A+ R A-
22 February 2024

Ayyukan Ibada Da Abubuwan Da Suka Faru A Watan Rajab

 

 

 

 

 

 

 
 

Abubuwan Da Suka Faru A Rajab

 

 

Abubuwa
Rana
Haihuwar Imam Muhamad al-Bakir (a.s)

1 Ga Watan Rajab

Shahadar Imam Ali an-Hadi (a.s)

3 Ga Watan Rajab

Haihuwar Imam Muhammad al-Jawad (a.s) 10 Ga Watan Rajab
Haihuwar Imam Ali Ibn Abi Talib (a.s) 13 Ga Watan Rajab
Shahadar Sayyida Zainab (a.s)

15 Ga Watan Rajab

Shahadar Imam Musa al-Kadhim (a.s) 25 Ga Watan Rajab
Shahadar Sayyiduna Abu Talib (a.s) 26 Ga Watan Rajab
Mi’irajin Manzon Allah (S) 27 Ga Watan Rajab
 

 
 

Falala da Ayyukan Rajab

 

Falala da Wasu Daga Cikin Ayyukan Da Ake Son Aikatawa a Wannan Wata.

Wannan wata na Rajab da Sha'aban da Ramalana watanni ne da suke da girma da kuma falaloli masu yawan gaske.

An ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa:

rajab wata ne na Ubangiji mai girma, wani wata daga cikin watanni bai yi kusa da shi ba wajen falala da daukaka, Yakan kafirai a cikinsa haramun ne. Ku sani fa Rajab wata ne na Allah Madaukakin Sarki, watan Sha'aban kuwa wata na ne, sannan Ramalana kuwa watan al'ummata ne; ku sani duk wanda ya azumci rana guda cikin wannan wata zai samu yardar Allah da kuma nesanta shi daga fushin Allah da kuma rufe masa kofa daga cikin kofofin wuta.

Haka nan kuma an ruwaito Imam Musa bn Ja'afar (a.s) yana cewa:

Wanda ya azumci rana guda cikin wannan wata na Rajab, za a nesanta shi da wuta kimanin tafiyar shekara guda, wanda kuwa ya azumce shi na kwanaki uku, to za a sanya shi a Aljanna.

Haka nan kuma an ruwaito daga gare shi (a.s) cewa:

Rajab wani kogi ne daga cikin Aljanna, farinsa ya fi nono haka nan kuma zakinsa ya fi zuma; duk wanda ya azumci rana guda daga cikinsa, Allah Madaukakin Sarki Zai shayar da shi daga wannan kogi.

Har ila yau an ruwaito Imam Ja'afar al-Sadik (a.s) yana cewa:

Manzon Allah (s) yana cewa: Rajab wata ne na neman gafarar Ubangiji ga al'ummata, don haka ku yawaita yin istigfari a cikinsa, don kuwa Allah Mai gafara ne, Kuma Mai Rahama....Ku yawaita fadin: Astagfirullah Wa Asluhuttaubah.

Wannan wata dai yana da falaloli da yawan gaske, mai son karin bayani sai ya koma littattafan da suka yi magana kan hakan.

Sannan kuma an ruwaito cewa duk wanda ba zai iya yin wadannan abubuwa da muka ambata ba, to yana iya karanta wannan tasbihi sau dari kowace rana don ya samu ladan masu azumin. Tasbihin kuwa shi ne:

Subhana Ilalahil Jalili; Subhana Man La Yanbagi al-Tasbihu Illa Lahu, Subhana al-A'azzi al-Akram, Subhana Man Labisa al-Izza wa Huwa Lahu Ahlun

Haka nan kuma bayan azumi a cikin wannan wata akwai wata salla kuma da Manzon Allah (s) ya kwadaitar da mu da mu yi a ranar Alhamis na farko na wannan wata mai alfarma wanda ya ce duk wanda ya yi ta zai samu wadannan falaloli:

 

 • Gafarar manyan zunubai.
 • Garkuwa daga bala'in daren farko cikin kabari, da kuma samun matsuguni a Ranar Hisabi, bayan an hura kaho. Wannan salla za ta zo kabarin wanda ya aikatata cikin mafi kyawun yanayi tana mai cewa: "Ya masoyina, ina maka albishir da tsira daga dukkan wahalhalu. Mutum zai tambaya: 'Wane ne kai, don ban taba ganin fuska mai kyau kamar taka ba, kuma ban taba jin magana mai dadi kamar taka ba, kamar yadda kuma ban taba jin kamshin mai dadi irin kamshinka ba?. Sai sallar ta ce masa: 'Ya Masoyina! Nine ladan sallar nan da ka yi a daren kaza, a gari kaza, a wata na kaza kana kuma a shekara ta kaza. Na zo cikin wannan dare ne don saka maka da kuma cire maka duk wata damuwa ta kadaitaka da rashin sanin makoma da kake ciki. Kuma lokacin da za a hura kaho zan kasance maka inuwa a kanka. Don haka ka kasance cikin farin ciki Kuma babu abin da za a rage maka har abada'.

  Yadda Ake Yin Sallar:

  Da farko dai ka yi azumi a wannan ranar Alhamis ta farko na rajab, lokacin da ka zo sallar magariba da lisha, tsakanin wadannan salloli biyu sai ka yi raka'oi goma sha biyu, kana mai yin sallama bayan kowani raka'oi biyu. A kowace raka'a za ka karanta Suratul Fatiha sau guda da kuma Inna Anzalnahu sau sau uku da kuma Kulhuwallahu Ahadun sau goma sha biyu.

  Bayan ka idar da wannan salla sai kuma ka karanta, wannan addu'an ko kuma salati sau saba'in (70):

   
  • "Allahumma Salli `Ala Muhammad, Annabiyyil Ummiyyi, Wa `Ala Aalihi" Daga nan sai ka yi sujada ka karatan wannan du'a'i sau saba'in alhali kana cikin sujadan:
    

  • "Subbuhun Quddusun, Rabbul Mala`ikati Warruh". Daga sai ka dago kanka ka karanta wannan addu'a sau saba'in:
    
  • "Rabbigh-Fir, War-ham, Watajawaz `Amma Ta’alamu, Innaka antal `aliyyul A`a-zam" .
    
  Daga nan sai ka roki abin da kake so, Allah Zai biya maka bukatanka Inshallah.

   

 

 

 
 

Sauran Ayyukan Rajab

Kadan Daga Cikin Muhimman Ayyukan Wannan Wata.

(1) Azumi

Hakika an kwadaitar da mutum da ya azumci wannan wata ko da na rana guda ne. An ruwaito cewa: Wanda ya azumci rana guda cikin wannan wata na Rajab, za a nesanta shi da wuta kimanin tafiyar shekara guda, wanda kuwa ya azumce shi na kwanaki uku, to za a sanya shi a Aljanna.

Imam Ali(a.s) ya kasance ya kan azumci wannan wata dukkansa, kamar yadda mabiyansa ma suke yi.

Wata rana wani tsoho ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce masa: "Ya Manzon Allah, lalle ba ni da karfin azumtan dukkanin wannan wata" Sai Manzon Allah (s) ya ce masa:

 

"Ka azumci farkon watan, tsakiyarsa da kuma karshensa, to za a baka lada kamar wanda ya azumci dukkan watan, don kuwa aikin mutum mai kyau ana rabanya shi sau goma ne".

(2) Neman Gafara (Istighfaari)

Rajab wata ne na neman gafarar Ubangiji ga al'ummata, don haka ku yawaita yin istigfari a cikinsa, don kuwa Allah Mai gafara ne, Kuma Mai Rahama....Ku yawaita fadin: Astagfirullah Wa Asluhuttaubah.

(3) Sadaka da ba da Taimako

Taimakawa wadanda ba su da shi da ba da sadaka a wannan wata dai yana da lada mai girma. Wanda ba zai iya yin azumi ba to yana iya ba da sadaka kowace rana cikin wannan wata, ko kuma ya yawaita karanta "Subhana Ilalahil Jaleeli Subhana Man la Yanbaghil Tasbeehu Illa Lahu; Subhanal A`azzinil Akrami; Subhana Man Labisal Izza wa Huwa Lahu Ahlun."

(4) Yawaita Karanta "Laa ilaaha illa-Allah" sau 1000.

(5) Yawaita karanta "Astaghfirullaaha dhul jalali wal Ikraam min jami' al dhunubi wal aathaam" sau 1000.

(6) Yawaita karanta Sura Al Tawheed ‘Qul-hu-wallahu Ahad‘ sau 1000 don samun ladan Mala'iku dubu da kuma albarka ga shi kansa mai karatu, 'ya'yansa, iyalansa da kuma makwabtansa

(7) Karanta ‘Qul-hu-wallahu Ahadsau 100 kowace Juma'an rajab.

 

 

 
 

Ladan Azumi A Rajab

Kadan Daga Cikin Ladan Azumi a Wannan Wata.

Shaikh Al-Sadooq (r.a) daga isnadinsa ya ruwaito Abu-Sa’eed Al-Khudri (r.a) yana cewa Manzon Allah (s.a.w.a) cewa:

“Duk wanda ya azumci rana guda na rajab, ya rufe wa kansa kofa guda ta wuta.

Duk wanda ya yi azumi na kwana uku cikin rajab, Allah Zai halicci wani shamaki tsakaninsa da wutan Jahannama, wanda fadinsa ya kai (tafiyar) shekaru saba'in.

Duk wanda ya yi azumi na kwanaki bakwai cikin Watan Rajab-Allah zai rufe kofa guda daga cikin kofofi bakwai na wutan Jahanna na kowace ranar azumin. Duk wanda kuma ya azumci kwanaki takwas na rajab, Allah zai bude kofa guda cikin kofofi takwas na Aljanna da kowace rana guda na azumin

Duk wanda ya yi azumi na kwanaki 14 cikinrajab, Allah Zai ba shi ladan, a fadojin da aka yi su da lu'u-lu'u da abubuwan kyalkyali, da idanuwa ba su taba gani ba, kuma kunnuwa ba su taba ji ba haka nan kuma zukata ba su taba tunaninsu ba.

Duk wanda ya yi azumin kwanaki 16 cikin rajab zai kasance daga cikin na farko da za su hau wata dabba ta aljanna mai haske da zata zagaya daga Aljanna zuwa ga Gidan Rahama

Duk wanda ya yi azumin kwanaki 18 cikin rajab, zai kasance tare da Annabi Ibrahim (a.s) a fadarsa; fadar da aka yi ta da abubuwan kyalkyali.

Duk wanda ya yi azumi na kwanaki 19 cikin rajab, Allah Zai gina masa gida (fada) da aka yi shi da abubuwan kyalkyali yana duban fadar Annabi Adamu da Annabi Ibrahim (a.s)a Aljanna. Daga nan zai gaisar da wadannan Annabawa kana su kuma su mayar masa da gaisuwar suna masu jaddada cancantansa.

Duk wanda ya yi azumin kwanaki 30 cikin rajab, Wani mai kira a Aljanna zai yi kira ya ce: 'Ya kai bawan Allah! an gafarta maka abubuwan da ka aikata, don haka ka fara aiki don makomarka'. Sai aka tambayi Manzon Allah (s): 'To idan kuma mutum bai samu daman yin azumin ba saboda rashin lafiya, tsufa ko kuma jinin haila?'

Sai Manzon Allah (s) ya amsa da cewa: 'To sai ya/ta ba da sadaka ko da kuwa na guntun biredi ne a kowace rana. Na rantse da Wanda raina ke hannunSa idan har suka bayar da wannan (sadaka) to ladarsu za ta kasance daidai.' Sai wani mutum ya sake tambaya: 'To idan mutum kuma ba zai iya ba da wannan sadaka ba fa? Sai Manzo (s) ya ce masa: 'To sai ya karanta wannan tasbihin sau 100 kowace rana: Subhanal Elahil Jalil, Subhana Man Layanbaghil Tasbeeh Ella Lah, Sobhanal A'azil Akram, Subhana Man Labesal Izza Wa Huwa Lahu Ahl.”

Biharul-Anwaar; Juzu'i na8, Shafi na 170.

 

 
 

Addu'ar rajab

Addu'ar da ake Son Karantawa a Wannan Wata.

Wannan addu'a dai ana son a karanta ta duk bayan kowace salla ta farilla Shaykh Abbas Qummi cikin littafinin MafateeHul Jinaan ya ce Imam Ja`far as-Sadiq (a.s) ne ya koyar da ita.

Ga yadda addu'an ta ke cikin Larabci:

Ina neman alfarma wajen duk wanda ya karanta wannan aiki da wadannan adu'oi da ya sanya ni da mahaifana da suka rasu cikin addu'ansa, da fatan Allah Ya sanya mu da iyayenmu cikin wadanda Allah Zai 'yanta a wannan wata.