A+ R A-
23 July 2019

Mahangar Imam Khamenei Kan Hanyoyin Magance Matsalar Palastinu

Magance Matsalar Palastinu Ta Hanyar Diplomasiyya

 

Don a magance wannan matsala mai girma ta Palastinu a ko da yaushe ana gabatar da hanyoyi guda biyu: na farko hanyar da take cike da kuskure, wata hanyar kumaita ce ingantacciyar hanya (da za ta iya magance matsalar). Karkatacciyar hanyar ita ce a tattauna da wadannan ‘yan mamaya wadanda ba sa girmama koyarwa ta ‘yan’adamtaka ko kuma dokokin kasa da kasa ko kuma kudurin Majalisar Dinkin Duniya sannan kuma a cimma wata yarjejeniya da su. Wannan hanya dai ta kowace fuska ta tabbatar da cewa kuskure ne. Don kuwa haramtacciyar kasar Isra'ila ta tabbtar da cewa ba ruwanta da duk wata yarjejeniya da ta sanya mata hannu; ko da sun cimma yarjejeniya, ko da ma sun sanya hannu kanta, to ba za su ci gaba da girmama wannan yarjejeniyar ba. Wannan hanya wacce za a sanya wa mai wuce gona da irin zuma a bakinsa don a samu damar rufe bakinsa a ci gaba zuwa mataki na gaba, ba hanya ce da za ta magance matsalar ba. Al’ummar Palastinu dai sun gwada hakan na tsawon shekaru sittin sun gani. An fitar da kudururruka a Majalisar Dinkin Duniya, a zahiri ma Amurka, wacce take goyon bayan wadannan ‘yan mamaya ido rufe, ta sanya hannu kan wannan kudurin, amma wadannan ‘yan fashin kasa ba su yi aiki da shi ba.

Hanyar magane matsalar wacce ta yi daidai da hankali sannan kuma dukkanin masu farkakken lamiri na duniya da kuma dukkanin mutanen da suka yarda da ma’anonin na wannan duniya wajibi ne su yarda da ita ita ce hanyar gudanar da kuri’ar jin ra’ayin dukkanin al’ummar Palastinu; dukkanin mutanen da aka tilasta musu gudun hijira daga Palastinu; ko da yake wadanda suke son dawowa kasar Palastinu da kuma gidajensu. Wannan wani lamari ne da ya dace da hankali. Wadannan mutane da suke (gudun hijira) a Labanon da Jordan da Kuwait da Masar da sauran kasashen larabawa, su koma gidajensu da kasar su ta Palastinu sannan kuma dukkanin mutanen da suke Palastinun kafin shekarar 1948 wacce ita ce shekarar da aka kafa wannan haramtacciyar gwamnati ta Isra’ila – musulman cikinsu ne ko kuma kiristocinsu ko kuma yahudawansu – a ji ra’ayinsu. A gudanar da kuri’ar jin ra’ayinsu gaba daya su zabi irin gwamnatin da suke so ta yi mulki a kasar Palastinu. Wannan ita ce demokradiyya. Da wani dalili ne za a ce tsarin demokradiyya abu ne mai kyau ga kowa da kowa, amma demokradiyya ba tsari ne mai kyau ba ga al’ummar Palastinu? Da wani dalili ne ya sanya dukkanin al’ummomin duniya suna da hakkin tsoma bakinsu cikin yadda makomarsu za ta kasance, amma al’ummar Palastinu su ba su da wannan hakkin?

Babu wani wanda yake shakkan cewa wannan gwamnati da a yau take mulki a Palastinu, gwamnati ce wacce aka kafa ta bisa amfani da karfi, yaudara da matsin lamba. Babu wani wanda yake shakkan hakan. Yahudawan sahyoniya ba su zo cikin ruwan sanyi ba; ta wani bangaren sun zo ne ta hanyar yaudara ta wani bangaren kuma ta hanyar amfani da makami da matsin lamba; a saboda haka suna da wata gwamnati ce da aka tilasta musu ita. Al’ummar Palastinu su taru, su ba da ra’ayinsu sannan kuma su zabi irin gwamnatin da suke son ta yi mulki a wannan kasar. Sai a kafa wannan gwamnati, sannan kuma ta dau matsayar da ta ga ya dace dangane da mutanen da suka zo wajen tun daga shekarar 1948. Idan har ta yanke shawarar su ci gaba da zama a wajen, to su ci gaba da zama, idan kuma ta yanke shawarar su tafi, to sai su tafi. Wannan dai ra’ayin al’umma ne, kuma hakan demokradiyya ce kuma hakkokin bil’adama, sannan kuma abu ne da ya dace da hankali da hikima ta wannan duniyar.

 

Matsa Wa Gwamnatin Sahyoniyawa Lamba

 

Dan mamaya dai cikin ruwan sanyi ba zai amince da wannan hanya ta magance matsalar da ta dace da hankali ba! To a nan ne ya zamanto wajibi dukkanin wadanda abin ya shafa su ji cewa lalle suna da wani nauyi a wuyansu; shin gwamnatocin larabawa ne ko kuma gwamnatocin kasashen musulmi da kuma al’ummomin musulmi a duk inda suke a duniya musamman ma dai al’ummar Palastinu da kuma cibiyoyin kasa da kasa. Kowane guda daga cikinsu yana da wani nauyi a wuyansa wajen ganin ya matsa kaimi wajen ganin an tabbatar da wannan hanya da ta yi daidai da hankali sannan kuma ana iya cimma hakan. Bai kamata wasu su ce ai wannan wani mafarki ne kawai, abu ne da ba zai yiyu ba; a’a, abu ne mai yiyuwa. Kasashen kogin Baltik wadanda bayan gushewar shekaru arba’in da wani abu suna a matsayin wani bangare na tsohuwar tarayayyar Sobiyeti, daga baya sun dawo da baya sun sami ‘yancinsu. Haka nan kasashen yankin Kabkaziyya sama da shekaru dari kafin a kafa tarayyar Sobiyetin sun kasance ne karkashin ikon Rasha, daga baya sun zo sun sami ‘yancinsu. A halin yanzu kasashen Kazakistan, Azarbaijan da Jojiya da sauransu duk sun sami ‘yanci; su da kansu ne. A saboda haka wannan lamari mai yiyuwa ne. To sai dai hakan yana bukatar irada, azama da jaruntaka. Jarumar al’umma ba ta tsoro kuma a shirye take. A saboda haka, gwamnatoci suna da nauyi a wuyansu a wannan fagen; musamman kuwa gwamnatocin larabawa. A yau gwamnatocin kasashen larabawa suna iya fitowa fili sannan kuma su sami irin kauna da goyon bayan al’ummominsu cikin lamarin da ya shafi Palastinu. Matukar wata gwamnati da wata hukuma ta samu goyon bayan al’ummominta, to kuwa Amurka ba za ta iya cutar da ita ba, sannan kuma ba za ta sake jin tsoron Amurka ba, daga nan kuma ba zai zama dole sai ta dinga lura da Amurka ba.

 

Amfani Da Makamin Man Fetur

 

Daga cikin ayyuka masu muhimmanci da gwamnatocin larabawa za su iya yi shi ne cewa kasashen da suke fitar da man fetur su yi amfani da man fetur din. Wadannan maganganu da ‘yan kasashen yammaci suke ta yi kan kada su yi amfani da makamin man fetur, ba magana ce da ta dace ba. Man fetur mallaka ce ta al’ummomi don haka wajibi ne su yi amfani da shi kan abin da zai samar musu da riba. Kasar Amurka ta yi amfani da alkama da sauran kayayyakin abinci a matsayin makami; sannan kuma tana amfani da hakan a wajaje da yawa na duniya. Da wani dalilin ne ya sanya kasashen musulmi da na yammaci ba su da hakkin su yi amfani da hakan? Kawai su dakatar da sayar da man fetur ga dukkanin kasashen da suke da kyakkyawar alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila na wata guda a matsayin wata alama ta nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu. A yau kasashen duniya sun dogara ne da man fetur din kasashen musulmi wajen ayyukansu da masana’antu da samar da makamashi da wuta, wadanda wasu rukunai uku ne na rayuwa. Matukar aka hana su man fetur, to kuwa ayyukan masana’antu da samar da wutansu za su tsaya cak.

 

Taimakon Kudi Ga Al’ummar Palastinu

 

Taimakon kudi ga Palastinawa, ba lamari ne kawai da ya dora kan wuyan gwamnatoci ba ballanatana ma wata gwamnatin ta ce: “Ai ni na ba dala miliyan goma, dala miliyan ashirin, dala miliyan hamsin” ba a ma san a ina ta bayar da wadannan kudaden ba, ta wace hanya ce ta bayar, ga waye ta bayar ba. A yau al’ummar Palastinu tana bukatar abinci ne, tana bukatar magani ne. Al’ummar Palastinu ba aljamirai masu bara ba ne, madaukaka ne, to amma suna karkashin ikon makiya ne. Wajibi ne kowa da kowa ya taimaka musu. Ku dauka cewa idan da a dukkanin kasashen musulmi – a kasar Iran da sauran kasashe – kowane mutum daga cikin mutanen wannan kasar zai ba da taimakon Tuman (sunan kudin Iran ne) dubu kawai ga Palastinu, ku ga mai zai faru. Tuman biliyan dubu wani irin tasiri ne zai yi cikin al’ummar Palastinu da rayuwar al’ummar Palastinu. A samar musu da abinci, magunguna, da dukkanin abubuwan da suke bukata wajen ci gaba da tsayin daka da kuma aika musu su.