A+ R A-
09 December 2019

Amsoshin Tambayoyi Kan Juyayin Ashura Daidai Da Fatawar Ayat. Khamenei (2)

NB: A kwanakin baya mun kawo muku kashin farko na fatawoyi da mahangar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei dangane da juyayi da zaman makoki na Ashurar Imam Husain (a.s) da kuma na sauran Imaman Ahlulbaiti (a.s); kamar yadda Hujjatul Islam wal muslimin Muhammad Husain Fallahzadeh, daya daga cikin membobin bangaren amsa tambayoyin fikihu a ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya amsa.

To a halin yanzu ga kashi na biyu na wadannan tambayoyi da amsoshinsu:

T: Assalamu alaikum. Muna godiya da wannan mataki mai kyau wanda kuma ya dace. Tambaya ta ita ce na yi bakance gudanar da taron juyayin (Ashura) na kwana arba’in, to sai dai kuma yanayin  gidana ya sanya ba zan sami damar gudanar da juyayi na kwanaki arba’in din ba. A nan me ya kamata in yi?

Amsa: Ya zo cikin hukunce-hukuncen bakance cewa matukar mutum ya yi bakance da sharuddan da shari’a ta tanadar, to aiki da hakan ya zama wajibi. To amma idan har daga baya ya zama ba shi da karfin aikata wannan bakance na sa, to wajibcin ya fadi.

A saboda haka idan har ba ka da karfin aikata wannan bakance, sannan kuma ka sanya sharadin cewa za ka aiwatar da bakancen naka ne a cikin gidanka sannan kuma a halin yanzu ba za ka iya yin hakan a cikin gidan ba, to batun wajibcin ya tashi. To amma idan har ba ka daure bakance da wani sharadi ba (misali ba ka ce a gida din ne kawai za ka yi ba), sai ka fara yi a gidan naka sai kuma daga baya ya zamana ba za ka iya yi a gidan ba, amma akwai wani wajen da za ka iya yi, to a nan aiki da wannan bakancen wajibi ne.

A saboda haka amsar wannan tambayar a takaice ita ce cewa idan har mutum ya yi bakance da ingantattun sharudda, to ya zama wajibi a kansa ya aiwatar da bakance. Amma idan a halin yanzu ya zamana ba shi da karfin aikata hakan ta bangaren kudi ko karfi na jiki ko kuma wani dalili na daban, to wajibcin aiki da bakancen ya fadi a kansa.

T:  Shin ya halalta a sauya bakance daga wani waje zuwa wani wajen na daban ko kuma daga wani nau'i zuwa ga wani nau'i na daban saboda wata lalura? A matsayin misali mutum ne yayi bakancen cewa zai ba wa masu juyayi abin ruwan sha mai zaki, to amma a halin yanzu da yake ana sanyi sai ya yanke shawarar ba su madara mai dumi.

Amsa: Idan har bakance ya cika sharadi na shari’a wanda daga cikinsu har da fadin sigar bakance wanda a yayin bakance wajibi ne a fadi siga, wato a fadi cewa na yi bakance wa Allah cewa zan aikata kaza, mai yiyuwa ne a sanya sharadin cewa ga misali (a ce) idan har na sami saukin rashin lafiyan da na ke fama da shi ko kuma na sami damar sayen gida ko kuma na ci jarabawar da zan rubuta da makamantan hakan. To matukar ya samu biyan bukata ko kuma cikar wannan sharadin, to wajibi ne ya aikata wannan bakancen.

Idan har bakancen ya zama wajibi, to babu wata maganar sauyi kuma. Amma idan har yanayin aiwatar da wannan bakance ya kawu, wato ga misali mutum yayi bakancen cewa zai ba da ruwan zaki mai sanyi to amma sai ga shi sanyi ya shigo, to aiki da wannan bakancen ba wajibi ba ne. To amma idan maimakonsa sai ya ba wa mutane ko kuma masu juyayin madara mai dumi, shin akwai matsala? A’a babu matsala. Zai ma sami ladar hakan, to amma a mahangar hukunci na shari’a kan cewa shin hakan wajibi ne ko a’a? To mahangar mai girma Jagora dai ita ce cewa idan har maudhu’in abu ya kau ta kowane yanayi, ta yadda ba za a iya aikata wannan bakance ba, to aiki da shi ba wajibi ba ne. To amma idan har yana son samun lada, babu matsala cikin hakan. A matsayin misali maimakon ruwan sanyi mai zakin sai ya ba wa masu juyayin madara mai dumi.

T: Ya ya mu’amalar wani mawakin juyayin Ahlulbaiti (a.s) ya kamata ta kasance?

Amsa: To daga dukkan alamu ba yana tambaya ne dangane da yanayinsa da kuma ayyukan mawakin juyayin Ahlulbaitin na ibadu ba ne. Daga tambayar za a iya fahimtar cewa tambayar tasa ta shafi bangaren aikinsa na wake ne. A daya daga cikin tambayoyin da suka gabata mun yi ishara da cewa abubuwan da za a fadi a kan mimbari a matsayin wa’azi da kuma bayanin abubuwan da suka faru a Ashura da makamantansu, da farko dai: wajibi ne ya zamanto babu karya a ciki. Na biyu kada ya zamanto akwai guluwi dangane da Ma’asumai cikinsa, wato wuce gona da iri. Ko shakka babu (Imamai) suna da matsayi mai girman gaske, suna da matsayi na isma da imamanci ko kuma Annabi (s.a.w.a) yana da matsayi na annabci; babu wani matsayi da ya wuce wannan. Su kansu sun hana a yi musu guwuli da wuce gona da iri.

Haka nan bai kamata su dinga fadin maganganun da suka saba da kuma maganganu na haramun irin su gaiba (cin naman) wasu, cin mutumci da kaskantar da muminai, abubuwan wadanda ba su dace da matsayin ma’asumai ba, abubuwan da suka saba wa matsayi na muminai da sauran munanan maganganu cikin waken da suke yi ba. Haka nan kuma su yi la’akari kada su dinga fadin abubuwan da, koda kuwa su a kan kansu ba maganganu ne masu muni ba, to amma makiya za su yi amfani da hakan wajen yada bakar farfaganda a kan mazhabar Ahlulbaiti ko mabiya mazhabar Ahlulbaitin. Lalle wajibi ne su kula da hakan.

Haka nan kuma wajibi ne ayyukan mawakin Ahlulbaitin, da farko su zamanto saboda Allah kawai. Wato su zamanto don Allah ba saboda riya da nuna kai ba. Na’am mai yiyuwa su karbi lada ko wata kyauta, to amma kada waken na su ya zamanto saboda wannan kyautar ne. Haka nan kuma ya zamanto akwai darasi da karantarwa cikinsa.

Lalle zan iya tunawa kuma ina wajen da mai girma Jagora ya ke gaya wa wasu mutane biyu daga cikin sanannun mawakan kasar bayan da suka gabatar da majalisin waken juyayi da Jagoran ya ke shiryawa. Bayan da suka gama wakensu a majalisai mabanbanta sun zo wajen Jagora, a fili na ji yana gaya musu cewa wajibi ne wadannan wakoki na ku su zamanto masu ilmantarwa da kuma darasi a cikinsu. Daga nan sai ya yi musu wasicci da su nemi wasu kasidu. Ina iya tunawa har ya kawo sunan littafin Diwan Sa’eb, yana cewa akwai kasidoji masu kyau da ma’ana cikin littafin da za ku iya amfani da su. Wajibi ne mimbarinku ya zamanto mai cike da ilmintarwa ta yadda masu saurarenku za su amfana da kuma kara irin masaniyar da suke da ita. Yana da kyau wakokinku su zamanto sun kumshi tarihin tsarkakan Imamai, da irin musibun da suka shafe su da kuma irin danyen aikin da makiya suka aikata musu, insha Allahu.

T: Shin akwai matsala cikin karbar kudi saboda waken juyayi?

Amsa: Duk da cewa ayyana farashi saboda wannan aikin ba lamari ne da ya dace ba, to amma karbar lada da kyauta saboda mutum ya hau mimbari ya yi wakoki da wa’azi na juyayi, babu matsala cikin hakan. Kamar yadda muka fadi bai kamata a ce asalin manufa da burin mai wa’azi da waken juyayin Ma’asumai da Aba Abdillah al-Husain (a.s) ya zamanto su ne wadannan abubuwan ba, don insha Allahu ya samu damar samun ladar wannan juyayi da wakoki na juyayi sosai kamar yadda mai girma Jagora da kuma Imam Khumaini (r.a) suke fadin cewa suna daga cikin mafiya girma da falalar a ayyukan da suke kusata mutum da Ubangiji da kuma gina mutum.

T: Me ya kamata mu yi a lokacin da muke zaune a wani majalisi na juyayin da mai wa’azin yake fadin abubuwan da za su iya cutar da hadin kai tsakanin Sunna da Shi’a?

Amsa: A lokuta da dama kun sha jin kiran da Jagoran juyin juya halin Musulunci – a baya kuma marigayi Imam Khumaini – ya ke yi da kuma irin jaddadawar da ya ke yi kan muhimmancin hadin kai tsakanin musulmi. Da yake a yau muna da makiyan da muka yi tarayya kansu: wato ma’abota girman kan duniya da sahyoniyawan duniya; wadanda ba wai Shi’a ne kawai suke hari ko kuma Sunna ba, face dai addinin ne gaba dayansa suke kiyayya da shi. A saboda haka ne ake kira sannan kuma a hukumci na shari’a a mahangar mai girma Jagora, bai halalta a yi duk wani abu, shin cikin jawabi ne ko kuma cikin wakoki da sauran ayyuka wanda zai cutar da wannan hadin kai da ake da shi tsakanin musulmi wanda makiya za su yi amfani da hakan wajen cimma manufofinsu ba, hakan ma haramun ne. Wajibi ne a nesanci hakan.

T: An yi tambayar cewa shin ya halalta mutum ya shasshafa laka da tabo a jikinsa da sunan alama ta juyayi?

Amsa: Akwai bambanci dangane da yadda ake sanya laka ko kasa din a wasu bangarori na jiki. A wasu wajajen a ranar Ashura wasu su kan shasshafa laka ko tabo a kansu don su nuna cewa suna cikin yanayi na juyayi ne. To amma idan har lamarin ya kai yanayin da zai zamanto abin dariya da izgili da kuma nuna yatsa ga mutum ko kuma makiya su yi amfani da hakan wajen cutar da mazhabar Ahlulbaiti ko kuma mabiyansu, to hakan haramun ne. A saboda haka idan dai a yanayi ne da aka saba da shi da bai kai wancan matsayin (na izgili ko kuma makiya su yi amfani da hakan wajen cutar da mazhabar ba), don kawai mutum ya nuna yana cikin yanayi na juyayi ne, to babu matsala cikin hakan. Amma idan har ya kai yanayin da za a dinga izgili da mutum ko kuma cin mutumcin mazhabar, to bai halalta ba.

T: Shin akwai matsala mutumin da ba muharrami ba ya ji sautin wakokin juyayi ko kuma kukan mata masu juyayin?

Amsa: Idan har hakan zai iya janyo hankulan mazajen da ba muharramai ba ko kuma zai iya haifar da wata lalata, to lalle akwai matsala cikin hakan. To idan har bai kai hakan ba, ba haramun ba ne a mahangar mai girma Jagora, amma dai bai kamata mazajen da ba muharramai ba su dinga jin muryar kuka da ihun juyayin mata ba.

Kira Na Gaba Daya Ga Masu Juyayi Da Kuma Yadda Ya Kamata A Yi Juyayin.

Wani lamari da na ke son karawa shi ne cewa a irin wadannan shirye-shiryen da masu juyayi suke tsarawa, wadanda a mafi yawan lokuta abubuwan da ake yi, ana yin su ne saboda juyayi da kuma kaunar Imam Husain (a.s) ne. Amma wasu suna fadin wasu maganganu na cewa majalisin juyayin Aba Abdillah al-Husain wani majalisi ne na so da kauna, ba wai na fikihu ba. Wato suna cewa ne wadannan hukunce-hukuncen fikihu, na halal da haramun, ba su da matsayi a nan.

Na’am duk da cewa mun yarda da cewa juyayi yana da girman matsayi, sannan kuma kamar yadda mai girma Jagora ya ke fadi cewa juyayi yana daga cikin mafiya daukakan ayyukan kusaci da Ubangiji, sannan kuma wajibi ne a kiyaye irin juyayin da aka saba da shi da kuma nesantar shigo da wasu abubuwa marasa kyau ciki. To amma duk wanda yake son samun lada cikin juyayin nasa, to da farko dai wajibi ne ya kiyaye hukunce-hukunce na fikihu. Ya ya za a yi a ce shi kansa Imam Husain a lokacin sallar azahar din ranar Ashura, duk da makiya sun kewaye shi, amma haka ya yi salla a farkon lokaci sannan kuma cikin jam'i.

Wato yana nuna mana ne cewa babu yadda za a iya yin watsi da wadannan hukunce-hukunce na shari’a hatta a mafi tsananin yanayi. Har zuwa karshen lokaci, kiran da yake yi shi ne cewa kada mata su fito daga cikin haihominsu, ta yadda har makiya suka fahimci cewa hari ga wannan haimar ne zai iya dunkufar da shi. Wato wannan kan wani lamari ne da ba za a iya jure masa ba.

Wato batutuwan da ya shafi muharrami da wadanda ba muharramai ba. A saboda haka wannan magana ta kauna da kuma watsi da fikihu, kuskure ne. Hukunce-hukuncen fikihu suna gudana a ko ina sannan kuma a kowane yanayi. Wajibi ne a kula da kuma lura kada, abin Allah ya kiyaye, juyayi su zamanto dalilin aikata ayyuka na haramun da suka hada da haduwan muharramai da wadanda ba muharramai ba, da take hakkokin mutane ko kuma cutar da su. Haka nan kuma kada a yi watsi da wajibai, kada a bar salla, kada a yi wasa da sallar asuba har ta zamanto ramako.

Batu na karshe shi ne cewa a mafi yawan lokuta masu juyayi su kan taru ne a majalisi na juyayi suna rera wakoki na juyayi da makoki, suna bugu kirginsu, suna bugun jikinsu da sarka, saboda me suke yin hakan? Saboda su sami lada. Idan har muka da shakku kan wani aiki, wato ba mu san shin yana da lada ko babu ba, to me ya kamata mutum mai hankali ya yi? Sai ya yi watsi da abin da yake da shakku kansa, ya nemi abin da ya ke da tabbas akwai lada cikinsa.

A saboda haka a yayin juyayi da zaman makokinku, a yanayi na gaba daya ku dinga sauraren kiraye-kirayen maraja’ai, kiraye-kiraye da wasiccin mai girma Jagoran juyin juya halin Musulunci, da kuma nesantar abubuwan da za su zamanto abin isgili ga mazhaba, ayyukan da makiya za su yi amfani da su wajen cutar da mazhabar ko kuma wadanda za su haifar da rarrabuwan kai tsakanin musulmi. Ku gudanar da juyayinku ta yadda yayi daidai da matsayin mai girma Aba Abdillah da tsarkakan Imamai. Ku san cewa tabbas akwai lada cikin hakan. Ku nesanci ayyukan da suke haramun ne da wadanda kuke da shakku cikinsu, wato ko shakku na haramci ko kuma shakkun cewa shin akwai lada cikin ko kuma a’a.

Muna rokon Allah da Ya ba wa dukkaninmu dacewar gudanar da juyayin da ya yi daidai da shari’a.

----------------------------------------

Amsoshin Tambayoyi Kan Juyayin Ashura Daidai Da Fatawar Ayat. Khamenei (1)