A+ R A-
23 July 2019

Mahangar Jagora Kan Shirin Sulhu Da Kuma Ha’incin Kasashen Larabawa

Shirin Sulhu Da Kuma Ha’incin Kasashen Larabawa

A yau hanyar yaudarar da sahyoniyawa da masu daure musu gindi – wacce gwamnatin Amurka ita ce babbar mai daure musu gindin – ita ce su dinga amfani da wannan suna mai dadi da kyau na sulhu. Ko da yake sulhu lamari ne mai kyaun gaske; to amma sulhu a ina kuma da wa? Wani mutum ne ya shigo cikin gidanka, ya karya kofar gidan da karfin tsiya sannan kuma ya yi maka dukan tsiya, ya ci mutumci da kuma wulakanta iyalai da ‘ya’yanka sannan kuma ya kwace dakuna biyu daga cikin dakuna ukun da suke gidan ya zauna a cikinsu sannan kuma ya ke cewa da wani dalili ne ya sanya kake kai kara zuwa nan da can, da wani dalili ne ka ke fada da kuma nuna rashin amincewarka; ka zo mu yi sulhu. Shin akwai sulhu cikin hakan? Dabi’ar wannan gwamnati ita ce wuce gona da iri. Gwamnatin yahudawan sahyoniya, bisa asasi ma ta ginu ne bisa amfani da karfi da zalunci kuma da hakan ne ta ke ci gaba. Idan ba don hakan ba, da ba ta ci gaba ba sannan kuma a nan gaba ma ba za ta ci gaba din ba. Suna ce musu su yi sulhu da wannan gwamnatin! Idan har sun amince da hakkinsu – wato idan har sun yarda su dawo da wannan gina wanda shi ne Palastinu ga masu shi sannan suka kama gabansu; ko kuma suka nemi izini daga wajen gwamnatin Palastinu suna cewa ku ba mu izinin wasu daga cikinmu, ko kuma dukkaninmu mu zauna a wannan kasar – babu wani wanda zai yake su. (Abin da zai janyo) yaki shi ne cewa su shigo gidajen mutane da karfin tsiya; su fitar da su daga gidan sannan kuma har ya zuwa yanzu su ci gaba da zaluntar su. A halin yanzu ma suna ci gaba da zaluntar dukkanin kasashen wannan yanki sannan sun kasance barazana ga kowa da kowa. A saboda haka, wadannan mutane suna son sulhu ne a matsayin matakin farko na wuce gona da irin su na gaba. Idan har aka tabbatar da sulhu, hakan zai zamanto musu wani share fage ne na aiwatar da wuce gona da irin da suke son aikatawa a nan gaba.

 

Shirin Sulhu Da Zaman Lafiya Tsakanin Palastinawa Da Isra’ila

 

Daya daga cikin batutuwan da a yau suke yawo, don a mance da matsalar Palastinu da kuma hana gabatar da hakan cikin tunanin al’ummar musulmi shi ne dai wannan batun na tattaunawar da suke kira ta sulhu da take gudana tsakanin wata jama’a ta Palastinawa da Isra’ilawa. Wato wannan batu na zaman lafiya da kafa hukumar da suka kira mai cin gashin kai ta Palastinu. Wannan kuwa daya ne daga cikin mafiya munin yaudarar Isra’ilawa wanda abin bakin cikin shi ne cewa wasu daga cikin musulmi da wasu daga cikin su kansu Palastinawan sun fada tarkonsa. Don me? Saboda bisa asasin zato mafi kyau ga daya daga cikin irin wannan tattaunawa da suka yi, idan har ma abin a ce ne dukkanin alkawuran da Isra’ilawa suka yi za su tabbata, to abin da wadannan Palastinawa za su samu shi ne dan wani abu kadan sama da kashi hudu cikin dari na kasar Palastinu! Wato daga wannan kasar Palastinun wacce mallaka ce ta Palastinawa kuma dukkaninta mallaka ce ta al’ummar Palastinun kuma hakkinsu ne, kashi hudu cikin dari ne kawai za a ba su. Shi din ma wani irin kashi hudu cikin darin? Shi kansa wannan kashi hudu cikin darin ba wai waje guda ba ne; a gurare daban-daban ne. Ba za su taba barin wannan mutumin da suka ce masa ka zo ka kafa wannan hukumar ya gudanar da wani aiki kamar na hukuma ba. Sun bukace su ne da su tafi can din amma kuma su tabbatar da cewa Palastinawa ba su yi wani abin da zai zama cutarwa ga haramtacciyar kasar Isra'ila ba. Wato wani dan yanki karami wanda aka rarraba shi wanda kuma ba za a iya mulkansa a matsayin wata kasa wacce ba ta cika ba ce za a ba su. Sannan kuma abin da ake son su aikata sakamakon hakan (abin da aka ba sun) shi ne cewa baya ga wadannan cibiyoyin tsaro na Isra’ila, su ma (wajibi ne) su dinga fada da Palastinawa da suke cikin yankunan Palastinu da aka mamaye. Irin ha’aincin wadannan mutane wadanda suke aikata hakan da sunan Palastinawa ya fi dukkanin ha’incin da ya zuwa yanzu aka yi a kan al’umma Palastinu muni. Babu wani aiki da suka yi wa wannan al’umma kuma ba ma za su iya ba.

 

Manufar Sulhu Tsakanin Larabawa Da Isra’ila

 

Gwamnatocin kasashen larabawa suna fadin cewa mu dai ba mu fi su kansu Palastinawa zama Palastinawa ba! Abin da su da kansu suke so, wajibi ne a aikata shi. Da farko dai batun Palastinu wani lamari ne na duniyar musulmi. Baya ga bangaren na siyasa da tsaro da tattalin arziki, lamari ne na nauyi na Ubangiji da kuma na Musulunci. Sama da komai kuma, batu ne na Ubangiji; to amma idan ma har mutum bai yi imani da Allah ba amma dai duk da haka yana son ya yi hidima wa al’ummar Palastinu, wajibi ne ya duba ya ga mene ne dukkanin al’ummar Palastinu suke fadi. A yau al’ummar Palastinu wadannan wadanda ‘yan’uwansu da aka kama suna nan cikin gidajen yarin haramtacciyar gwamnatin yahudawa da kuma dubun dubatansu wadanda suke nan a kan tituna da masallacin al-Aksa da kasuwanni da dukkanin yankunan da aka mamaye suna rera take da kuma yunkurawa. Wasu ‘yan tsiraru ne kawai wadanda aka kwadaitar da su suke tafiya su yi sulhu, ba wai dukkanin al’ummar Palastinu suka tafi sulhun ba ballantana a ce mu dai ba mu fi Palastinawa zama al’ummar Palastinu ba.

 

Dalilin Rashin Nasarar Boren Intifadar Farko

 

A wancan lokacin – wato a lokacin boren intifada na farko – yanayin sulhu da zaman lafiya a hankali a hankali ya kama ko ina cikin wannan yanki; wasu sun mika zuciyarsu ga Amurka, wata kungiyar kuma ta yi amanna da cewa ba za su iya tsayawa a gaban irin wannan matsin lamba na kasa da kasa ba, don haka ba su da wata hanyar da ta rage musu in ban da amincewa da batun sulhun – hakan ma da sharudda irin na Amurka da Isra’ila-. Bayan abubuwan da suka faru a wancan lokacin a wannan yankin, an samar da yanayin amincewa da wannan nazariya.

A wancan lokacin (lokacin Intifadar farkon) an gabatar da wasu hanyoyi guda biyu ne na mu’amala da haramtacciyar kasar Isra'ila: (wato ko dai kai) kai hari na sojin kasashen larabawa ga Isra’ila – wanda dukkanin kwarewar da aka samu a wannan fagen sun fuskanci rashin nasara ne – ko kuma hanyar sulhu da zaman lafiya wanda za ta iya tabbatar da bukatun Isra’ila ta hanyar zaman lafiya da ruwan sanyi a bangare guda su kuma za su fice daga wasu yankuna na Palastinawa da suka mamaya, hakan kuma zai tabbatar da rashin ci gaban sojin kasashen larabawa; irin abin da aka cimma a Camp David. A wadancan ranakun, ba a ma maganar hanyar gwagwarmaya, ana cewa wai hakan bai samu karbuwar dukkanin al’umma ba

 

Sakamakon Shirin Zaman Lafiya Na Oslo

 

Al’ummar Palastinu sun fuskanci hasarori daban-daban sakamakon wannan bore na Intifadarsu da ta gabata sannan kuma sun sadaukar da shahidai da wadanda suka sami raunuka da yawa a wannan tafarki na Musulunci da kuma ‘yanto kasar Musulunci. To amma daga karshe dai yarjejeniyar Oslo ta dakatar da hakan. A halin yanzu dai hatta su kansu wadanda suka tsara wannan yarjejeniya ta Oslo da kuma masu goyon bayanta ba sa kare ta kuma; saboda kuwa a aikace sun fahimci cewa Isra’ila tana so ne kawai ta magance matsalolin da take fuskanta. Idan ma sun ba wa Palastinawa wani dan karamin abu to sun yi hakan ne don kawai a kashe wutan boren Intifada da kuma rage irin hasarar da za su yi. Daga lokacin da suka magance matsalarsu daga nan cikin kuskure suka ji cewa shi kenan al’ummar Palastinu ba su da karfin sake kaddamar da wani bore na Intifadan da gwagwarmya da kuma fuskantarsu. Don haka sai suka dakatar da aiwatar da dan wannan abin da suka ba wa Palastinawan sannan kuma suka fitar da maitarsu ta mamaya a fili. Irin tafarkin da aka bi wajen sulhu da kuma yarjejeniyar Oslon ta sanya al’ummar Palastinu cikin wani yanayi da kuma fahimtar cewa ba su da wata mafita da ta wuce mikewa tsaye.

 

Ha’inci Ga Koyarwar Palastinu

 

Dukkanin kokarin (wadannan mutane) ya ginu ne bisa ganin cewa an mance da sunan al’ummar Palastinu gaba daya; tamkar ka ce babu wata kasa mai suna Palastinu da aka yi kuma babu wata al’umma da take mallakan wannan kasar. Ta haka ne suka samar da yanayin share fagen wannan aiki sannan kuma mutum cikin dukkanin al’ajabi da bakin ciki yana ganin yadda wasu suka mika kai sannan kuma har ya zuwa yanzu mutum yana iya ganin yadda wasu suke amincewa da irin wannan lamari da ke cike da zalunci mai ban mamaki da kuma wauta – ga wadannan mutane da suka mika kai din – suna amincewa da shi. A yau hakan yana faruwa. Wasu mutane da ake kira Palastinawa ne suka kawo su wani yanki na kasar Palastinu mai girma sannan kuma suka ajiye a can – cikin wannan yanki wanda kashi hudu ne cikin dari na kasar Palastinu – su kafa wata hukuma nakasassiya ta karya, wani irin mulki na jeka na yi ka sannan kuma abin da suke bukata daga wajensu (sakamakon dan wannan abin da suka ba sun) shi ne a mance da lamarin Palastinu da al’ummar Palastinu a yi watsi da shi. Sannan kuma duk wani daga cikin Palastinawa da ya ambato sunan Palastinu, sunan kasar Palastinu da tarihin Palastinu za su yi mummunar mau’amala mai cutarwa a gare shi, sannan kuma jami’an tsaronsu za su fada masa da dukkan karfinsu.

 

Ha’incin Mahukuntan Larabawa Ga Palastinu

 

Yahudawan sahyoniya da masu daure musu gindi a sahun gabansu kuwa ita cewa kasar Amurka suna ta rera taken sulhu da zaman lafiya don tabbatar da ikon ‘yan fashin kasar Palastinu sannan kuma suna fada wa duk wani mai adawa da hakan da dukkan karfinsu. A shekarun da suka gabata wasu daga cikin gwamnatocin musulmi hatta ta baya ma sun kai hari kan wasu kasashe da suke sahun gaba! irin shiru da ke nuni da amincewa na mafi yawa daga cikin shugabannin kasashen larabawa wanda a wasu lokuta ma yake tare da ha’inci a fili, bugu da kari kan wasu matakai na wulakanci da ha’inci na wadanda suke da’awar jagorantar al’ummar Palastinu sun gudanar da wasu abubuwa wadanda suke tabbatar da cewa suna so ne kasar Musulunci ta Palastinu ta ci gaba da kasancewa karkashin mamaya sannan kuma al’ummar Palastinu da ake zalunta su ci gaba da zama fursunoni da ‘yan gudun hijira.

Shiru da kuma yin sulhu mai cike da ha’inci na mafi yawa daga cikin gwamnatocin larabawa hatta ma bayyanar da rashin damuwa da kuma halin ko in kula ga batun Palastinu da wasunsu suke nunawa, hakan ya kai lamarin ta yadda haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa, bayan shekara da shekaru na boyewa a wasu lokuta ma da inkarin, a halin yanzu a fili take maganar babbar Isra’ila sannan cikin rashin kunya da wauta suke sake fadin aniyarsu ta sake kwace wasu sabbin yankuna na kasar musulmi.