A+ R A-
23 July 2019

Goyon Bayan Palastinu A Mahangar Jagora Imam Khamenei

Goyon Bayan Palastinu Ta Bakin Jagora Imam  Khamenei

 

Sakamakon Rarrabuwa Cikin Al’ummar Musulmi

 

Idan da a ce a yau musulmi suna da hadin kai sannan idan da a ce sun dogara da ruhi na Musulunci, to da makiya ba su sami damar irin wannan cin mutumci a fili da suke yi wa al’ummar Palastinu da shiga gidajensu da irin wadannan azabtarwa da matsin lamba da suke yi musu ba. Matsalar Palastinu tana sanya zuciyar duk wani mutum mai lamiri – ko da kuwa bai kasance mai riko da addini sosai ba – tana zubar da jini da kuma kawar masa da kwanciyar hankali.

 

Nauyin Ba Da Kariya Ga Al’ummar Palastinu

 

Ba da kariya ga al’umma Palastinu da ake zalunta da kuma irin tsayuwar daka da yunkurin da suka yi cikin jaruntaka, wani nauyi ne na Musulunci a kan wuyan dukkaninmu. A yau din nan wata al’umma ce ta musulmi da a ke zalunta take tsaye a fage tana bukatar taimako daga wajen al’umma musulmi. Ni dai ba zan taba mancewa da sautin wata mace Bapalastiniya wacce ta tsaya a gaban kamarar wani dan jarida da dusassen sautinta tana fadin cewa: “Ya al’ummar musulmi ku kawo mana dauki ….” ba.

Wajibi ne dukkanin musulmi da larabawa su goyi bayan halalcin gwagwarmayar da al’ummar Palastinu suke yi. Wajibi ne wannan lamari ya zamanto abin nuna wa goyon baya a kungiyoyi na kasa da kasa na cewa dukkanin wata al’umma maras kariya da aka kwace mata hakkinta karkashin mamaya, tana da hakkin ta yi gwagwarmaya wajen kwato hakkinta. A saboda haka ci gaba da gwagwarmayar Intifada da gwagwarmayar al’ummar Palastinu wani halaltaccen hakkin ne da suke da shi sannan kuma a bisa dokokin kasa da kasa hakan wani lamari ne abin girmamawa. Duk kuwa da cewa abin bakin cikin shi ne cewa wadannan dokoki ana ba su fassara ne gwargwadon yadda za su yi daidai da bukatun ma’abota girman kan duniya.

Al’ummar musulmi dai, bai kamata su ci gaba da zuba ido suna ganin ana ci gaba da zaluntar al’ummar Palastinu ba. Wajibi ne su fahimtar da haramtacciyar kasar Isra'ila cewa ci gaba da zaluntar al’ummar Palastinu da kuma yankunan da Palastinawa suke zaune lamari ne da zai fuskanci gagarumin mai da martanin dukkanin al’ummar larabawa da al’ummar musulmi.

 

Duniyar Musulmi Da Batun Palastinu

 

Goyon Bayan Duniyar Musulmi Ga Palastinu

 

Batun Palastinu, batu ne na farko na duniyar musulmi a fage na kasa da kasa. Shekara da shekaru kenan a hankali a hankali suka sanya musulmi suka fara sabawa da kwace musu wasu yankuna na gidajensu. Ba wai kwace gidajen musulmi ba ne kawai; face dai lamarin ya wuce haka. Lamarin shi ne cewa makiya al’ummar musulmi da duniyar musulmi sun kwace wasu yankuna ne na gidajen musulmi don su mayar da su garkuwa da kuma inda za su dinga kai musu hari, da rarraba sahun musulmi da kuma fada da abubuwan da suke bukata.

A nan magana ce kan matsaloli, tilasta gudun hijira da zaluncin da ake yi wa wata al’umma; magana ce kan kwace wata kasa; magana ce kan samar da wata cutar kansa a tsakiyar zuciyar kasashen musulmi da kuma yankin da ya hada gabashi da yammaci duniyar musulmi; a nan magance ce kan zaluncin da ake ci gaba da yi da ya zuwa yanzu ya lankwame wata zuriya guda biyu ta al’ummar Palastinu. A yau da aka tabbatar da wannan yunkuri na Musulunci wanda ya dogara da tsayin dakan al’umma a kasar Palastinu, hakan ya zamanto babbar barazana ga ‘yan mamaya marasa lamiri wadanda ba su san wani abu ‘(mai suna) yan’adamataka ba. A yau salon da makiya suke dauka ya fi zama mai rikitarwa da kuma jan kunnen da wajibi ne dukkanin musulmi a duk inda suke a fadin duniyar nan su dau lamarin da dukkanin muhimmanci sama da lokacin baya sannan kuma su yi tunani da kuma aiki saboda hakan. Asasin kafa gwamnatin yahudawa – ko kuma da ma’anar da ta fi dacewa, gwamnatin yahudawan sahyoniya – a wannan yanki na duniyar musulmi, yana da wata babbar manufa ta nan gaba a wajen ma’abota girman kai. Alal hakika samar da wannan gwamnati a wannan yanki mai matukar muhimmanci wanda ana iya cewa zuciya ce ta duniyar musulmi – wato bangaren yammacin duniyar musulmi wanda yake shi ne nahiyar Afirka, zuwa ga bangaren gabashin duniyar musulmi wanda shi ne dai wannan yanki na gabas ta tsakiya da Asiya da gabashi wanda shi ne ya ke hada su wanda kuma ya kasance wata mararraba ce mai hanyoyi uku tsakanin nahiyoyin Asiya, Afirka da Turai - saboda wannan manufa ce ta cewa a shekaru masu zuwa ma wannan mulkin mallaman ‘yan mulkin mallaka na wancan lokacin - wanda gwamnatin Ingila ce take kan gaba – ya ci gaba da zama a duniyar musulmi.

Ingantaccen tafarkin fada da wannan hukuma ta ‘yan fashi shi ne dai wannan tafarki da a yau al’ummar Palastinu suka gano kuma suka rika sannan kuma suka sanya karfafan kafafunsu a wajen, nauyin da ke wuyan dukkanin musulmi shi ne su taimaka musu a wannan tafarkin. A yau babu yadda za a iya amincewa da irin halin ko in kulan da gwamnatocin musulmi suke nunawa batun Palastinu. Gwamnatin kwace (yahudawan sahyoniya), ta kai matsayi na koli na zalunci da amfani da karfi, sannan kuma sun tabbatar da cewa a shirye suke su aikata duk wani mummunan aiki na ta’addanci saboda cimma wannan manufa ta su ta mamaya mai tsananin hatsari. Yunkuri na Musulunci da al’ummar Palastinu suka yi har ila yau ya tabbatar wa dukkaninmu hujja sannan kuma yana nuni da cewa duk da irin matsin lamba da zaluncin makiya masu zubar da jini da kuma ha’incin masu da’awar abokantaka, an riga da an dasa bishiyar gwagwarmaya kai face ma dai ta riga da ta yi saiyoyi da kuma kafuwa. A saboda haka wajibi ne a kan dukkanin al’ummomi da dukkanin gwamnatoci su sanya lamarin Palastinu a matsayin wani lamari na farko a gabansu sannan kuma gwargwadon karfinsu su taimaka masa.

Babu wani bambanci tsakanin mazhabobin Musulunci sannan kuma dukkanin (malaman) fikihun (mazhabobin Musulunci) sun tafi kan cewa matukar dai makiya suka kwace wani yanki daga cikin yankunan musulmi sannan kuma suka tabbatar da ikonsu a wannan yankin, to wajibi ne dukkanin al’ummar musulmi su yi dukkanin abin da za su iya wajen dawo da wannan yanki zuwa ga ikon musulmi.

Al’ummar Palastinu – wadanda a yau idanuwan duniyar musulmi sun koma gare su ne – su san cewa zukatan al’ummar musulmi suna musu kyakkyawan kallo sannan kuma suna yi musu addu’oi; idan da a ce kofofi a bude suke wajen taimaka musu, da al’ummar musulmi sun ci gaba da kai musu taimako; ko da gwamnatoci sun amince ko kuma ba su amince ba. Al’ummar musulmi ba za su taba barin Palastinu ba, ba za su taba kawar da idanuwansu daga kan al’ummar Palastinu ba, sannan kuma ba za su taba kawar da idanuwasu daga kan matasan Palastinu ba.

 

Goyon Bayan Gwamnatocin Musulmi Ga Palastinu

 

Fatan da ake da shi daga wajen gwamnatocin musulmi shi ne su samar da dukkanin damar da ake da ita wajen ba da kariya ga al’ummar Palsatinu, kamar kuma yadda ake fatan ganin an matsa wa dukkanin mutanen da suke ba da kariya da kuma goyon baya ga manuofin yahudawan sahyoniya a duniya lamba. Ana iya yin wannan aiki kuwa cikin alaka ta bangarori biyu, cikin cibiyoyi na kasa da kasa, cikin maganganu na jama’a da kuma tattaunawa ta musamman da ake yi a bayan fage. To idan kuma har mai kai hari da mai adawar suka zamanto ba a shirye suke su yi watsi da irin wadannan danyen aiki da suke aikata wa ba, to al’ummar Palastinu – wadanda gaskiya tana tare da su sannan kuma za su ci gaba da kare kansu – wajibi ne su sami damar da za su iya kare kansu.

 

Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Al’ummar Palastinu

 

Al’ummar Iran kamar kullum kuma a ko da yaushe ta kasance mai ba da kariya da goyon bayan al’ummomi da ma’abota girman kan duniya suke zalunta ne sannan kuma za ta ci gaba da zama hakan. Al’ummar Iran a ko da yaushe ta kasance a gefen al’ummar musulmi, ‘yar gwagwarmaya kuma madaukakiyar al’ummar Palastinu wajen fuskantar sahyoniyawa ‘yan ta’adda kuma za ta ci gaba da zama hakan. Tana kiran ‘yan’uwansu Palastinawa da su ci gaba da riko da wannan tafarki na Ubangiji – wato tafarkin gwagwarmaya da makiya ‘yan mamaya da masu goya musu baya – ta hanyar dogaro da Allah da yarda da shi har a kawo karshen gwamnatin sahyoniyawa. Al’ummar Iran masu girma da imani da kuma gwagwarmaya tana daukan goyon bayan al’ummar Palastinu a matsayin wata farilla ta addini sannan kuma suna ganin a bisa tafarkin Allah babu wata manufar da ba za a iya cimma wa ba.

Amfani Da Wayar Da Kai Wajen Goyon Bayan Palastinu

 

Bayan yakin duniya na biyu, yahudawa a duk fadin duniya sun shirya daruruwa kai dubban fina-finai don nuna (wa al’ummomin duniya cewa) yahudawa mutane ne da aka zalunta sannan kuma mutane da suke fada da su – a hakika ne ko kuma ba haka ba – a matsayin azzalumai. Irin zaluncin da ake yi wa al’ummar Palastinu a yau, ba a taba yin irin sa wa wata al’umma ba; sai dai abin bakin cikin shi ne cewa al’ummomin duniya ba su san irin wannan zaluncin ba. Wajibi ne a yi bayanin hakan da kyau. Wajibi ne a shirya fina-finai, wajibi ne a gudanar da ayyuka na fasaha don dukkanin al’ummomin duniya su san me ya faru.