A+ R A-
25 March 2023

Yakin Siffin Da Mu'awiyya Dan Abu Sufyan

Yakin Siffin Da Mu'awiyya dan Abu Sufyan:

________________________

Mafi girman matsalar da Imam Ali (a.s) ya fuskanta a lokacin halifancinsa ita ce matsalar tsofaffin gwamnonin da suka kasance suna shugabantar garuruwan Musulmi.

A hakikanin gaskiya dai wajibi ne gwamnonin su kasance sun kai kololuwa wajen tsantseni da tsoron Allah, gudun duniya da tsarkin niyya, ta yadda za su iya zama abin koyi ga mutane, kuma jagorori zuwa ga shiriya da gyara; alhali tsofaffin gwamnonin ba su kasance haka ba, maimakon haka sun siffantu ne da fasikanci, zalunci, wawure dukiyoyin jama'a da keta haddin rayukansu.

Wasu daga cikin wadancan gwamnonin sun kasance daga cikin masu matsananciyar kiyayya da cutarwa ga Manzon Allah (s.a.w.a); misalin irin wadannan akwai Hakam bin al-As, wanda ya kasance mafi tsananin cutarwa ga Manzon Allah (s.a.w.a), ta yadda har sai da Annabi ya kore shi, tare da dansa, daga Madina. Daga cikin su akwai Walid bin Ukbata bin Abi Mu'id, gwamnan Usman a Kufa, wanda ya kasance: "Mazinaci, mashayin giya, har yana da wani abokin shan giya Kirista(3)". Ya taba yiwa mutane sallar asuba raka'a hudu a lokacin yana cikin maye.

Daga cikin irin wadannan akwai Abdullahi bin Sa'ad bin al-Adi, wanda ya kasance marubucin Annabi ne da farko, sai ya ha'ince shi cikin rubutunsa, sai Manzo ya kore shi, daga nan sai ya yi ridda ya bar Musulunci; daga baya sai Usman ya nada shi gwamnansa a Masar.

Daga cikin irin wadannan akwai Mu'awiya dan Abu Sufyan, gwamnan Sham, Mu'awiya ya kasance yana mulkin Sham baki dayanta, ya yi gwamna tun lokacin Umar; ya kasance yana wata irin rayuwa ta annashuwa da holewa irin wadda ba wata shari'a da ke mata iyaka, kuma bai lizimta wa kansa addini ba.

Ahmad bin Hambali ya fitar a cikin Musnad dinsa, daga Abdullahi bin Baraidata, ya ce:

""Na taba shiga wajen Mu'awiya ni da Babana, sai ya zaunar da mu a shimfida, sannan ya zo mana da abinci muka ci, ya zo mana da abin tsotsawa kayan maye, sai Mu'awiya ya taba, Babana ma ya taba, sai (shi Baban Baraidah) ya ce, rabo na da shan giya tun da Manzo (s.a.w.a) ya haramta ta(4)".

Da alamun Mu'awiya ba ya jin wani kunci ko damuwa da shan giya, ta yadda har ya kasance ana dauko masa ita a kan rakumi a bi da ita ta hanyoyi da kasuwanni. Har ma wata rana an taba bi da rakuma dauke da jakunkunan giya ta wajen Sahabin nan Ubadata bin Samit, a lokacin yana Sham, sai ya tambaya mene ne wannan? Hala Mai ne? Sai aka ce: a'a giya ce da za a sayarwa mutumin -Mu'awiya- sai ya dauki wuka ya keta wadannan jakunkunan.

Mu'awiya ya kasance mai tsananin kiyayya ga Ali (a.s), saboda ya kashe dan'uwansa Hanzalah daga cikin Mushrikan da ya kashe a lokacin Badar, da kawunsa Walid bin Utbah, da wasu mutane masu yawa daga danginsa wadanda suka kasance cikin sojojin kafiran Kuraishawa; wannan na daga manyan dalilan da suka haifar da kiyayyar Mu'awiya ga Imam Ali (a.s), ta yadda har sai da ya sa ana zagin Imam a kan mimbarorin masallatai da hudubobin juma'a.

Ta bangaren Imam Ali (a.s) kuwa, ba shi da wata hanya a lokacin da yake dauke da tutar Musulunci a gabansa in ba sauke irin wadannan gwamnoni da musanya su da wasu Mununai mutanen kirki daga Sahabban Annabi (s.a.w.a) ba. Wannan ya sa wadanda wadannan sauye-sauye suka shafa suka dauki Mu'awiya a matsayin mafakarsu, don haka sai suka tafi suka yi dandazo a karkashin tutarsa, sai Mu'awiya ya sanar da tawayensa a kan matsayin Imam Ali (a.s) na tsige shi, ya ki yin biyayya ga halifa na gaskiya, ya fara shiri don kalubalantar Imamin zamaninsa.

Bayan gama yakin Basra (Jamal), Imam Ali (a.s) ya komo garin Kufa a shekara ta 36 bayan hijira. A lokacin ya yanke shawarar ya dawo da helkwatar hukumarsa daga Madina zuwa Kufa, saboda gurin ya fi zama a tsakiya, sannan kuma zai ba shi damar kawo karshen irin fitina da kutsawar da Mu'awiyya yake kokarin yi a Iraki.

To amma kafin Imam Ali (a.s) ya fuskanci Mu'awiyya da mutanensa don dawowa da su tafarkin gaskiya, ya yi kokarin magance matsalar ta hanyar ruwan sanyi, inda ya aike da manzonsa Jarir, shugaban kabilar Bani Bajila kana kuma gwamnan Hamdan zuwa Sham (Siriya) don tattaunawa da Mu'awiyya. Amma abin bakin ciki ko da isarsa sai Mu'awiyya ya saye shi da kudade masu yawa da kuma shirya masa bukukuwa da dai dukkan abubuwa kawa na duniya, ya ci gaba da zama a Sham din har na tsawon watanni, daga baya, bayan watanni uku ya dawo ya ce wa Amirul Muminina Ali (a.s) ai babu yadda za a yi a yi sulhu sai har an binciko wadanda suka kashe Usman da kuma hukumta su. Wato a takaice irin take da su Mu'awiyya suke yi da kuma fakewa da shi wajen cimma burinsu na tawaye wa halaltacciyar gwamnatin Ali (a.s). Daga karshe dai Jarir ya bar rundunar Imam Ali (a.s) ya koma cikin rundunar Mu'awiyya.

Daga karshe dai Imam Ali (a.s) ya ga cewa babu wani abin yi face dai a shirya yakan 'yan tawaye, don haka sai ya shirya runduna ya fito ya nufi Sham. Kafin dai ya isa inda Mu'awiyya ya tara rundunarsa a Siffin sai da ya dan fuskanci wasu 'yan sojoji na mutane Sham a Sur a'-Rum ya gama da su kafin ya isa ga asalin sojojin da aka ajiye a Siffin din, hakan kuwa ya faru ne a watan Zulhajji shekara ta 36 bayan hijira.

A Siffin din dai, Mu'awiyya ya ajiye sojoji kimanin 10,000 karkashin jagorancin kwamandansa, Abu Awr, a bakin tafkin da ke wajen inda ya umarce su da su hana sojojin Imam Ali (a.s) ruwa. Ganin haka sai Ali (a.s) ya tura Sasaa bn Sauhan al-Abdi zuwa wajen Mu'awiyya yana mai ce masa babu bukatan ya dau wannan mataki don kuwa mutanen da ya hana su ruwan musulmi ne, yana mai jaddada masa cewa da a ce shi ne ya riga zuwa wajen da bai hana su ruwa ba. Amma ina, sai Mu'awiyya ya mayar da martani da cewa wadanda suka kashe Usman ba su bari an kai masa ruwa ba lokacin da suka kewaye gidansa, don haka Mu'awiyya yana daukan fansa kan hakan ne.

Ganin haka da kuma tabbatar da cewa 'yan tawayen ba za su sauko ba, sai Imam Ali (a.s) ya kaddamar da hari karkashin jagorancin Malik al-Ashtar, jarumin kwamandan Amirul Muminina Ali (a.s). Nan take kuwa ya yi kaca-kaca da sojojin Mu'awiyya bayan yaki mai tsanani, ya kore su daga wajen da kuma kame bakin ruwan. To amma sabanin Mu'awiyya, Imam Ali (a.s) sai ya bar sojojin 'yan tawayen su yi amfani da ruwan don biyan bukatunsu.

Daga nan sai Ali (a.s) ya raba dakarunsa na sojoji 90,000 zuwa rundunoni bakwai karkashin jagorancin jaruman kwamandojinsa, shi ma a nasa bangaren Mu'awiyya ya raba nasa dakarun na sojoji 120,000 zuwa rundunoni bakwai. Ta haka kowace rana runduna guda sai ta fuskanci 'yar'uwarta a ta gabzawa.

Imam Ali (a.s) ya yi kokarin ganin ba yi yakin na gaba daya ba saboda gudun kada a zubar da jinin musulmi, don haka a mafi yawan lokuta an yi yaki ne na mutum guda daga kowani bangare ya fito ya fuskanci dan'uwansa, ko kuma 'yar karamar runduna ta fuskanci 'yar'uwarta. Haka dai yakin ya ci gaba har karshen watan Zulhajji da kuma shigowar watan Muharram, inda aka tsayar da yakin saboda haramta yaki da Musulunci ya yi a cikin wannan wata na Muharram. A daidai wannan lokaci dai Imam Ali (a.s) ya yi kokarin ganin an dakatar da yakin ta hanyar tattaunawa, yana mai cewa a shirye yake ya hukumta wadanda suka kashe Usman din matukar dai Mu'awiyyan zai nuna su, amma ina Mu'awiyya ya ki yarda a tsaida yakin, saboda daman ta wannan yaudara ta maganar daukan fansar jinin Usman ne ya samu mutane da yawan gaske da suka bi shi.

Yaki ya sake barkewa bayan shigowar watan Safar, inda aka yi ta yi har na sati guda, a kullum lamari sai dada munana ya ke yi. Don haka a mako na biyu sai Imam Ali (a.s) ya shigo fagen fama da kansa a karo na farko, inda ya gama da duk wani wanda ya tunkare shi har sai da ya rasa wani mutum guda da zai nufo inda yake saboda jaruntar da aka sanshi da ita.

Haka dai aka ta rasa mutane a kowace rana musamman ma dai daga cikin sojojin Mu'awiyya, duk da cewa a bangaren Ali (a.s) ma dai an rasa wasu manyan mutane da kuma sahabban Ma'aikin Allah (s) irinsu Ammar Yasir da Hashim bn Utba da dai sauransu.

Shahadar Ammar bn Yasir wanda a lokacin yana dan shekara 93 a duniya ya tabbatar da cewa rundunar Ali (a.s) ita ce take kan gaskiya, don kuwa an jiyo Manzon Allah (s) yana gaya wa Ammar din cewa rundunar 'yan tawaye da suka kauce wa hanya ne za su kashe shi. Kamar yadda wannan shahada ta Ammar din kuwa ta nemi ta kawo baraka cikin rundunar Mu'awiyya din, saboda wasu daga cikin sojojin nasa sun ji wannan kalami na Manzon Allah (s) don haka suka san cewa lalle suna kan bata, don haka suka nemi yin tawaye. Ganin haka sai Mu'awiyya ya fara tunanin yadda zai bulllo wa lamarin inda daga karshe dai ya ce wa mutane ai Ali ne ya kawo Ammar wannan yaki don haka shi ne ya kashe shi ba su ba, don haka rundunar Ali ne Manzon Allah (s) ya ke nufi ba rundunarsa ba. To da yake rundunar wawaye ne aka tara, sai suka yarda da wannan karya ta Mu'awiyya suka ci gaba da yaki har zuwa dare na sha uku na watan.

A wannan rana babban kwamandan dakarun Imam Ali (a.s) wato Malik al-Ashtar ya nuna gagarumar jarunta da kai mummunan hari ga sojojin abokan gaba, sai kabbararsa kawai ake ji a duk lokacin da ya kashe abokin gaba. Hakan ya tsorata makiyan da kuma tarwatsa su, dukkan alamun nasara ta fara bayyana. Ganin haka sai Mu'awiyya ya tara na kurkusa da shi yana neman shawarar abin yi, inda ya tuntubi sanannen na kusa da shi din wanda kuma aka sanshi da iya kulla makirci wato Amr bn al-Aas, wanda kuma ake kira da Dilan Larabawa saboda wayon da yake da shi, kan abin yi. Nan take sai ya ce masa: "Ka kira su zuwa ga kalmar Allah".

Jin haka sai Mu'awiyya ya umarci mutanensa da su daga kwafi 500 na Alkur'ani sama a kan masunsu suna masu cewa Littafin Allah ne zai raba rikicin da ke tsakaninsu. Wannan dabara ta Ibn al-Aas kuwa ta ci don kuwa yayi tasiri ga wasu daga cikin rundunar Ali (a.s) inda suka ce to lalle a dakatar da yaki don Alkur'ani ya yi hukumci.

Ganin haka sai Imam Ali (a.s) ya fito ya bukaci dakarun nasa da su ci gaba da yaki, kada su bari wannan makirci ya ci su, don kuwa makirci ne kawai Mu'awiyya yake son yi amma ba wai ya yi imani da Littafin Allah din ba ne, don da ya yi imani da Littafin da bai yi tawaye wa halaltacen halifan Manzo ba. Amma ina, wadannan dakaru na Ali (a.s) da suka rudu sun ki amincewa da hakan. Hakan ya tilasta wa Ali (a.s) ya yarda aka kawo karshen wannan yaki, inda aka yanke shawarar cewa kowani bangare zai kawo mutum guda don tattaunawa da kuma daukar matsaya ta karshe.

Don haka Mu'awiyya sai ya fitar da Amr bn al-Aas ya wakilce shi, a bangaren Imam Ali (a.s) kuma sai aka fitar da Abu Musa al-Ash'ari. Da farko dai Imam Ali ya so Abdullahi bn Abbas ko Malik al-Ashtar ne ya wakilce shi, amma mabiyansa suka ki yarda suka fifita Abu Musa din.

Abu Musa al-Ash'ari dai ko da wasa bai yi daidai da Amr bn al-Aas ba, saboda rashin wayon da yake da shi da kuma saukin hali, alhali kuwa bn Al-Aas kowa ya sanshi da iya makirci da wayon tsiya.

An tsara dai cewa wadannan mutane biyu za su hadu da juna su tattauna don zaben abin da "yafi alheri" wa al'umma da kuma makomar musulunci don "dakatar da wannan yaki". Don haka bayan wani lokaci sai mutanen biyu suka hadu kowani guda daga cikinsu tare da rundunarsa ta mutanensa. A yayin wannan haduwa dai an samu halarta manyan mutane daga Makka, Madina, Iraki da kuma Sham (Siriya) don gane wa idanuwansu abin da zai gudana.

Daga cikin wadanda suka raka Abu Musa al-Ash'ari har da Abdullah bn Abbas, wanda ya ja kunnen Abu Musa din da ya yi hankali da abokin tattaunawar tasa, kada ya bari ya yi masa wayo, sannan kuma ya san cewa babu wani laifi da Ali (a.s) ya yi da zai hana shi jagorantar al'umma kamar yadda kuma Mu'awiyya ba shi da wata falala ko kuma siffa mai kyau da za ta sanya shi ya jagoranci al'umma.

Isar Abu Musa ke da wuya wajen da za a yi wannan tattauna, sai Amr bn al-Aas ya fara wannan makirci da aka san shi da shi, inda ya karbi Abu Musa hannu bibbiyu. Daga nan kuma sai suka shiga wani waje da aka kebe musu su biyu za su tattauna donfitar da matsaya. Tuni dai Ibn al-Aas ya san irin rauni da rashin wayon Abu Musa, don haka sai ya yi kokarin girmama shi da ba shi kulawa ta musamman ta yadda har sai da ya gama janyo hankalinsa zuwa gare shi (Ibn al-Aas). Koda Ibn al-Aas ya ga ya samu kan Abu Musa, sai ya sanya shi ya yarda da cewa an kashe Usman ne cikin zalunci, duk dai da nufin ya sa shi ya yarda da cewa to ai Mu'awiyya, wanda da man ya fito daga kabila guda ne da Usman din kana kuma a halin yanzu yana ikirarin daukan fansar jininsa, shi ne ya dace ya gaje shi. To sai dai Abu Musa ya ki amincewa da hakan, face dai abin da yake da muhimmanci shi ne su yi kokari wajen ganin ba a ci gaba da zubar da jinin musulmi ba.

Jin haka, sai Ibn al-Aas ya bukaci Abu Musa da ya yarda su tube Ali (a.s) da Mu'awiyya don ba da dama ga musulmi da su zabi wani halifan,(wato kowannensu ya tube wanda yake wakilta), yana mai ce masa wannan dai ita ce kawai hanyar da tafi sauki. Nan take Abu Musa ya yarda da haka, ya ce to su fita su shaida wa jama'a wannan kuduri da suka yanke.

Tuni daman an shirya mimbari inda kowani guda daga cikin wakilan biyu zai gabatar da nasa jawabin. Da suka fito sai Abu Musa ya bukaci Ibn al-Aas da ya fara gabatar da nasa jawabin, to sai dai saboda makircin da ya kulle cikin zuciyarsa, sai ya bukaci Abu Musa da ya fara gabatarwa yana mai cewa Abu Musa ai tsoho ne kuma yana daga cikin sahabbai na gaba-gaba. Don haka sai Abu Musa ya dare mimbari ya ce:

"Ya ku mutane! Ni da Amr bn al-Aas mun yi nazari cikin wannan lamari kuma mun yanke shawarar cewa babu wani abin da zai tabbatar da zaman lafiya da tsaida fitina kamar mu sauke Ali da Mu'awiyya sannan mu bar al'umma su zabi wanda ya fi dacewa gare su. Don haka na tube Ali da Mu'awiyya daga halifanci kamar yadda na cire zoben nan nawa daga hannuna".

Bayan da gama wannan jawabi nasa, sai Abu Musa ya sauko kasa don ba wa Ibn al-Aas damar ya gabatar da nasa jawabin kamar yadda suka tsara. Saboda haka sai Ibn al-Aas ya dare mimbarin don gabatar da nasa jawabin, inda ya ce:

"Ya jama'a! kun dai ji yadda Abu Musa ya tsige shugabansa Ali daga halifanci, to ni a bangarena, ni ma na tube shi kuma na dora shugabana Mu'awiyya a matsayin halifa kamar yadda nake sanya wannan zobe nawa a hannuna. Na yi hakan ne kuwa cikin adalci saboda Mu'awiyya shi ne mai daukan fansar jinin Usman".

Yana gama fadin haka sai ya sauko, ya bar Abu Musa cikin tsananin mamaki saboda irin wannan ha'inci da Ibn al-Aas ya yi masa ta hanyar canza maganar da suka yanke. Wannan lamari dai ya faru ne a watan Ramalana, shekara ta 37 bayan hijira.

Irin wannan abu dai shi ne abin da daman Imam Ali (a.s) ya san zai faru don haka ne ma yaki amincewa da Abu Musa a matsayin wakilinsa, to amma wasu mutane suka matsa cewa dole ne Abu Musa din shi ne zai wakilci Ali (a.s) kai ka ce kamar daman wani makirci ne aka kulla.

Ta haka ne dai aka kawo karshen wannan yaki, kuma Mu'awiyya ya tsira daga babban rashin nasarar da yake fuskanta a yayin wannan yaki.

A karshen wannan yaki dai an kashe mutanen Mu'awiyya kimanin mutane 45,000, shi kuma Imam Ali (a.s) ya rasa mabiyansa guda 25,000.
 ____________

(3)- Umar bin Abi Shibh, Tarikh al-Madina, juzu'i na 3, shafi na 984.

(4)- Ahmad bin Hambali, Musnad, juzu'i na 5, shafi na 347.