A+ R A-
25 March 2023

Imam Khumaini (r.a) Da Batun Kwato Masallacin Qudus

Ranar 16 ga watan Mordad 1358 hijira Shamsiyya (7, Augusta, 1979), wato kasa da shekara guda da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran labari ya zo wa marigayi Imam Khumaini (r.a) kan irin sabbin ayyukan ta’addancin da yahudawan sahyoniya suke yi a Kudancin Labanon da ma sauran yankunan Palastinawa. A irin wannan lokacin ne marigayi Imam Khumaini (r.a) ya fitar da wannan sako nasa da ke cike da tarihi na sanar da “Ranar Kudus Ta Duniya.

Ga abin da yake cewa:

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

 

Tsawon shekaru masu yawa, na kasance mai sanar da musulmi irin hatsarin da ke tattare da wannan Isra’ilar ‘yar fashin (kasa), wacce a yau ta kara kaimin irin hare-haren wuce gona da irinta a kan ‘yan’uwanmu Palastinawa maza da mata, musamman a Kudancin kasar Labanon da nufin kawar da gwagwarmayar Palastinawa. Ina kiran dukkanin musulmin duniya da gwamnatocin musulmi da su hada hannu waje guda wajen gutsure hannayen wadannan ‘yan mamaya da masu goya musu baya. Ina kiran dukkanin musulmin duniya da su sanya ranar Juma’ar karshe ta watan Ramalana – wanda daya ne daga cikin ranakun al-Qadr (Lailatul Qadari) wanda kuma za ta iya zama mai ayyana makomar al’ummar Palastinu – a matsayin “Ranar Qudus. Sannan kuma ta hanyar bukukuwa da tarurrukan da za su gudanar za su bayyanar da irin hadin kai da musulmin duniya suke da shi da kuma nuna goyon bayan su ga halaltattun hakkokin ‘yan’uwansu musulmi (na Palastinu). Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa musulmi nasara a kan kafiran duniya.

Manufar marigayi Imam Khumaini (r.a) na sanar da wannan ranar, ita ce karfafa gwagwarmayar da al’ummar Palastinu suke yi da ‘yan mamaya yahudawan sahyoniya da kuma mayar da wannan gwagwarmayar ta zamanto wata gwagwarmaya ta kasa da kasa da kuma bayyanar da irin goyon bayan da al’ummar musulmi na duniya suke ba wa Palastinawan na ‘yanto kasarsu ta haihuwa daga wajen sahyoniyawa ‘yan share guri zauna.

A lokuta da dama, bayan wannan sanarwar, marigayi Imam Khumaini (r.a) ya sha karin bayani da kuma bayyana cewar babbar manufar ita ce ‘yantar da masallacin Al-Aqsa daga mamayan sahyoniyawa da kuma kafa gwamnatin Palastinawa mai cin gashin kanta a kasar Palastinu. Wanda idan har aka tabbatar da hakan, hakan yana nufin kawo karshen wannan cutar kansar (haramtacciyar kasar Isra’ila) ce. Saboda haka ne marigayi Imam Khumaini (r.a) ya fito da wannan hanyar ta karfafa gwagwarmayar Palastinawa daga cikin gida da kuma samar mata da goyon baya na kasa da kasa, don karfafa Palastinawan a wannan kokari da suke yi na tumbuke wannan cutar kansar daga kasarsu. Ko shakka babu dukkanin wadannan bangarori biyu (wato karfafa gwagwarmayar a cikin gida da kuma bayyanar da shi a fagen kasa da kasa) lamari ne da zai taimaka nesa ba kusa ba wajen cimma wannan manufar, musamman idan aka yi la’akari da rawar da fahimtar al’umma take takawa wajen kai kowace irin gwagwarmaya ce ga nasara.

Kafin wancan lokacin lamarin Palastinu dai bai fito fili ga da dama daga cikin al’ummomin duniya kai har ma da na musulmin ba. Hakan kuwa yana da alaka da irin yadda kafafen watsa labaran duniya suka yi shiru kan wannan lamarin kai a wasu lokuta ma da murguda hakikanin abin da ke faruwa. Su kuwa kafafen watsa labaran kasashen musulmi babu wani abin a zo a gani da suke yi, in ma sun yi din ba su da wani tasiri na a zo a gani a duniya. Amma bayyanar da wannan rana da kuma irin tarurruka da jerin gwanon da ake yi a duk fadin duniya, don amsa wannan kira na marigayi Imam, ya sanya fitowa da wannan lamari fili kowa kuwa makiya din ba sa so.

A halin yanzu dai a kowace rana bangarori daban-daban na manufar sanar da Ranar Kudus ta duniya da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi sai dada fitowa suke yi, wanda ke nuni da irin hangen nesar da wannan babban bawan Allah yake da shi.

Ana iya cewa sanar da wannan rana ta Kudus, wani riga malam masallaci ne da Imam ya yi don fada da abubuwan da a yau duniyar musulmi take gani na kokarin kawo karshen wannan lamari na Palastinu da Qudus ta hanyar shigo da rikice-rikice na kabilanci da mazhaba da wasu masu bakar aniya ga al’ummar musulmi suke yi ta hanyar fitar da wasu fatawoyi na kafirta musulmi da halalta jininsu da kuma sauya alakar irin farkawar da al’ummar musulmi suke yi cikin ‘yan shekarun nan.

Ranar Kudus ta duniya wani lamari ne da ke nuna wa musulmi cewa ba su da wata manufa da buri a halin yanzu da ya wuce su hada kansu waje guda da kuma ‘yanto wannan masallaci wanda ya ke a matsayin alkiblarsu ta farko. Duk wani abu sabanin haka kuwa wani kokari ne kawai na rarraba kansu da kuma karfafa  sahyoniyawa ‘yan fashi.

Ko shakka babu al’ummar musulmi ta hanyar raya wannan rana ta hanyar tarurruka da jerin gwano da makalolin da za a dinga rubutawa da sauran hanyoyin wayar da kan al’umma, za su iya taka gagarumar rawa wajen cimma wannan manufa da aka sa gaba da kuma kawo karshen duk wani kokari na haifar da fitina a tsakaninsu.

Ayatullah Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr

An haifi Ayatullah Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr, daya daga cikin manyan malaman Shi'an kasar Saudiyya sannan kuma limamin garin Awamiyya na kasar Saudiyya, ne a shekarar 1379 hijiriyya (1968 miladiyya) a garin Awamiyya na lardin Al-Qatif da ke gabashin kasar Saudiyya. Iyayensa dai mutane ne da aka san su da riko da addini da kuma tafarkin ilimi.

Ya fara karatunsa ne dai a wannan gari na su na Awamiyya inda bayan ya yi karatun firamare da sakandare a wannan gari na su, daga nan ne ya kama hanyar karatu na addini inda ya tafi Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kasar Siriya don yin karatu na addini. Ya tafi Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ne dai a shekarar 1400 hijiriyya (1989 miladiyya) don yin karatun Hauza inda ya shiga makarantar Hauza ta Al-Qa'im (a.s) da ke birnin Tehran wanda Ayatullah Sayyid Muhammad Taqi Modarrisi ya kafa ta a wannan shekarar. Sheikh Nimr Baqir Al Nimr, ya shafe shekaru 10 yana karatun addini a wannan makaranta inda ya yi karatu a wajen manyan malamai irin su Ayatullah al-Uzma Sayyid Muhammad Taqi Modarrisi (wanda bayan wasu karatun da ya yi a wajensa, har ila yau kuma ya yi karatun 'Bahasul Kharij' a wajensa. Sai kuma Allamah Sheikh Sahib al-Sadiq da kuma Ayatullah Sayyid Abbas al-Mudarrisi. Kamar yadda kuma ya karanci darasin Akhlaq a wajen Ayatullah al-Uzma Sayyid Sadiq Al-Shirazi.

Bayan wadannan shekaru goman, Allamah Nimr ya tafi kasar Siriya don ci gaba da karatunsa inda ya shiga makarantar Hauza ta Sayyida Zainab (s.a.w.a) da ke birnin Damaskus. A can din kuwa ya yi karatu a wajen malamai daban-daban da suka hada da Ayatullah Al-Khaqani da kuma Ayatullah Tabataba'i, wadanda ya yi karatun 'Bahasul Kharij' a wajensu.

Tsawon wadannan shekaru dai Ayatullah Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr ya karanci manyan littafa na bangaren fikihu da usul da sauransu ta yadda dai har ya kai matsayin ijtihadi.

Irin wannan dimbin ilimi da kokari ne ya sanya shi rike wannan makaranta ta Hauzar Al-Qa'im (a.s) da ke birnin Tehran din (wato makarantar da ya fara karatu a wajen) haka nan kuma da makarantar da ya yi karatu a kasar Siriyan ma ya taba rike shugabancinta. A lokacin shugabancin da ya yi wa wadannan makarantu guda biyu, an samu gagarumin ci gaba da kuma sauye-sauye a wadannan makarantu.

 

Ayyukansa Na Ilimi

 

Bayan komawarsa gida Saudiyya, Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na karantarwa da shiryar da mutane. Daga cikin ayyukan da ya ke gudanarwa sun hada da:

- Limancin salloli biyar na rana da kuma sallar juma'a a Jami'ar Imam Husain (a.s) da ke garin Awamiyyan.

- Ya kafa Hauzar Imam al-Qa'im (a.s) a garin na su na Awamiyya, wacce a farko ake kira da Ma'ahad al-Islamiyya a shekarar 1422 hijiriyya.

- Shi ya fara tsayar da sallar Juma'a a garin na Awamiyya a shekarar 1424 hijiriyya bayan an dakatar da ita na shekaru.

- Ayyyukan da yake gudanarwa na tsaida sallolin jam'i da Juma'a a garin na Awamiyya ya sanya an sami damar tsaida irin wadannan salloli a wasu yankunan na daban.

- Gudanar da lakcoci da wa'azi a garuruwa daban-daban.

- Bugu da kari kan rubuce-rubuce da buga littafa.

 

Ayyukansa Na Siyasa:

 

Baya ga ayyuka na ilimi da karantarwa, har ila yau Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr ya kasance yana gudanar da ayyuka na siyasa a wannan gari da kuma wannan yanki na gabashin kasar ta Saudiyya. Irin wadannan ayyuka na siyasa da lakcocin da ya ke yi dai ba su yi dadi wa mahukuntan kasar Saudiyyan ba saboda irin yadda yake tona musu asiri da kuma wayar da kan al'umma kan irin abubuwan da suke yi. Hakan ne ya sanya mahukuntan kama shi a lokuta da dama da tsare shi.

Gwamnatin Saudiyyan ta fara kama shi ne a shekara ta 2006 miladiyya jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Bahrain inda ya halarci wani taro na kasa da kasa kan Alkur'ani mai girma. Dalilin kama shi din dai shi ne kiran da ya yi ga gwamnatin Saudiyyan da ta sake gina Makabartar Baqi'a da kuma amincewa da mazhabar Shi'a a hukumance da kuma soke manhajar karatu da ake amfani da ita da sauya ta da wata sabuwa wacce ba ta karan tsaye da cin mutumcin akidun Shi'a.

Har ila yau kuma a shekara ta 2008, mahukuntan Saudiyyan sun kama Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr da tsare shi na kwana guda. Dalilin kama shi din kuwa shi ne zarginsa da Sa'ad al-Faqih daya daga cikin masu adawa da 'ya'yan gidan Al-Sa'ud masu mulki a kasar Saudiyya da ke zaune a birnin London na cewa Iran ce take goyon baya da kuma taimakawa shi Allamah Nimr din sannan kuma gwamnatin Saudiyya ta gagara kama shi.

Haka nan kuma a shekara ta 2009 ma jami'an tsaron Saudiyyan sun sake kama shi da tsare shi sakamakon suka mai tsanani da ya yi wa mahukuntan kasar sakamakon da kuma barazanar ballewar yankin gabashin kasar.

Kamu na karshe da mahukuntan Saudiyyan suka yi masa kuma suke ci gaba da tsare shi har ya zuwa yanzu shi ne wanda suka yi masa a shekara ta 2012 bayan kakkausar sukar da ya yi wa Yarima Nayef bn Abdul'aziz bayan mutuwarsa inda ya siffanta shi da cewa shi din nan dagutu ne sannan kuma za a azabtar da shi yana mai cewa ba zai shiga Aljanna ba. Hakan ne ya sanya jami'an tsaron gwamnatin kai masa hari da bindigogi inda suka harbe shi a cikin motarsa kana suka yi gaba da shi da ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da aka gabatar da shi a gaban kotu inda mai shigar da karar ya bukaci kotun da ta  yanke masa hukumcin kisa.

Kama  Sheikh Nimr din dai da ci gaba da tsare shi ya janyo zanga-zangogi a yankin Gabashin kasar ta Saudiyya da kiran mahukuntan da su sake shi. Haka nan kuma bayan wannan bukata ta a yanke masa hukumcin kisa ma, malamai da sauran jama'an gabashin Saudiyyan da ma sauran malumma da jama'a na kasashen musulmi sun yi Allah wadai da hakan da kuma bukatar da a gaggauta sako shi.

Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr ya yi kaurin suna wajen sukan bakar siyasar gwamnatin Saudiyya da kuma tsayawa kyam wajen kare hakkokin mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) na kasar Saudiyya wadanda gwamnatin take ci gaba da take musu hakkokinsu da kuma daukansu a matsayin 'yan kasa masu daraja ta biyu.

Allamah Sheikh Nimr Baqir al-Nimr yayi shahada ne a ranar Asabar 02 ga watan Janairun 2016, lokacin da mahukuntan Saudiyya suka sanar da zartar da hukuncin kisan da suka yanke masa inda yayi shahada a matsayin shahidin da aka zalunta.

Allamah Sheikh Nimr Baqir Al Nimr yana da mace guda da kuma 'ya'ya uku.

Allah muna rokonka ka sanya jinin wannan shahidi da aka zubar ya zamanto mafarin kawo karshen gidan sarautar Al-Saud.