A+ R A-
25 May 2020

Sayyid Nasrallah: Mu ‘Yan Shi’an Ali (a.s) Ba Za Mu Taba Yin Watsi Da Palastinu Ba

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana haramtacciyar kasar Israila a matsayin babbar barazana ga kasashen musulmi wanda kawar da ita maslaha ce ga dukkanin wadannan kasashen kamar yadda ya jaddada cewa ‘yan Shi’an duniya ba za su taba yin watsi da matsalar Palastinu ba.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron Ranar Qudus Ta Duniya da kungiyar Hizbullah din ta gudanar a birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon inda ya ce haramtacciyar kasar Isra’ila dai wata cutar kansa ce (kamar yadda marigayi Imam Khumaini ya bayyana ta) wadda kawar da ita ita ce hanya guda kawai ta magance wannan cutar.

Sayyid Hasan Nasrallah ya ci gaba da cewa: Isra’ila wacce take a matsayin hanyar cimma bakar aniya da siyasar sahyoniyanci a yankin nan, babbar hatsari ce ta koda yaushe, ba wai kawai a kan Palastinu ba, face dai hatsari da kuma barazana ce ga dukkanin kasashen yankin Gabas ta tsakiya.

Shugaban kungiyar Hizbullah din ya ci gaba da cewa manufar marigayi Imam Khumaini (r.a) ta ware Juma’ar karshe ta watan Ramalana a matsayin Ranar Qudus ta duniya ita ce tunatar da musulmi da duniya baki daya batun Qudus don kada a mance da shi. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne a san cewa wannan Palastinun da muke magana ita ce dukkanin Palastinu, ba wai wani bangare nata ba, sannan kuma wajibi ne a dawo da ita gaba dayanta ga al’ummar Palastinu. Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Babu wani a duniyar nan, sarki ne shi ko shugaban kasa ko kuma gwamnati da take da hakkin yin watsi ko kuma yin sassauci kan mita guda na kashin kasar Palastinu.

 

Yaki Da Bakar Farfaganda Kan Iran Da Shi’a

 

A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Hasan Nasrallah yayi ishara da kokari da shirin da wasu kasashen larabawa bisa goyon bayan Amurka suka kaddama na yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma ‘yan Shi’an duniya da sunan fada da ‘barazanar Iran’ allhali sun yi watsi da batun Palastinu da kuma batun adawa da Isra’ila, yana mai cewa da a ce sun kashe rabin abin da suke kashewa wajen fada da Iran a kan batun Palastinu, da kuwa an ‘yanto Palastinu daga mamayan yahudawa ‘yan share guri zauna.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Sun shirya sojoji don fada da Iran, maimakon fada da Isra’ila.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Bayan da wannan makirci na su na ‘barazanar Iran’ ya sha kashi, sai kuma suka sake kirkiro wani abin na daban da sunan ‘Yaduwar Shi’anci’ da kuma amfani da wasu mutane don cimma wannan manufa.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Wasu mutanen, ba sa ganin Isra’ila a matsayin abokiyar gaba sannan kuma babbar barazana saboda a halin yanzu an kirkiro musu wani makiyin na daban. Shugaban kungiyar Hizbullah din ya ci gaba da cewa: Duk wanda ya kirkiro da kuma goyon bayan kungiyoyi masu kafirta musulmi a duniyar musulmi, to yana hidima ne wa Isra’ila sannan kuma shi ne yake da alhakin dukkanin zubar da jini da hasarar da ke faruwa a duniyar musulmi a halin yanzu.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: A halin yanzu wasu mutane (da gwamnatoci) suna ci gaba kokarin haifar da fitina ta mazhaba da yaki da Shi’anci a tashohin talabijin da sauran kafafen watsa labarai da kuma hanyar sadarwa ta internet, kamar yadda kuma wadannan mutanen suke ta kokarin tunzura wasu ‘yan Shi’an wajen fada da ‘yan Sunna. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Babbar manufar masu tada fitina tsakanin Shi’a da Sunna ita ce don a mance da batun Palastinu da kuma kyamar duk wani abin da ke da alaka da Palastinu.

 

‘Yan Shi’an Ali, Ba Za Su Yi Watsi Da Palastinu Ba

 

Don haka sai Sayyid Hasan Nasrallah ya jaddada aniyar ‘yan Shi’an duniya da kuma kungiyarsa ta Hizbullah da ci gaba da riko da tafarkin ‘yanto Palastinu daga hannun yahudawa ‘yan share guri zauna da cewa: Ku kira mu ‘Rafidha’, ku kira mu da masu laifi, ku fadi duk abin da kuke son fadi, haka nan ku kashe mu duk yadda kuke so, lalle mu ‘yan Shi’an Aliyu bn Abi Talib (a.s) ba za mu taba yin watsi da Palastinu ba. A ranar Qudus, ina sanar da dukkanin makiya da masoya cewa: Mu ‘yan Shi’an Aliyu bn Abi Talib (a.s) a duniya ba za mu taba yin watsi da Palastinu, da Qudus da kuma matsalar Palastinu ba.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa kungiyar Hizbullah za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Palastinu da kuma dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya na Palastinu.

Daga karshe dai Sayyid Nasrallah ya gode wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kasar Siriya saboda irin goyon bayan da suke ba wa kungiyoyin gwagwarmaya na kasashen musulmi masu fada da mamaya da kuma bakar aniyar yahudawan sahyoniya.