A+ R A-
23 July 2019

Imam Khamenei: Gwagwarmaya, Tafarkin Ceto Al’ummar Palastinu

Hanyar Ceto Palastinu

 

Abubuwan da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa ta aikata ga al’ummar Palastinu cikin wadannan shekaru, ya isa ya tabbatar da cewa babu wani fata da ake da shi na ‘yanto al’ummar Palastinu (daga mummunan yanayin da suke ciki) ta hanyar dogaro da manyan masu karfi na duniya da wadanda suka dogara da su a wannan yankin. Juyin juya halin Musulunci mai girma na Iran, ya tabbatar da cewa mabudin magance wannan matsala mai girma su ne su kansu al’ummar Palastinun da kuma iradar mutane ta yadda idan aka dogara ga Allah da kuma alkawarin Ubangiji da kuma yin tunani to kuwa za a iya yin galaba a kan masu karfin da suka doru a kan al’umma. A yau sakamakon abubuwa da dama da suka faru a duniya to kuwa irin gudumma da rawar da mutane suke iya takawa ta sake fitowa fili. Dangane da batun fuskantar mashaya jini yahduawan sahyoniya masu mamayan Palastinu, iradar al’ummar Palastinu ce kawai za ta iya tsayawa kyam sannan kuma ta hanyar gwagwarmaya cikin jaruntaka za ta tilasta wa makiyi ja da baya da kuma amincewa da shan kashi. Bai kamata al’ummar Palastinu su nemi ‘yanci da hakkokinsu cikin tarurrukan da shugabannin kasashen larabawa suke gudanarwa ba. Saboda irin wadannan tarurruka idan ma dai ba an gudanar da su ne wajen cutar da al’ummar Palastinun da ake zalunta ba, ko kuwa alal akalla lamari ne da ba shi da wata fa’ida (a gare su).

 

Gwagwarmaya, Tafarkin Ceto Al’ummar Palastinu

 

Ba za a taba ‘yanto Palastinu ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya ko kuma ta hannun manyan kasashe masu karfi na duniya ko kuma ta hanyar gwamnatin ‘yan mamaya ba; hanyar ceto da ‘yanto Palastinu ita ce kawai hanyar tsayin daka da gwagwarmaya, ta hanyar hadin kan Palastinawa da kuma hadin kai da aiki kafada da kafada cikin yunkuri na jihadi.

Rukunan wannan gwagwarmaya, a wani bangaren su ne kungiyoyin jihadi na Palastinu da dukkanin al’ummar Palastinu ma’abota imani da gwagwarmaya da suke ciki da wajen Palastinun. A bangare na daban kuwa, gwamnatoci da al’ummomin musulmi a duk fadin duniya, musamman malaman addini, masana da ‘yan siyasa da ‘yan jami’a, matukar wadannan rukunai guda biyu suka tsaya kyam a inda suke, ko shakka babu farkakkun lamiri da zukata da tunanin da ba su gurbata daga farfagandar ‘yan mulkin mallaka na watsa labaran ma’abota girman kai da yahudawan sahyoniya ba, a duk inda suke a duniya za su tsaya wajen taimakon masu hakki da wadanda ake zalunta, sannan kuma za su tilasta wa cibiyoyin girman kai na duniya wajen su mika kai ga irin wannan gagarumin yunkuri.

Gwagwarmaya da hakurin mujahidai da al’ummar Palastinu da goyon baya da taimako ta dukkan bangarori a gare su daga dukkanin kasashen musulmi za su iya kawar da zaluncin ‘yan mamayan Palastinu. Karfi mai girman gaske na al’ummar musulmi zai iya kawar da matsalolin duniyar musulmi ciki kuwa har da matsalar Palastinu.

 

Farkawar Al’ummar Palastinu

 

Abin farin cikin shi ne cewa farkawa ta Musulunci ta al’ummar Palastinu, ya zuwa wani haddi mai girma ta haskaka yanayi na nan gaba. A yau zuriyar al’ummar Palastinu, suna gwagwarmaya ne, alhali suna masu riko da sunan Allah da kuma imani na Musulunci, wannan gwagwarmaya kwa lamari ne mai tsananin sanya fata cikin zuciya kamar yadda ake gani. Makiya – shin mahukuntan sahyoniyawa ne ko kuma Amurkawa da sauran masu goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila ko kuma ha’inan (shugabannin) wannan yanki – suna tsananin fushi sannan kuma suna bin kowace irin hanya da za su iya bi wajen ganin sun kawar da wannan gwagwarmaya daga asalin tafarkin da take kai. Amma addini, shi ne abin da zai ceto al’umma Palastinu. Musulunci shi ne zai kwato Palastinu daga hannun masu wuce gona da iri.

Sabbin zuriyar Palastinu sun fahimci wannan hakika cewa matukar suna son su tsira daga irin wannan wulakanci da matsin lamba da ake musu, to hanyar hakan ita ce gwagwarmaya da yunkurawa; hanyar hakan ba ita ce zama a teburin tattaunawa ba, su kansu masu tattaunawar babu wani abin da za su samu.

 

 ‘Yan Kasanci Na Larabci Da Batun Palastinu

 

A wani lokaci a kan ji wasu mutane suna fadin cewa: Palastinu wani lamari ne na larabawa. Da wata manufa ake yi irin wannan maganar? Idan har manufar hakan ita ce cewa don su sami shu’uri da kuma son yin hidima da kuma kara yin gwagwarmaya, to hakan lamari ne abin yarda da kuma karbuwa. Amma idan har ma’anar wannan magana ita ce cewa shugabannin wasu daga cikin kasashen larabawa su nuna halin ko in kula da kiran neman taimako da al’ummar Palastinu suke yi sannan kuma su hada baki da makiya da masu fashin kasa cikin lamari mai muhimmanci na irin danyen aikin da aka aikata a Gaza sannan kuma su dinga daga murya a kan mutanen da suke ganin (taimakon Palastinun) a matsayin wani nauyi da ke wuyansu sannan hankalinsu ba ya kwanciya, suna masu cewa da wani dalili ne ya sanya kuke ba da taimako wa Gaza, to kuwa babu wani musulmi ko kuma wani balarabe mai kishi da kuma lamiri da zai amince da wannan magana sannan kuma masu fadin wannan magana ba za su taba tsira daga irin wannan zargi da munanawa ba.