A+ R A-
25 May 2020

Muhimmancin Palastinu Da Kudus A Mahangar Jagora Imam Khamenei

Muhimmancin Batun Palastinu

 

A bisa bincike, a halin yanzu cikin rayuwar musulmi sannan kuma a duniyar musulmi, babu wani lamari da yake da muhimmanci da kuma irin hatsarin da batun Palastinu yake da shi. Shekara da shekaru kenan a hankali a hankali suka sanya musulmi suka fara sabawa da kwace musu wasu yankuna na gidajensu. Ba wai kawai kwace gidajen musulmi ba ne kawai; face dai lamarin ya wuce haka. Lamarin shi ne cewa makiya al’ummar musulmi da duniyar musulmi sun kwace wasu yankuna ne na gidajen musulmi don su mayar da su garkuwa da kuma inda za su dinga kai musu hari, da rarraba sahun musulmi da kuma fada da abubuwan da suke bukata.

A cikin wannan lamari na Palastinu, manufa ita ce ceto Palastinu; wato kawar da gwamnatin (haramtacciyar kasar) Isra’ila. Babu wani bambanci tsakanin yankunan da aka mamaye kafin shekarar 1967 da wadanda suka biyo bayan hakan. Duk wani wajibi na kasar Palastinu, wajibi ne na gidajen musulmi. Duk wani iko a kan al’ummar Palastinu wanda ba iko ne na al’ummar Palastinu da kuma iko na musulmi a kasar Palastinu ba, to kuwa iko ne na fashi da kwace. Lamarin dai shi ne kamar yadda marigayi Imam Khumaini (r.a) ya fadi ne cewa: “Wajibi ne a kawar da Isra’ila”. Yahudawan da suke Palastinu, idan har za su amince da gwamnatin Musulunci a Palastinu, to suna iya ci gaba da zama a wajen. Lamarin ba wai shi ne adawa da yahudawa ba. Lamarin shi ne kwace gidajen musulmi da aka yi. Shugabanni da mahukuntan kasashen musulmi, idan har ba su kasance karkashin ikon ma’abota karfi na duniya ba, za su iya aiwatar da wannan gagarumin aiki. To sai dai abin bakin cikin shi ne cewa ba su aikata hakan ba.

 

Muhimmancin Baitul Mukaddas

 

A gefen batun Palastinu, ita ma Baitul Mukaddas tana da muhimmanci mai girman gaske. A halin yanzu yahudawan sahyoniya suna ci gaba da gudanar da makirce-makircen kwace wannan gari mai tsarki da kuma kawar da ababe na Musulunci da suke wajen. To sai dai wannan gari na dukkan musulmi ne sannan kuma dukkanin garin Kudus helkwata ce ta dukkan Palastinu, musulmi kuwa ba za su taba bari a aiwatar da abin da makiya suke son aiwatarwa ba, za su yi fada da hakan.

 

Mahangar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Dangane Da Palastinu

 

A Bangare Na ‘Yan’adamtaka: Irin zaluncin da ake yi wa al’ummar Palastinu wani lamari ne da yake dora wa kowane irin mutum nauyi a wuyansa. Irin zaluntar mutanen da suke cikin Palastinu da suke yi yana da yawan gaske, abin mamakin shi ne cewa cibiyoyi da kungiyoyin kare hakkokin bil’adama ma sun mutu! Amurkawa da wadansu daga cikin mutanen kasashen yammaci wadanda suke da’awar yada sakon demokradiya a duniya, sun zubar da mutumcinsu cikin wannan lamari (sakamakon irin shirun da suka yi). Hakan kuwa saboda a halin yanzu akwai wata al’umma wacce ba ta da wani sha’ani da tsoma baki cikin yadda ake gudanar da kasarta, sannan kuma babu wani waje da ake jin sautinsa; wannan al’umma kuwa ita ce al’ummar Palastinu. A mahanga ta ‘yan’adamataka, ga wata al’umma nan wacce ake zalunta; a daya bangaren kuma a gabanta ga wata hukuma nan da ta ginu bisa akidar wariya da kuma irin wannan zalunci da take gudanarwa; a daya bangaren kuma ga irin wannan gagarumar karya wacce Amurka da cibiyoyin kasa da kasa da masanan na kasashen Turai suke yi na kare demokradiyya.

A Bangaren Tsaro: Batun Isra’ila, wani lamari ne da ke cike da barazana ta tsaro ba wai kawai ga al’ummarta ba face ma dai ga dukkanin kasashen yankin nan. Saboda kuwa tana da rumbun makaman kare dangi sannan kuma tana ci gaba da kera irin wadannan makaman. Majalisar Dinkin Duniya a lokuta da dama ta sha jan kunne kan hakan, amma dai ba su ma kula da hakan ba, ko da yake mafi girman dalilin hakan shi ne irin goyon bayan da Amurka take ba ta ne; wato mafi girma da yawan ayyuka da laifuffukan da haramtacciya gwamnatin yahudawa ta ke aikatawa yana wuyan Amurka ne. Tsawon wadannan shekaru gomomi da suka kasance a kan karagar mulki, a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, an fitar da sama da kudururruka talatin a kan haramtacciyar kasar Isra'ila amma dai Amurka ta hau kujeran naki kan dukkanin wadannan kudururruka.

A Bangaren Tattalin Arziki: Isra’ila hatsari ce ga wannan yankin. Yahudawan sahyoniya da suke mulki a kasar Palastinu, sun gabatar da wani shiri da suka ba shi sunan “Sabon yankin gabas ta tsakiya”. Me ake nufi da sabon yankin gabas ta tsakiya? Wato gabas ta tsakiya ta irin yanayin da ya dace da Isra’ila ta yadda a hankali a hankali Isra’ila za ta samu iko kan kasashen larabawa da kasashen wannan yanki da yankunan da suke da arzikin man fetur na Tekun Fasha da samun iko na tattalin arziki. Wannan ita ce manufar Isra’ilawa. Wasu kuwa daga cikin gwamnatoci sun gafala. A lokacin da aka nuna musu hakan su kan ce to ai mu ba mu kulla alaka (da Isra’ila) ba; (abin da muka yi kawai) shi ne ba wa ‘yan kasuwansu dama su zo! To da man hakan shi ne abin da suke so. Suna so ne Isra’ila da irin wannan goyon baya na Amurka da kuma irin makaman kare dangi masu hatsari da take da su, ta yi amfani da gafala da raunin wadansu gwamnatoci don su sami damar kutsowa sannan kuma su kwace dukkanin cibiyoyin tattalin arziki da hanyoyin kudade. Wannan babbar barazana da hatsari ne ga wannan yankin. Wannan shi ne mafi girman hatsari. Kada Allah ya nuna mana wannan rana kuma ba za ta zo ba, sannan kuma al’ummar musulmi ba za su taba bari hakan ta faru ba. To amma dai shirin su shi ne cewa ta hanyar dogaro da makamin tattalin arziki za su sami damar kwace duk wasu cibiyoyi na karfi na wadannan kasashe.

A saboda haka, a bangare na Musulunci, a bangare na ‘yan’adamataka, a bangare na tattalin arziki, a bangare na tsaro, a bangare na siyasa, a yau samuwar Isra’ila, babban hatsari ne ga al’ummomi da kasashen wannan yankin.

 

Imam Khumaini (r.a) Da Batun Palastinu

 

Imam Khumaini (r.a), tun farkon kaddamar da wannan gwagwarmaya ta Musulunci a shekarar 1341 (hijira shamsiyya) a wancan lokacin batun Palastinu a Iran hatta a wajen masana da zababbun mutane ba a ma sanshi ba, maganar Imam ita ce cewa wajibi ne a ji cewa akwai hatsari cikin ikon da Isra’ila take da shi (a wannan yankin); wajibi ne a tsaya kyam a gaban hakan kuma a yi fada da shi. Daga nan kuma haka ya ci gaba, hakan kuwa ya kasance daya daga cikin manyan taken wannan babban bawan Allah. Yunkurin marigayi Imam Khumaini (yardar Allah ta tabbata a gare shi) ne ya sanya sabon rai cikin zuciyar lamarin Palastinu sannan kuma ya samar masa da kariya ta imani na Musulunci wanda a koda yaushe yake tare da jihadi da sadaukarwa. Babu wani lokaci da marigayi Imam Khumaini ya taba janye hannayensa daga ba da kariya ga al’ummar Palastinu saboda la’akari da masu amfani da karfi na duniya. Shi din nan tsawon tarihi ya kasance yana gabatar da batun Palastinu a matsayin lamari na asali. Imam cikin wasiyyarsa ta karshe da kuma cikin jawabansa ya kasance mai ba da tsananin muhimmanci ga kiran da al’ummomin da aka zalunta suke yi na neman taimako. Ya kasance mai bayyanar da goyon baya a fili ga hakkokin wadanda aka zalunta, kariya ga hakkokin al’ummar Palastinu da dukkanin al’ummomin da ake zalunta a fili. Wannan shi ne salo da kuma tafarkin Imam; wannan shi ne hanyar Imam da wasicci da kuma wasiyyar Imam.

Wani matashi musulmi Bapalastine yana cewa: A yau a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra'ila, fursunoni suna rera taken nuna kauna ga Imam da kuma tunawa da babban jagoran juyin juya halin Musulunci. A cikin dakunan gidajen yarin ana ganin irin ambato mai kyau da ake yi ga juyin juya halin Musulunci da Imam da kuma irin tsayin daka da gwagwarmayar al’ummar Iran.