamnatocin kasashen musulmi musamman na larabawa. Masana lamurran yau da kullum dai suna ganin daya daga cikin dalilan da suke sanya yahudawan ci gaba da wannan kokari da suke yi na rusa masallacin shi ne yakinin da suke da shi cewa babu wani abin da irin wadannan gwamnatoci za su yi musu, wato a takaice dai ko da sun rusa masallacin wadannan shugabanni babu wani abin a zo a gani da za su yi. Saboda tun da jimawa sun fahimci cewa ba abin da shugabanni suke yi a duk lokacin da suka yi wani danyen aiki a kan masallacin in banda kiran taro da yin Allah wadai kawai na fatan baki, amma a aikace kan babu wani abin da suke yi. Ko ba a fadi ba irin wannan matsaya ya taimaka nesa ba kusa wajen share fagen irin abin da yahudawan suke yi. Ko a halin yanzu ma da masallacin ke fuskantar barazana babu wani abin a zo a gani da suka yi in ban da kira ta fatan baki kawai.

Masanan dai suna ganin abu guda kawai da zai kawo karshen irin wannan danyen aiki shi ne hada karfi da karfe tsakanin kasashen musulmi da al’ummominsu wajen fuskantar yahudawan musamman a wannan lokaci da suke ciki tsaka mai wuya su da uwargijiyarsu Amurka bayan da mujahidan Hizbullah suka kwance musu zani a kasuwa, suka kunyata su suka tabbatar wa duniya abin da shugabansu Sayyid Hasan Nasrullah ya taba fadi a baya kuma ya nanata a wannan karon cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta fi gidan gizo gizo rauni. A irin wannan lokaci da musulman suka dawo da mutumcinsu da suka rasa, suka dawo da karfin da suke da shi, suka gano raunin haramtacciyar kasar Isra’ilan da ma mai daure musu gindi Amurka, don haka suna da dukkan karfin da za su iya tsayawa a gaban wadannan shedanu biyu don kwato hakkokinsu.