A+ R A-
07 August 2020

Amsoshin Tambayoyi Kan Alaka Da Mabiya Sauran Mazhabobi Daidai Da Fatawar Ayat. Khamenei

“Wajibi ne musulmi su yi fada da duk wani abin da ke karen tsaye ga hadin kan musulmi; wannan wani nauyi ne mai girma da ke wuyanmu; wajibi ne ‘yan Shi’a su yarda da hakan, haka nan ma ‘yan Sunna; haka nan bangarori daban-daban na Shi’a, haka nan ma bangarori daban-daban da ake da su a tsakanin ‘yan Sunna”. (Jawabin Jagora a ranar 29-10-1392).

A kwanakin baya ne Cibiyar Kula da Wallafa Ayyukan Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, ya sanar da wani shiri na tattaro tambayoyin muminai dangane da hukunce-hukuncen alaka da mabiya sauran mazhabobi da addinai, don amsa su daidai da fatawar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei. To bayan tattara wadannan tambayoyin, an mika su ga Hujjatul Islam wal muslimin Muhammad Husain Fallahzadeh, daya daga cikin membobin bangaren amsa tambayoyin fikihu a ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, wanda ya amsa su.

Abin da ke biye fassarar tambayoyi da amsoshin ne:

Gabatarwa:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

“Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba” daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci da ake gabatar da tambayoyi na fikihu kansu sosai, shi ne batun hadin kai tsakanin musulmi. Hadin kai tsakanin musulmi ba yana nufin su yi watsi da akidunsu ko kuma su koma su yi aiki da fikihun wasunsu ba ne. Face dai abin nufin shi ne cewa ‘yan Shi’a su yi aiki da akidunsu da kuma aiki daidai da hukunce-hukuncen fikihunsu, su ma sauran kungiyoyin musulmi, ‘yan Ahlusunna su yi aiki daidai da fatawoyinsu na fikihu da kuma akidunsu. Ma’anar hadin kai ita ce haduwa kan batutuwa na asali wadanda aka yi tarayya cikinsu da nufin fada da makiyan da aka yi tarayya kansu.

A jawabin da ya yi a wajen taron hadin kan musulmi da aka gudanar a shekarar 1368 (1989), Ayatullah Khamenei ya fadi cewa: “Hadin kan musulmi, ba yana nufin musulmi da mabiya mazhabobi daban-daban su yi watsi da akidu da hukunce-hukuncen fikihunsu ba ne”. Haka nan a wani wajen yana cewa: “Lamarin ba shi ne cewa ‘yan Shi’a ko ‘yan Sunna su yi imani da akidun juna ba; a’a, kowa yana da akidarsa, duk wanda yake aiki bisa wata hujja da ya dogara da ita, hakan daidai ne. Lamarin shi ne kada mabiya akidu daban-daban su mika wuya ga waswasin makiya. Kada su yi fada da junansu, kada su yi gaba da junansu, kada su dinga cin kafar junansu”. A saboda haka lamarin shi ne cewa a halin yanzu dukkanin musulmi suna da wani makiyi da suka yi tarayya a kansa shi ne girman kan duniya da sahyoniyawan kasa da kasa. Don haka suna da bukatar hadin kai. Hakan wani lamari na asasi mai muhimmanci. Ba wai wata dabara ba ce, face dai wani lamari ne na asasi. Musulmi suna da batutuwa masu yawa da suka yi tarayya cikinsu. Don haka wajibi ne su hadu kansu. Su hada kansu waje guda don tinkarar makiya.

A wasu lokuta a lokacin da ake magana kan hadin kai, wasu suna zaton cewa, misali, su yi watsi da akidarsu ta wilayar Amirul Muminin (a.s) da tsarkakan Imamai (a.s). A’a, babu wanda yake fadin hakan. Abin da ake cewa shi ne kada mu yi rikici a tsakaninmu. Kada mu dinga kawo abubuwan da za su haifar da sabani a tsakaninmu. Mu hada kanmu waje guda da goyon bayan juna. A duk lokacin da wani makiyin da aka yi tarayya kansa ya kawo wa wata kasar musulmi hari, a hada hannu waje guda don fada da shi. Wannan ita ce ma’anar hadin kai.

T: Mene ne ma’anar Tabarri? Sannan kuma mece ce alakar da ke tsakanin Tabbari da la’ana?

Amsa: A wasu lokuta a kan kirga ‘Tawalli wa Tabbari’ daga cikin shika shikan addini, a wasu lokutan kuma daga cikin rassan (furu’ai) addini. Na’am dukkanin biyu daidai ne; wato suna da bangare na akida da kuma wani bangare na aiki. A bangaren imani da akida, tawalli yana nufin mu mun yi amanna da wilaya da kaunar Waliyan Allah, Annabawan Allah da tsarkakan Imamai (a.s) haka nan da mabiyansu. Haka nan kuma yana da bangare na aiki, wanda shi ne biyayya ga wadannan Waliyan Allah.

Shi kuwa Tabarri kishiyar tawalli ne; wato nuna kiyayya ga makiya Allah da waliyansa. Wajibi ne mukallafi ya zamanto yayi imani da wadannan abubuwa guda biyu, haka nan ma a fagen aiki, yayi riko da su. To sai dai ba dole ba ne mutumin da yake son aikata ‘tabbari’ ya zamanto mai la’ana da fadin kalmomin da ba su dace ba. Akwai musulmi da yawan gaske, tun farkon Musulunci har zuwa yanzu, hatta ma a wannan zamani na mu – irin su Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei – wadanda ma’abota riko da tawalli da tabarri ne, to amma ba ma’abota zagi da la’ana ba ne. A saboda haka, mutum yana iya zama ma’abocin tabbari (barranta), amma kuma ba tare da ya zamanto ma’abocin cin mutumci da zagi da la’antar abubuwan da wasu suke girmamawa ba. Mai girma Jagora dai ba ya ganin halalcin cin mutumcin abubuwa masu tsarki na sauran mutane, kai yana ganin hakan ma haramun ne.

T: Shin hukuncin hadin kai bai yi hannun riga da tabarri ba? Shin wajibi ne mutumin da ba wa Jagora Imam Khamenei yake wa takalidi ba yayi biyayya ga umurninsa na haramcin la’ana?

Amsa: Ko shakka babu hadin kan musulmi bai yi hannun riga da tabarri ba. Wato mutum yana iya kiyayya da makiya Allah da waliyansa, ya yi fada da wadanda suke yaki da musulmi, sannan a daidai lokaci guda kuma ya zamanto mai hadin kai da sauran musulmi. A saboda haka babu wani hannun riga tsakanin hadin kai da barranta daga makiya Allah da makiya waliyan Allah. A matsayin misali Imam Khumaini (r.a) ya kasance ma’abocin wilaya sannan kuma mai barranta da makiya Allah da makiya waliyan Allah, a daidai lokacin da kuma bai kasance yana cin mutumcin abubuwa masu tsarki na sauran musulmi ko kuma la’antar abubuwan da suke girmamawa ba. Akwai manyan mutane da suka kasance suna kira zuwa ga hadin kai sannan kuma suna barranta daga makiya Allah.

Hadin kai tsakanin musulmi da kuma nesantar rarrabuwa wani lamari ne na wajibi, sannan kuma haifar da sabani da rarrabuwan kai tsakanin musulmi wanda zai amfani makiya da ma’abota girman kan duniya da sahyoniyawa na kasa da kasa, haramun ne. Amma dangane da cewa shin idan mutum ba mai takalidi da Jagora ba ne, shin wajibi ne ya kiyaye wannan lamarin? Na’am wajibi ne sauran mutane su kiyaye wannan lamarin. Babu wani bambamci cikin wannan lamarin tsakanin masu takalidi da Jagora da masu takalidi da sauran maraja’ai. Don kuwa bisa fatawar dukkanin mara’ja’ai masu girma, aikata abubuwan da ba wajibi ba ne – koda kuwa mustahabi ne – idan har aikata hakan zai zamanto abin da makiya za su yi amfani da shi wajen bakanta mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma cin mutumcin mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ko kuma zai haifar da sabani da rarrabuwan kai tsakanin musulmi, ba ya halalta.

T: Mene ne ra’ayin Ayatullah Khamenei dangane da gudanar da taron la’anta?

Amsa: A lokuta da dama mai girma Jagora ya sha fadin cewa kada ku yi batanci ga ababe masu tsarki na sauran mutane. A saboda haka wajibi ne a nesanci hakan sannan abin da ya kamata a lura da shi a nan shi ne cewa wasu suna fadin babu matsala a yi la’anar a kebantattun tarurruka; alhali shi mai girma Jagora bai sanya wani kaidi ba cewa a taro na jama’a ne ko kuma na kebance. Face dai abin da yake cewa shi ne kada ku ci mutumcin ababe masu tsarki na sauran musulmi, wato kada ku yi batanci ga sauran mazhabobi na Musulunci. A nan mai girma Jagora yana cewa: “Wannan dan Shi’an da cikin jahilci da gafala ko kuma a wasu lokuta saboda wata manufa – saboda akwai wasu mutane da suke cikin Shi’a wadanda lamarinsu ba wai jahilci da rashin sani ba ne, face dai akwai wani aiki ne da aka ba su na haifar da fitina tsakanin musulmi – wadanda suke cin mutumcin ababe masu tsarki na Ahlusunna. To ayyukan wadannan kungiyoyi biyun dukkaninsu haramun ne a shari’a sannan kuma ya saba wa doka. A saboda haka batanci ga ababe masu tsarki na sauran mazhabobin Musulunci, a wajen mai girma Jagora haramun ne.

T: Shin haramcin cin mutumcin akidun mazhabobi ya hada har da wadanda ba Ahlusunna ba ne?

Amsa: To akwai wasu mazhabobin wadanda mabiyansu suke zaman lafiya da musulmi sannan kuma ba kasafai suke cin mutumcin ababen girmamawarmu ba. A saboda haka cin mutumcinsu idan har hakan zai haifar da rarrabuwan kai da kuma fitina cikin al’umma, to ko shakka babu haramun ne.

T: Ya Ya Mu’amalarmu za ta kasance da ‘yan Shi’an da suka dage wajen haifar da rikici da rarrabuwan kai tsakanin musulmi? Shin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna wajibi ne a nan?

Amsa: Ra’ayin mai girma Jagora shi ne cewa rarraba kan musulmi haramun ne, haka nan batanci ga ababen girmamawan sauran musulmi ma haramun ne. Aikata haramun kuwa munkari ne, sannan kuma hani ga munkari wajibi ne; sai dai tare da kula da sharudda da kuma yanayi.

T: Wasu suna fadin cewa maganar ‘yan’uwantaka da daidaito tsakanin Shi’a da Sunna wata magana ce kawai ta siyasa, ba hukunci ne na shari’a ba. Shin haka lamarin yake?

Amsa: A’a, lalle ba haka ba ne. Hadin kan musulmi hukunci ne na shari’a. Abin da mai girma Jagora yake fadi shi ne cewa: “Ni dai ina ganin maganar hadin kan musulmi a matsayin wani lamari mai muhimmanci, ba wai wani lamari na siyasa ko maslaha ba, ta yadda za mu ce maslaharmu ta tilasta mana kulla alaka da musulmin da ba ‘yan Shi’a ba. Yana da kyau musulmi a hankali a hankali su rage irin sabani na mazhaba da kabilanci da ke tsakaninsu don kuwa hakan lamari ne da ke amfanar makiya”. Yin abin da zai amfani makiya kuwa haramun ne.

T: Bisa la’akari da fakewar da wasu suke yi da batun bahasi na ilimi suna haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi, shin wajibi ne sai an yi bahasin ilimi kan batutuwan da ake da sabani kansu? Shin wani amfani wannan bahasi na ilimi yake da shi, sannan kuma ya ya ya kamata ya zama? Sannan kuma su waye ya kamata su yi shi?

Amsa: Dangane da bahasi na ilimi, mai girma Jagora dai ya amince da yin hakan. Mai girma jagora ya amince masana su zauna a tsakaninsu a kebantaccen waje su yi bahasi kan batutuwan da ake da sabani kansu tsakanin Shi’a da Sunna. Su yi bahasin maganganun juna, amma fa a yanayi na malanta, a fagage na ilimi, tsakanin masana. Yadda za a gudanar da shi ma ya zamanto ta hanyar wannan kyakkyawan jidali kamar yadda Alkur’ani ya fadi. Babu wata matsala cikin irin wannan bahasi na ilimi wanda ba zai haifar da sabani da rarrabuwan kai tsakanin musulmi ba.

Abin da ke da matsala kana kuma haramun shi ne haifar da rarraba tsakanin musulmi. Dangane da bahasi na ilimi, mai girma Jagora yana fadin cewa: “Idan har suna son su yi bahasi na ilimi, to babu wata matsala, don kuwa ni na yi amanna da bahasi na mazhaba. Idan har suna son su yi bahasi na mazhaba tsakanin malamai da masana, ba matsala su zauna su yi. To sai dai ba a idon mutane ba, face dai a fage na ilimi, su zauna a tsakaninsu su yi bahasin”. To ala kulli hal, wadannan dai bahasi ne na ilimi, wanda wajibi ne a gudanar da su a fage na ilimi don kada hakan ya yi sanadiyyar rarraba kan musulmi.

T: Shin a yayin da muke halin tafiya sai muka zo wucewa ta garuruwan ‘yan Ahlusunna, shin daidai ne mu yi salla a masallacinsu shi din ma cikin jam'i? Sannan shin dole sai mun yi amfani da turba ko kuma a’a?

Amsa: Babu matsala cikin yin salla tare da Ahlusunna. A lokacin da kuke wucewa sai kuka shiga masallaci kuka ga Ahlussunna suna sallar jam'i, to bisa ra’ayin mai girma Jagora za ku iya bin sallar, kamar a Makka da Madina ne a Masallacin Annabi. Mai girma Jagora yana cewa ne lamarin bai takaita kawai ga wadannan masallatai biyun ba. Sannan amfani da turba, idan har babu wata matsala, to ana iya yi. Ko kuma idan babu turbar a wajen, to yana iya tafiya inda babu darduma ko kuma wani da yake da abin da ya inganta a yi sujada a kansa yayi sujadar a wajen matukar dai babu matsala. To amma idan a wani waje ne da babu turbar ko kuma mai yiyuwa wasu su nuna rashin jin dadinsu idan ka yi amfani da turbar, ko kuma idan ka yi amfani da turbar hakan zai iya zama abin da zai zamanto batanci ga ababe masu tsarki na mazhabar Ahlulbaiti (a.s), to a irin wannan yanayin, bai kamata ku yi amfani da ita ba.

T: A yanayi na gaba daya, mene ne ra’ayin Ayatullah Khamenei dangane da alaka ta abokanta da mabiya sauran addinai musamman idan har akwai alaka ta jini ko dangantaka a tsakani?

Amsa: Kiyaye akida ta gaskiya wajibi ne. Alaka da shige da fice matukar dai ba za ta zamanto da cutarwa ga akida da kyawawan halayen mutum ba sannan kuma ba za ta zamanto abin zargi ga mutum ba, babu matsala cikin hakan. Wato a yanayi na gaba daya dai, matukar bai babu cutarwa da kuma barna cikin wannan alakar, babu haramci cikin hakan. A wasu lokutan ma alakar tana da sakamako mai kyau, wato tana da bangaren umurni da kyawawa da hani da munkari; musamman idan har suka zamanto daga cikin dangi na jini ne. To ta bangaren cewa katse zumunci haramun ne, don haka katse zumunci gaba daya da su bai halalta ba. Don haka wajibi ne a kulla alakar, sai dai tare da kiyaye batutuwan da muka yi ishara da su.

T: Shin ya inganta a karba ko ba da kyauta ga Kiristoci saboda Kirsimeti ko kuma wani biki daga cikin bukukuwansu? Mene ne hukumci musulmi ya tafi coci da nufin girmama Annabi Isa?

Amsa: Cikin dukkanin wadannan abubuwa biyu, matukar dai babu barna sannan kuma ba zai zamanto da zargi cikinsa ba, babu matsala. Karbar kyautarsu ko kuma misali tafiya coci sau guda don halartar wani taro, matukar dai babu barna cikin hakan, wato ba zai zamanto sanadiyar lalata akidarka ba sannan kuma babu wasu da za su yi mummunan amfani da hakan da kuma zarginka ba, to babu matsala cikin hakan. Amma idan har akwai barnar, to hakan bai halalta ba.

T: Mene ne hukumcin saye da sayarwa tare da mabiya sauran addinai?

Amsa: Saye da sayarwa da mabiya sauran addinai, in dai ba wadanda suke cikin yaki da musulmi ba, sannan kuma babu barna cikinsa, to babu matsala. Kamar yadda a kasarmu akwai ‘yan tsirarru mabiya sauran addinai da mazhabobi wadanda suke da shaguna na sana’a da saye da sayarwa sannan kuma mutane suna ciniki da su. Lalle a mahangar shari’a babu matsala cikin hakan.

T: Shin amfani da abincin da mabiya sauran addinai suka dafa, halal ne ko haram? Sannan shin namar dabbar da Ahlulkitabi suka yankan, halal ne?

Amsa: A ra’ayin mai girma Jagora cin naman da musulmi, daga kowace mazhaba suka fito – wato mazhabobin da aka yarda da su – suka yanka babu matsala, naman halal ne kuma yana da tsarki. Amma naman dabbar da wadanda ba musulmi ba na daga Ahlulkitabi suka yanka, ba halal ba ne; saboda wajibi ne naman da za a ci ya zamanto musulmi ne zai yanka dabbar bisa sharuddan da aka kafa. A saboda haka abinci da suka dafa wanda yake da nama a ciki (wanda suka yanka da kansu) ba halal ba ne. Amma amfani da sauran nau’oi na abincinsu kamar ganyaye, ‘ya’yan itatuwa ko kuma abin da suka yi da hannunsu da babu nama a ciki, babu matsala ciki. A bisa mahangar mai girma Jagora, Alhlulkitabi suna da tsarki, don haka babu matsala cikin cin abincin da suka dafa wanda babu nama a cikinsa.

T: Mabiya wani addini ko mazhaba ne suke a matsayin najasa? Sannan a ra’ayin mai girma Jagora mabiya sauran addinai da mazhabobin da suke najasa ne su, shin daga yin hannu da su ne ake samun najasa ko kuma sai inda akwai danshi a jikin hannun?

Amsa: A bisa ra’ayin mai girma Jagora, mazhabobin musulmi da sauran addinai wadanda Ahlulkitabi ne irin su Kiristoci, Yahudawa, Zorostawa da Sabi’awa, dukkaninsu suna da tsarki. Dangane da alaka da wadanda ba Ahlulkitabi ba, mujarradin yin hannu da su ko da kuwa akwai jika a jikinsa to amma ba jika ce mai naso ba, ko kuma muka yi shakkun shin cewa jikar ta koma jikinmu ko a’a, to a nan ana hukunta hakan da tsarki. Lamarin ba shi ne daga kawai ka mika wa wadanda ba Ahlulkitabi hannu, shi kenan hannunka ya najastu ba. Face lamarin shi ne hannunka zai najastu ne a lokacin da hannun daya daga cikinku ko kuma dukkaninku biyun suna da jika mai naso.

T: Mene ne nauyin da ya hau kanmu dangane da shigar Ahlulkitabi wajeje masu tsarki kamar masallaci da haramin Imamai? Shin wajibi ne mu hana hakan? Shin mabiya wasu addini ne ba za su iya shiga masallatan musulmi ba?

Amsa: Daukar wadanda ba musulmi ba da kai su masallaci bai halalta ba; amma idan har yin hakan da kuma kasantuwarsu a masallacin ba zai zamanto cin mutumcin ko kuma najasta masallacin ba, to babu matsala. Haka hukuncin yake dangane da shigarsu haramin Ma’asumai (a.s) da kuma ‘ya’yansu.

T: Mene ne ra’ayin Ayatullah Khamenei dangane da auren dindindin ko kuma na wani lokaci (mut’ah) – shin budurwa ce saurayi –  tsakanin ‘yan Shi’a da mabiya sauran addinai ko mazhabobi?

Amsa: Da farko dai aure tsakanin musulmi, matukar dai babu barna cikinsa, to babu matsala. Amma idan har akwai barna da cutarwa, to ba ya halalta ko da kuwa a tsakanin mabiya mazhaba guda ne. To amma dangane da auren wanda ba musulmi ba, to idan dai aure ne na mut’ah tsakanin musulmi namiji da mace Ahlulkitabi, to babu matsala. Amma aure na dindindin kan da mace wacce ba musulma ba, bai inganta ba. Mace musulma kan ta kowace fuska ba za ta iya auren namijin da ba musulmi ba.

T: Ni din nan mai horarwa ne a wata cibiya ta tarbiyyar yara. Akwai wasu yara da matasa yahudawa a cibiyar. A lokuta da dama sukan ba ni abincinsu sannan ni kuma na kan dauka; a wasu lokuta ma na kan ci. To amma ni kuma a duk lokacin da na ba su wani abinci, a fili suke fadin cewa mu dai ba ma cin abincin musulmi. To a nan me ya kamata in yi? Shin mu ma bai kamata mu ci abincinsu ba?

Amsa: Idan har kana da shakku ne kan tsarkin abincinsu, shin halal ne ko kuma a’a, to idan kana zaune na a kasar musulmi sannan kuma abincin su a kasuwar musulmi suke samar da shi, to abincin halal ne.

T: Shin akwai matsala cikin saye da kuma amfani da kayayyakin da mabiya wasu addinai da mazhabobi suke kerawa sannan kuma suke amfani da kudin da ake samu din wajen yada wannan addini da kuma yawan mabiyansu? Sannan idan kuma ba a tabbatar da hakan ba fa?

Amsa: Da farko dai babu matsala cikin saye da sayar da kayan mabiya sauran mazhabobi. Idan har muna da yakinin cewa saye da sayarwar za ta sanya makiya Musulunci samun damar karfafa kansu kamar sahyoniyawa; ko kuma za a karfafa da kuma yada wata kungiya ko kuma mazhaba ta bata ko kuma taimako wajen yada hakan, to akwai matsala cikin hakan. Amma idan har ba mu da masaniyar cewa za a yi amfani da saye da sayarwar wajen yada batattun akidu da mazhabar bata ba, to babu matsala cikin saye da sayarwar.

T: A yayin da muke tafiya da ‘yan kasashen waje, shin akwai bukatar mu tambaye su addininsu? Shin za mu iya shan ruwa ta bangaren da suka sha?

Amsa: Babu bukatar tambayar addininsu. Idan har kuna rayuwa ne a kasashen musulmi, to insha Allahu musulmi ne babu wata matsala cikin tafiya tare da su. To amma idan a kasar da ba ta musulmi ba ce kuke rayuwa, a kasa ko kuma garin da mafiya yawan mutanen wajen ba musulmi ba ne, idan har ba kasan addininsu ba, to alaka da su daidai yake da alaka da wadanda ba musulmi ba. Cin abinci ko kuma tafiya tare da su matukar dai babu barna a cikin hakan sannan kuma abincin ba na haramun ba ne, babu matsala cikin hakan. Hakan bangaren da suka sha ruwa, idan har musulmi ne ko kuma Ahlulkitabi, to shi ma babu matsala za ku iya shan ruwan. Amma idan ka san cewa su din nan ba musulmi ba ne sannan kuma ba Ahlulkitabi ba ne, wato mabiya wani addini ne na daban, ko kuma ba su ma da adddini ko mazhaba. To a nan bangaren da suka ci abinci ko suka sha ruwa, ya najastu. Don haka bai kamata a ci ko a sha ta wannan bangaren ba.

T: Mene ne hukumcin gaisawa (shan hannu) tsakanin musulmi namiji da mace wacce ba musulmi ba?

Amsa: Bai halalta namiji da mace muharramai su mika wa juna hannu ba, babu wani bambanci a wannan bangaren shin daya bangaren musulmi ne ko ba musulmi ba. Wato taba jikin wanda ba muharrami ba haramun ne, shin musulmi ne ko kuma ba musulmi ba. Duk da cewa an toge wani yanayi wanda shi ne cewa idan har ya zamanto lalura, ana iya amfani da safar hannu ko wani kyalle shi din ma da sharadin ba za a matsa hannun juna ba sannan kuma babu barna cikin hakan kuma hakan ba zai tada sha’awa ba, to a ra’ayin Jagora babu matsala cikin hakan. A saboda haka yana da kyau a nesanci irin wadannan abubuwan don kuwa taba jikin wanda ba muharrami ba, haramun ne.

T: Shin umurni da kyakkyawa da hani da munkari yana hawa kan Ahlulkitabi? Ga misali a garin mu a unguwar da kiristoci suke zaune ba a kula da dokoki na Musulunci irin su hijabi da sauransu; shin akwai nauyi a wuyanmu dangane da hakan?

Amsa: Da farko dai kamar yadda aka dora wa musulmi wajibcin kiyaye hukunce-hukunce na shari’a, haka nan yake wajibi a wuyan wadanda ba musulmi ba. Na’am gaskiya ne ba su yi imani da wadannan hukunce-hukunce ba kuma ba sa aikata su, to amma a mahangar addinin Musulunci, a bahasi na akida, su ma suna da wannan nauyi na kiyaye hukunce-hukuncen a wuyansu. Na biyu dangane da hukunce-hukuncen zamantakewa na Musulunci irin su kiyaye hijabi a cikin al’ummar musulmi, ko kuma shan ruwa a gaban jama’a a watan Ramalana, wajibi ne su kiyaye su. A saboda haka idan wata mace wacce ba musulma ba da take rayuwar cikin al’ummar musulmi ta ki sanya hijabi, to hakan munkari ne na bayyane. Kamar yadda muke da nauyi a wuyanmu na umurni na kyakkyawa da hani da mummuna idan har sharudda suka cika a kan musulmi, haka ya zama wajibi a yi umurni da kyakkyawa da hani da mummunan a lokacin da aka ga wadanda ba musulmi ba sun aikata wani munkari sannan kuma sharuddan hakan sun cika.

T: Mene ne hukuncin alaka da mutanen da suke amsa sunan musulmi, amma a wasu lokuta ma suna inkarin addinin Musulunci da kuma Allah Madaukakin Sarki?

Amsa: Idan har a zahiri suna bayyanar da Musuluncin su, wato sun fadi kalmomin shahada, sannan kuma ba mu da masaniyar cewa har cikin zuciyarsu su musulmi ne ko a’a, to a wasu lokuta mai yiyuwa ne su aikata wani aiki wanda ya saba wa dokokin Musulunci, to su din nan suna da hukunci na musulmi ne. Amma idan har mun san cewa ba su yi imani da Musulunci ba, kawai magana ce ta fatar baki suke yi da kuma bayyanar da Musulunci a zahiri. To a nan kan ba su da hukunci na musulmi. Don haka alakar da za a yi da su ta banbamta da alakar da za a yi da musulmi. Koda yake ba wai muna cewa ne gaba daya alaka da su ba ta inganta ba ne. Babu matsala cikin alaka da su, to amma kada ya zamanto akwai barna cikin haka da kuma goyon bayan akidarsu. Kamar yadda kuma bai kamata a zargi mutanen da suke da alaka da su da cewa suna alaka da mutane ‘yan ba ruwanmu da addini ba.

T: Shin musulmi zai iya aiki wa kafiri da zama karkashinsa yana mai karbar albashi daga wajensa?

Amsa: Zama karkashin wani da ma’anar zama karkashin ikon wani wanda ba musulmi ba, bai halalta ba. Amma idan ma’aikaci musulmi yana aiki wa wani kafiri, da cewa ka yi min aiki kaza in biya ka sannan shi kuma yayi amma ba cikin kaskanci ba, face dai yana aikin ne don ya sami albashi, haka nan kuma aikin nasa bai saba wa shari’a ba, sanna kuma bai ci karo da irin wannan daukaka da karama ta Musulunci ba, to babu matsala cikin hakan. Sannan albashin da aka karba din halal ne.

Source:

http://farsi.khamenei.ir/news-content?id=28592

http://hausa.khamenei.ir/index.php?option=com_content&task=view&id=1465&Itemid=40